20

32 1 0
                                    

  
✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

              20.

******Har ga Allah so yake ya rungume ta shima, amma kuma yana tsoron masifar da zata masa daga baya, ganin tayi shiru ta lafe a jikin sa, yasa shi a  hankali ya ɗan rungume ta ba wani can sosai ba irin slide hug haka. Ɗagowa tayi hakan yasa shi saurin sakin ta, yayin da ita kuma ta maka masa harara.

"Wa ya ce ka taɓa ni?

Ta faɗa tana ƙoƙarin shigewa toilet.

"Allah ya baki haƙuri".

Shima ya faɗa yana komawa wurin zaman sa, sai de tunanin abinda ta aikata kawai yake yi a yanzun, wato ita batajin tsoro da shakka kowa? Komai zata iya yi? To me ye ruwan ta da rayuwar sa ? Sai kuma yayi shiru yana tuna maganar da tace akan ya ajje ya gani za su neme shi ko a'a. Mutanen da ya suka kori Baba aiki waye ba za su kora ba? Duk da cewar ya gani yanzu FD company ba na Kernel ne ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallan ta, ta fito ta fice da ido kawai ya bita, da za'a fita aka ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa.

"Masifa".

Ya faɗa a ran sa yana janyo lapton ɗin sa ya fara duba aiki.

Yayin da su kuma yan office kowa ya ƙame cike da mamakin abinda ta ce wai mijin ta. Daman yana da aure ne ko kuma de kawai faɗa tayi? Yayin da kowa yake cewa wannan bata dace da shi ba wajen halayya kowa da abinda yake ayyanawa a ran sa. Ta wurin Ogan na su kuwa sosai ya yayi tsaye yana jin takaicin wannan yarinyar ce take faɗa masa magana marasa daɗi akan Deeni. Ba abinda ya ɗaga masa hankali irin za su bar aiki, gaba ɗaya shine ƙarfin aikin da ake documenting, sanda Mahaifiyar sa ta rasu kafin ya fara aiki, sosai suka fara yin ƙasa akan al'amarin companyn amma sai gashi daga zuwan ko wata guda ba'a yi ba komai na su ya dawo hayyacin sa, ba abinda suka sani manyan wurin sai hassada da kwashe kuɗin ma'aikata, yayi imani da cewar muddin ƴan gidan su suna nan suma ba baya ba wajen aiki shiyasa yace masa zai ɗauki kowa nasa aiki suke bashi albashi kuma mai tsoka ashe de bakowa ke san kuɗi ba. Duk tunanin a cikin seconds yayi su. Kafin ya maida kallan sa ga wajen ma'aikatan dake ƙus-ƙus kowa da abinda ke ran sa, da'alama jira suke a fice sallah kowa ya tofa albarkacin bakin sa, mutane ba sirri sai tsegumi da munafurci iri-iri.

Ganin Aisha su Zainab sun rufe ta sai kuka take yi a hankali, yasa shi zuwa inda take yagan ta, jini ya wanke mata fuska, dake suna shashashu ne sai suka tsaya suna mata sannu ko tissue ba wanda yasa ya fara tsane jinin, fita da ita yace su yi su kai ta ɗan ƙaramin clinic ɗin dake companyn na su shine ya musu jagora da kan sa, yana tafe yana jinjinawa wannan yarinyar da irin ƙoƙarin ta. Suna fita da ita Hafsah na fitowa fuska a tamke, duk ido suka zubo mata suna kallan ta, haɗe fuska tayi tamau tana jan kujerar da ke kusa da Mu'azzam inda ta fara zama ta zauna.

Ɗagowa tayi ta kalle su ganin irin kallan da suke jifan ta da shi, ta haɗe rai ta fara gunguni a ran ta. Mu'azzam na jin ta be ce komai ba kafin ya  ɗan kalle ta ya cigaba da abinda yake, sai de a zahiri kawai jinjinawa karfin halin ta yake yi, suna sabbin zuwa su da suke lallaɓa komai su zaman ma'aikata amma shine take faɗin wannan abun.

"Dan Allah na tambaye ki?

"Uhm".

"Nawa za'a ke biyanmu a wata? Na ji ɗazu kin ce sai de ya dawo anan ake biyan shi 30k haka ne?

Kallan sa tayi, har zata masa shiru sai kuma ƴan mutuncin suka zo.

Tace, "Da za su ɗauke aiki haka suka ce ?

"Dubu ɗari fa suka ce a wata".

Jinjina kai tayi tace, "Dubu arba'in ne a wata".

"Arba'in kuma?

ZARAHADDEEN Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin