Numfashi ta ja a hankali tana fitarwa, kafin ta tashi ta yaye curtains ɗin ɗakin ta, ta zauna a table coffee ɗin dake wajen tana kallan ƴan tsirarun mutanen dake wuce a titin wajen.

Tace, "D tarbiyya tana da matuƙar girma a rayuwar mu".

"Wacce irin tarbiyya kake tambaya na?

"Maryam ki dena wahalar da kan ki wajen tambaya na, tambayarki nayi dan Allah ki faɗa min".

Ajiyar zuciya ta sake saukewa cike tausayin sa da taji ya ɗarsu a ran ta batare da tasan dalili ba.

"D tarbiyya wata kalma ce wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta renon jikin,  hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Ma'ana  tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a. Tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa". Ita ce ayyukan ɗaukakowar halittu, ƙarawa mutum mutumtaka domin ya samu kaiwa cikakkiyar daraja matabacciya a jiki da aiki da ruhi da kuma cuɗanya".

"D".

"Tarbiyya na sawa a ga mutum da daraja, kima, kwarjini, duk mutumin dake da tarbiyya zaka same shi farin cikin sa baya yankewa. Kuma da kake ganin ta, kala kala ce tarbiyyar mutun baya zama mutum sai zama mai cikakken tarbiyya, ta haɗa da ladabin iyaye, wanda suka girme ka, ganin darajar na ƙasa da kai, taimakon da sauran su.  Sannan akwai tarbiyya ta ladabin cin abinci da kuma abin sha, akwai ta sallama yadda mutum zai shiga ɗakin da bana sa ba, ko gidan da bana sa ba, da kuma idan yayi sallamar a ina ya kamata ya tsaya, da sanda ake zuwa gidan mutane duka addinin mu be bar mu haka ba sai da ya koya mana shi, babu abinda Monzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama be yi mana har wani ɗaya daga cikin Sahabbai yake cewa harda yarda ake bayan gida ya koya mana"....

'anzo wajen'.ya faɗa a ran sa. Yana mai cigaba da sauranta, sai da suka shafe kyawawan awowi uku suna waya batare ta gaji ba, yayin da shi kuma yake auna irin abubuwan da yake aikatawa, ba ganar dashi kurakuren sa, ta lusar da shi abubuwa da dama da shafi iya rayuwar sa wanda ya kamata ace ya sauya. Sai da suka gama tas.

Tace, "D ? Faɗa min mene ya faru?

Jin ya sami nutsuwar zuciya har wani ƙwari yaji zuciyarsa na yi da karfi da ya ji ya zo masa. Ya tashi yaje ya kunna TV.

Yace, "Faɗa min sunan tashar nan da kike kallo ta wa'azi".

"Akwai Africa TV 3, Sunna Tv, wisal, manara, Daawa sunna....

"Ahh Maryam".

"Baka faɗa min ba. Mene ya faru".

Sai da ya kai channel ɗin sannan ya kwashe komai ya faɗa mata, har ƙona gidan da tayi, da kuma irin zagin da ta masa,wani abu ya bata dariya har ta kasa riƙe wa sai da ta dara.

Tace, "Wallahi matar nan masifaffiya ce D. kayi hankali kar ta kona min kai".

"Dariya ma kike min?

Tana danne dariyan nata.

Tace, "D ba haka ne ba yi hakuri".

"Zaki sani".

Tace, "Kasan ranar da na fara ganin ta ka ji zagin da tayi kuwa? Allah jikina har tsuma yake yi Bro. Ga shi ta iya tsawa kai matar nan bala'i ce. Kayi a hankali idan kaje bikon matar ta ka".

"Dan Allah ka haɗa ni da ita zan kira ka da number na".

"Ashe haka kike da surutu?

Sai tayi murmushi.

Yace, "Waje ne baki samu ba ko?

"Kamar ka ba".

Sai shima yayi murmushin kawai sai kuma ya sami kan sa da yin dariyan. Daga nan suka yi zancen da ba su taɓa yi ba tunda suka zo duniya. to her biggest surprised godiya ta ji yana mata sai abin ya bata mamaki lalle yana so ya sauya. Suna ajje wayar ta sami kan ta da yin dariya ita kaɗai tana shiga wankan ta, tana wanka tana murmushi, duk wani kuncin zuciya sai ta ji bata jin sa a yau. 

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now