Tana sunkuyar da kan ta tana wann turo baki gaba ga kwalla da ta ka cika mata ido.

Tace,"Anyi".

"Allah shikuwa shiyasa Anty take burgeni ta wani lokacin, yanzu ne zaka ji ɗau ta ɗauke mutun da bari bata san reni ita a rayuwar ta".

Sadiq yace, "Ai naga alamar halin ku ɗaya da ita, komai faɗa komai faɗa haba dan Allah ku sauya rayuwar ku Wallahi. Ku ke yin haƙuri bakomai ake yin magana akai ba".

Deeni yana tattare kayan sa, yana tunanin su kam ba su da faɗa sam, mutum sai musu laifi amma za su bashi haƙuri, Sadiq ne kawai yayi fada sanda yana yaro amma yanzu shina be da faɗa, ko cacar baki ake zaka same shi shine mai sulhu saɓanin shi da ko kashe kan ku zakuyi ba zai kalle ka ba, ita kuma Zarah hayaniya amma akwai cika baki a baya wanda ya mata laifin. Sun kasance tamkar mahaifin su haka suke. Yayin da su kuma suka biyo halin Kakar su da sam ba sa barin ta kwana musamman Hafsat da har yau be taɓa ganin masifaffiya irin ta ba.

"To sai de ku kuke haƙurin amma nide ba zan yi ba".

Ya faɗa yana tashi ya wuce dan dagaske zuciyarsa tafasa take yi akan me zai taka ta? Duk laifin Zarahn ma yake gani. 

*****Hashim kuwa matuƙar mamaki ta bashi mamaki, to mene dalilin ta na bashi haƙuri bayan shine ya mata laifin? Haka de ya ture komai ya sai abinda zai siya ya wuce. Koda yaje kwanciya yana rufe ido fuskar Zarah ta zo masa, tare da 'ouch' ɗin da ta ce. Tashi zaune yayi yana shafa kan sa, kawai ya taka ta ne dan yaga wacce iri ce ita? Ita masifaffiya ce ko aka sin haka? Sai ya tarar da ita mai haƙuri ce dan har yanzu marin da Hafsat ta masa idan ya tuna haushin kan sa yake ji. Har yau be san wanne irin mataki zai ɗauka ba. Daga ƙarshe ficewa ma yayi daga hotel ɗin yaje ya sarara kan sa ya sake sannan ya dawo da ya tabbatar da baccin ya ci idan sa tukunna. Washegari babu aiki amma hakan be hana shi gudanar da abubuwan da suka zo yi ba.

*****Yau kam dukan su suke zaune a parlour har Hafsat da ta kasance mai zaman ɗaki. Ummu na matsawa Hajja ƙafar ta, ita tana aiki Sabir da Taufiq na karatu yana ƙara masa Hadithn da be iya ba, Ameerah kuma na kallo, Hafiz shima aikin yake yi.

"Allah idan baka mai da hankali ba zan ki fa maka mari abin ya ishe ni tun ɗazu ake faman yin abun ɗaya".

Taufiq ya faɗa a zafafe. Sabir yana jerin mutanen da baya saurin ɗaukan karatu amma idan ya ɗauka baya mantawa gashi kuma yana san karatun hakan yasa yake da san karatu. Irin su kuwa kowa yasan daman sai ankai zuciya nesa ake musu karanta.

"Kayi haƙuri".

Sabir ɗin ya faɗa abin tausayi, shi kan sa abin yana damun sa amma idan ya iya zo kaga yadda ake murna.

"Munafuki kamar na Allah".

Taufiq ɗin ya faɗa ƙasa-ƙasa yarda shi kaɗai ne zai ji shi, haka suka ci gaba amma kuma be iya ɗin ba, agogo ya kalla yaga goma saura tun wajen takwas da rabi suke faman yin abu ɗaya Hadith ƙwara ɗaya ya gagara ya riƙe shikam ya gaji. Karanta masa yayi be iya ba, ya buge masa baki be sauke nasa hannun ba yaji an kife shi da mari, marin da ya janyo hankalin kowa ya zuba musu ido, ko be ɗago ba yasan Antyn su ce.

"Tashi kasan inda dare yayi maka".

Ta faɗa tana rufe laptop ɗin ta. Tare da janyo Sabir ta daura shi akan cinyar ta ta kwantar da kan sa a jikin ta tana janyo Hadithn, tasan ba zai taɓa yin bacci ba matuƙar be iya wannan karatun ba, hakan yasa ta ajje duk wani aikin nata domin koya masa.

Hajja da ta fara gyangyadi kin mari yasa ta buɗe ido tana zabura.

"To nide a gidan ana yawan ɗaukan hakki na".

Banza tayi mata ta fara koya masa a hankali a hankali.

Hafiz yace, "Me kayi aka mare ka?

Shiru yayi yana muzurai yana ɗan kallan ta, duk ya tashi ya yi nesa da su.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now