"Yayaaaa".

Ta faɗa da ƙarfi kamar ta  ta so ta gudu ta rungume shi, murmushi yayi sosai yana dosowa wajen ta tare da tsugunnawa yana kallan ta.

"Yaya sannu da dawowa".

"Sannu ya gidan?

"Alhamdulillah".

"Ameer?

Sadiq ya faɗa yana nuna farin cikin sa na ganin sa, shima murmushin yayi yana ƙarasowa suka gaisa.

"Yaya tare kuka zo?

Sadiq ya tambaya yana tashi domin miƙa masa hannu.

Ameer yace, "A'a daga sama na fito".

Dariya suka yi suna gaisawa.

Zarah tace, "Ina yini".

Ganin sa da tayi sangameme da shi ya cika mata ido dan ya kusa Sadiq sam batayi tunanin Ameer ne ba duk da cewar suna chat da shi, kuma bata fiye wani ganin hotunan sa ba a cewar sa wai baya hoto, shi kuwa Ameer ya sake ya amsa da lafiya.

Sadiq yace, "Ehh lalle su Zarah yaushe aka fara gaida ɗan sa'a kuma?

Ameer yace, "A'a Wallahi Yaya Sadiq na girme ta wannan yarinyar".

Deeni tashi yayi dan ba zai iya wannan musun ba, Zarah idan aka musu da ita ba'a taɓa gamawa sai ta ƙure mata, baya jin ita da Sadiq har yau Sadiq ya  taɓa cinye ta gashi ita ce bata da gaskiya amma idan ta haƙiƙance zaka rantse da Allah ita ce mai gaskiyar ta kuma yi nasara. To shima Ameer haka yake.

Tace, "Ya Sadiq bangane ba? Wai Sa'a na ne wannan ɗin? Harda wani ya girmeni?

Yace, "Baki gane shi ba wai? Ameer ne fa. Ɗan Baba shida Ameera".

"Ameer? Wai na Ameerah? Laaa kuma shine cib. Kai Ameer haka ka zama sangameme da fa wani ɗan firit da kai kamar a hure ka ka faɗi ƙasa "

"Lalle Yarinyar nan kin ga makwanci na shiyasa".

"Lalle yaron nan ka ga ka fini tsayi shiyasa".

Ta kuma faɗa tana kwankwayen muryan sa.

Yace, "ehh ɗin, yarinyar de ta gaida ni. Kuma daga yau Yaya Ameer zaki na cewa idan ba haka ba na daka ki a gidan nan".

"Ka daka wa?

"Ke".

Be rufe baki ba yaji tana wani abu. Sai ga geese sun fito daga wata ƙaramar ƙofa sun nufo wajen su. Ameer ganin jibga jibgan abubuwa sun nufo shi yasa shi ɓoyewa a bayan Sadiq, ganin sun biyo shi yasa shi arta da gudu zuwa cikin gida aikuwa suka rufa masa baya yana gudu suna bin sa. Me kuwa Zarah da Sadiq za su yi ba dariya ba.

Da gudu ya shige cikin parlourn su wanda yake da ɗauke da ɗaki huɗu abin su kowa daya sai na gwaggo dake tare da su har yau. Kallan sa Deeni yayi da ya fito jin ihu yana masa kallan lafiya?

Jin ana ƙwanƙwasa ƙofar ne yasa shi sanin geese ne ya biyo shi. Yasan kuma wannan ba kowa ba ne sai Zarah har ta fara nuna halin kenan kai kawai ya girgiza kan sa ya koma.

Gida ne madaidaici mai ɗauke da ɗaki huɗu da parlour sai kitchen ɗin su tsakar gidan babba ce ba irin can ɗin nan ba dan a ƙalla mota uku zuwa huɗu za su iya shiga. Daga can ta baya kuwa wata ƙofa ce ƙarama wanda idan ka buɗe ta zaka ga wurin kiwon su ne. Akwai dabbobi wurin su daban haka ma tattabaru suma na su wajen daban, sai talatalo da kuma geese sai shuke shuke wasu na ci wasu kuma na kwalliya da bishiyo wajen yayi kyau sosai. Geese ɗin masu bin mutane idan ba su san su ba sun riga sun riƙa gashi ba su fiye ƙyanƙyansa ba.

Sadiq ne ya shigo yana zama.

Yace, "Daga zuwan ka har an fara yi maka welcoming naka da wancan abubuwan ko?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now