36

1.8K 218 55
                                    

Na kasa jefarda takardar kuma na kasa fadawa kowa cewar ya bani takardar kamar yadda na kasa fadawa yan sanda. Shi kuma be fasa chusa kansa a cikina ba, har kara ma da bibiyata kawai yake amman a yanzu har yarana yake yi ma siyayya ta kudi mai yawa ya kai musu a scul a gida kuma ya aiko min da ita, a kullum ina fargabar idan Mama ta tambayi wanene shi wa zan fada mata ba? Bayan karyar da nai mata cewar wani ne dana hadu da shi yake min haka yai ma su Namra, amman idan aka samu akasi yarana ko kuma Mama da kanta ta ganshi fa? Duk wanda ya gan ni da kafiri zai yi mamaki abunda ya hada ni da shi ina diyar musulmai.
Sai dai a yadda na fahimta kamar shima yana gudun mutane domin baya min magana a inda yakr ganin jama'a da yawa, sai idan ina a kebance kamar idan zan hau napep ko na sauka ko zanje wani gurin sai kuma da dare zai aika yace ana min sallama. Duk kuwa da ban tana fitowa da sunan amsa sallamar da yake min ba, hakan be hana shi aiko min lokaci zuwa lokaci ba, kamar yadda yake yawan bibiyata yana rokon na saurareshi.
Ni kuma na kasa saurarensa saboda bana jin aminci a tare da shi wata kila saboda ba addinin mu daya da shi ba oho, sai dai a yadda na lura yana da kamun kai da taka tsantsan da kuma natsuwa wacce ba ko a musulman mu ba kowa kake samu da wannan ba.
  Ba ni da wata fargaba a yanzu sai ta abubuwa uku,wannan Abraham din sai kuma Aminu wanda shi ma ya saka ni a gaba da yawan bugo min waya da sunan zai gaisa da yayansa tun yana kira ina dagawa na bawa yaransa har ta kai yanzu idan ma ya kirani sai dai na mika musu wayar su su yi magana da shi, hakan kuma be hana idan ya kare magana da su yace su ba ni wayar idan ni kadai ce ko kuma da kanen sai na yanke kiran idan a gaban Mama ne kuma na kan dauka saboda ta gargade ni cewar na daina kin karbar wayarsa ko dan darajar yarana, ina yi mamata biyaya ne kawai saboda ina gudun bacin ranta gudun kar tace ban dauki shawararta ba, amman har ga Allah bana kaunar jin sunan Aminu ma balle jin muryarsa, shi kuma yanzu har wani zillon rashin kunya yake domin wani sa'in har cikin gida yake shigowa ya gaishe da Mama da Baba sannan ya fita, ga wata bakar al'ada da ya tsiro ta daukar yaran yana tafiya da su gidansa ko wani gurin daban su wuni can sai dare zai kawo su gida. Idan na nuna zan hana sai Mama tace min ba haka ba. Wani lokacin sai dai nai ta jin haushin a zuciyata kawai amman ban isa na nuna a fili ba saboda kar mama tace saboda ita nake yi.
  Na tattara komai a yanzu na aje a gafe, babu da bukakata da damuwa kamar abu na ukun nan wato neman aiki, duk inda naji wata ma'aikata ko wani kamfani sai na mika takarduna, sannan na saka addu'a a gaba nai ta yi ko Allah zai saka a dace.!

Bayan na gama sallah isha'i ina rike da wayata ina latse latsena kamshin turaren Abdallah yai min sallama kamin muryarsa ta daki dodon kunnena, a take na nemi natsuwata na rasa sai na ji duk na kwadaitu da son ganinsa fuskarsa a take na aje wayar na unkura ina gyara Hijab dina na mike tsaye ina juyowa sai nai arba da mutum, faduwar gaba ta same ni a lokacin wacce take yayin yin haka a duk lokacin da nai arba da Abdallah, abun ka da wacce ta rude sai na kasa komawa na zauna daman dakin babu kowa sai ni kadai da aljanuna idan ma ina da su, ratsawa nai gefensa na da zimmar na fita domin a bakin kofar yake tsaye ya zuba min idonsa kamar ya cinye ni, ban san yadda akai ba na kasa lura da kyau har na buga kaina da garun kofar a take goshina ya fara zogi ni kuma na saka hannu ina murzawa jikina na ta rawa kamar marar gaskiya, har lokacin be dauke idonsa daga kaina ba kuma be kauce daga kofar ba. A dole na koma na zauna saman kujerar da ke kusa da inda nai sallah, amman me sai na gagara samun natsuwa domin jikina na bani cewar idonsa na kaina. Sai da ya ji muryar Inna ta doso dakin tana masa lale marhabun sannan ya karaso cikin dakin ya zauna a saman carpet din da na tashi wanda nai sallah, idonsa ya koma gurin kafafauwa ya sakar musu ido kamar mai son tantance abu, ni kau na daga abuna sama na dora saman kujera na lullube su da hijab, sai kallon ya koma gurin hannayena, su ma na nade abu cikin hijab din sannan ya kalli Inna wacce ta shigo ta zauna.

“Abdallah yaushe rabonka da gidan nan”

“Bana samun zama ne sosai yanzu shiyasa aikin yana min yawa, ya gida ya kwana biyu?”

GOBE NA (My Future)On viuen les histories. Descobreix ara