23

1.5K 192 16
                                    

Na kan dora komai a mizanin kaddara, na yarda dukan abunda ya same ni ko zai same ni rubuttacen al'amari ne daga gurin mahaliccina, wani be isa ya goge min ba kamat yadda ban iya na yayewa kaina ba.

Wannan ma yana cikin kaddararki Halimatu, haka zuciyata take yawan fada min kuma ina samun natsuwa sosai idan na tuna cewa ko wane abu da izinin Ubangijina yake samu na. Iyakar kokarin da nai na danne zuciyata ne daga kokarin aikata wani abu marar kyau wanda wani bangare nata yake hararo na ke ganin kamar mafita a gareni. Tun daga lokacin ba mu sake hada shimfida da Abdulhamid zai ba, ma'ana dai be sake leko dakina ba kamar yadda ni ma ban sake taka kafata dakinsa ba matukar yana a cikin gidan, ban fasa masa girki ba be fasa ci ba, ban kasa mika masa ko wace  irin gaisuwa ba, sannu da dawowa, Allah ya tsare daman halina ne. Sai dai ban sake ganin walwalar fuskarsa ba kamar yadda walwalarsa ta hana tawa walwalar.
Idan ina zaune a falo baya zama, idan kuma yana zaune na zauna sai yai kamar ya tsargu a take zai tashi ya shige dakinsa.

Ban taba ganin laifin Abdulhamid min akan wannan ba, idan na saka kaina a matsayinsa ni kaina na san kwatankwacin abunda zan yi kenan, ba lallai ne ya gasgata ni ba, kamar yadda ba kowa zan fada haka ya yarda ba, sai dai abunda yafi min ciwo kallon da yake min na cewar na ci amanarsa.
  Ina ji ina gani zaman gidan yaki yai min dadi, na kasa sakewa, kwanciyar hankali yai min kwara walwala ta yi min bankwana, kuka da damuwa suka kwankwaso min kofa.

Har ta kai bana iya bachi idan lokacin bachin yai, sai dai na raya dare da sallah ko kuma na zauna nai ta kallon sillin ko da kuwa bana tunanin komai bachin ba zai dauke ni, da rana kuma sai na tsargu ina ganin kamar ni ce kadai nake cikin matsala. Da kaina na fita chemist din dake unguwar na siyo maganin mura na ruwa a duk lokacin da na ji ina bukatar bachi sai na sha, wani abun mamaki a take bachi zai dauke ni kuma sai na manta da duk wata damuwa dake tare da ni.
Da dare kawai ba, da rana ma idan na ji damuwar ta matsa min na dan kan sha sai kuma na samu salama da natsuwa, na sani akwai illa abunda nakr sha, kuma na san ba abu ne mai kyau ba, mace kamar ni mai yaya hudu ace na buge da shan kayan maye domin na samu bachi, wannan ma yana saka ni damuwa sai dai babu yadda na iya idan ban yi hakan ba ban san abunda rashin bachin zai janyo min ba. Gaba daya yanayi na ya canja ni kaina na sani, bana sakewa kamar da ga ciwon ido ya saka ni a gaba har ta kai bana iya daga idon sosai.
  Tun lokacin da abun ya faru ban sake fita da sunan zuwa unguwa ba ko wani gurin, Hajara ma ban sake labarta mata komai ba, a ganina duk wanda zan fadawa ba zai sama min mafita ba dan haka babu amfanin fallasa sirrin nawa.

Yau ma kamar jiya ta kama weekend sai dai yau Sunday ba Saturday ba, Abdulhamid tun safe ya fita kamar yadda ya sabawar kansa yanzu da fita ranar weekend ya wuni a wani gurin sai dare zai dawo, bayan da can ba haka ya saba ba. Lamarinsa na ya bani tausayi ta wani bangaren kuma sai ya bani tsoro na kan yi tunani anya ko wace mace zata iya sadaukarwar da nai? Auren mutum kamar Abdulhamid a lokacin da tawa kaddarar ta same ni sai ya juya min baya? No be kamata nai wannan tunanin ba, shi ai ba shi da lafiya rashin lafiyarsa babbar damuwarsa ce sai kuma ni na kara masa wata, ya fa kamata na gane wani abu a duk lokacin da wani ya rabe ni sai wani abu marar kyau ko kuma na bakinciki ya same shi, misali kamar Kabir ko yana ina ma yanzu?
Ni kadai nake zaune a falona ina ta sake sake da tunani kala kala wasu masu amfani wasu kuma marar amfanin. A tsorace na kalli kofar falon saboda knocked din da akai, haka nake yawan tsorata ko iska ya kada sai gabana ya yanke ya fadi. Sai da na sake jin an kwankwasa kuma na ji kamar hayani a waje sannan na tashi na nufi kofar na bude. Kanwata ce Hafiza tare da Namra da Aiman da Adnan da Amal da kuma wata yarinyar da ban waye ta sosai ba. Da gudu suka rumgume ni su dukansu wani kalar farinciki na ji wanda na dade ban ji irinsa ba, lallai ya'ya rahama ne, a take idona ya cika da kwalla ni kaina na san na yi kewar ya'yana, dukawa nai na dauki Amal muka shigo falon tare da su.
  Bayan sun huta na dauko musu abincinmu, sannan na shiga dora wani domin ban san da zuwansu ba kuma nasan wanda za su cin ma ba isarsu zai yi ba, ina cikin kitchen din Hafiza ta same ni da zancen siyayyar da Aminu yake ta musu Namra a kwanakin nan, daman kuma Mama ta fada min a waya a duk lokacin da ya zo sai ta fada min domin ita ma mamaki abun yake bata kamar ni. Daga ni har sun mun rasa dalilinsa na nunawa yarana kulawa a yanzu, bayan siyayya ma duk bayan kwana biyu sai ya zo ya fita da su ko kuma ya duba lafiyarsu.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now