59

2.5K 336 245
                                    

Kwance take a dakinta tana kallon windows din dakinta da suke bude, pillow na rumgume a kirjinta babu abunda ke fita daga idonta sai hawaye masu zafi.
  Mai aikinsu ce Hindatu ta turo kofar dakin ta shigo da sallama.

“Assalamu Alaikum, Siyama Hajiya na nemanki”

“Ki ce zan zo”

Ta amsa ta ba tare da ta juyo ta kalleta ba. After like one hour Hajiya ta turo kofar dakin ta shigo.

“Siyama....”

Sai a lokacin ta fara kokarin yin kamar bachi take, hakan yasa Hajiya ta karasa kusa da gadon ta zauna leken fuskarta da hawaye ya gama yi mata kwalliya.

“Miye abun kuka kuma? Me yake damunki?”

Juyowa tai da kyau ta kalli Hajiya wasu hawayen na cika mata ido.

“Hajiya...”

Sai kuma tai shiru ta tashi zaune tana matsar yatsun hannunta.

“Ba ki fito kin ci abinci ba, ko yau ba kya zuwa makarantar ne?”

“Hajiya bana son na sake rasa kowa”

Ta fada cikin hawaye.

“To wa za ku rasa?”

“Ban sani ba, amman yanzu idan ciwo ya kama wani a cikinmu sai na rika ganin kamar zan rasa shi ne, i don't want to be alone....”

Ta fashe da kuka, tana kwantawa jikin Hajiya.

“Babu abunda zai samu yayanki zai samu sauki In-Sha-Allah, ki daina tada hankalinki kin ga nima kina daga min nawa, da kuzari da karfin zuciya da nake da shi sai ki sa ya karye”

“Hajiya ina jin tsoro”

“Ki daina kawai ki yi masa addu'a, ki tashi ki wanke bakinki ki fito ki yi breakfast”

Ta gyada kai tana share hawayenta Hajiya ma ta yi saurin tashi tana tare hawayen da ke son zubo mata, cikin rashin kuzari ta fita daga dakin ba Siyama kadai ba ita kanta abun ya bata tsoro jin cewar ba a ga komai ba kuma gashi yace yana jin ciwo, tun daga lokacin da ciwon ya same shi baya iya komai daga zaune sai tsaye sai kwance wani lokacin kuma ya kan dan zagaya cikin asibitin amman fa sai idan am masa allurar kashe ciwo, ga shi baya wani iya cin abu mai nauyi daga lemu sai ruwa sai tea shi ma can ba a rasa ba, sai dai tana addu'a kuma tana fatar idan an je check up din nan a gano matsalarsa. A dinning din take zaune amman ta kasa taba komai balle ta ci kamar ba ita ta dafa abun karyawar ba, yadda yake fito daga part dinsa ya zo part dinta su karya ko kuma idan ba shi da lokaci sai ya dauki breakfast din ya tafi da shi ko mug ne abunda yafi tsaya mata a rai, yau kusan 7 days yana asibiti mutumen da bata bari yai nisa da ita, and the most saddest part is aurensa aka daura yana cikin farinciki wannan abun ya same shi.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta dora hannayenta saman dinning din ta dafe kanta kamin ta kike tsaye ta nufi upstairs dan jin tai bata bukatar cin komai.

HALIMATU POV.

Ba karamin tsoro ne ya kama ni ba, na san ban tana kiran Ahmad ba tun da nake a rayuwata, amman mi zai saka yanzu na kira shi yaki dagawa? Amman ya kamata nai masa uzuri, after like seven minutes a sake gwadawa still be daga ba na sake gwadawa be daga ba haka nai ta yi har kusan 20 miss calls amman be yi picking ba, a lokacin ne fargabana ya karu tsoro ya auri zuciyata na fara sake sake kala kala, ji nai bana da natsuwa kwata kwata a rayuwata jikina ya bani cewar akwai abunda Ahmad yake boye min.
Tashin nai na shiga dakina na canja tufafin jikina na saka wata rigar yadi na dauki medium veil na yafa na saka talkamina na dauki yar purse dita cikin dabara na fice na bar gidan domin na san idan nace zan fadawa Mama zata iya cewa ba zan fita ba tare da izinin mijina ba, tun da ba fada mata zan yi gurinsa zan je ba, ina tafe ina waige waige kar wani dan gidan mu ya gan ni kamar wata marar gaskiya, Allah ko ya bani sa'a har na tari napep na hau ban hadu da kowa ba, zuciyata bata raya min na je ko'ina ba sai gidansu Ahmad, duk kuwa na san hakan be dace ba amman ba ni da wata mafita wacce ta fi wannan ko dan samun natsuwar zuciya dole naje na ga halin da yake ciki, tun da yanzu yamma ta yi ba na san baya kamfaninsa.
  Sai da mai napep din ya kai ni har kofar gidan na sallame shi sannan nai knocked din gate din gidan cikin sa'a kuwa mai gadin ya bude min, sai da muka gaisa da shi sannan na tambaye shi ko masu gidan suna ciki, ya amsa min da suna ciki har ma da bude min kofar, sai da na doshi harabar gidan sannan na soma tambayar kaina to idan na shiga ciki me zan fada musu? Idan ma mahaifiyarsa ce tai masa katanga da ni fa? Kuma gashi na shigo har cikin gidan anya shi ma kansa zai jidadi? No wait idan ma babu duk wannan anya ban yi rashin kunya ba na tukari idansu kai tsaye? A take duk na ji wani iri hakan yasa ban karasa ba na juyo na dawo gurin mai gadin.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now