GN-2

2.4K 224 21
                                    

Sai da na jika mata kanwar ta sha na shiga dakina nai sallah isha'i, ina sallamewa nai saurin mikewa tsaye na nufi inda wayata take tana ringing na duba na yi zaton ko Abban Namra ne da farko sai dai ganin bakuwar number yasa ni aje wayar har sai na koma saman carpet har sai da na gama tasbihina nai addu'a ma mijina nai ma kaina da iyayena sannan na nemawa yara na shiriya. Daga bisani na mike tsaye na nufi inda wayar take aje na dauka na sake kiran layin da aka kirani da shi.

“Assalamu Alaikum”

Ni na fara mika sallamar kamin wanda na kiran ya fara min sallamar.

“Wa'alaikissalam Halimatu”

“Na'am Ranka ya dade”

Na gane cewar ogana ne na gurin aiki wato oga Dahiru.

“Ki yi kokarin hada document dinka kamin gobe ina da bukatarsu”

“To ranka ya dade”

“Kuma ki yi saving din wannan number ita ma number ta ce”

“To ranka ya dade”

Daga haka ya kashe wayar be sake ce min komai ba, ni ma kuma ban ce ba, daman kuma me zan ce masa, bayan kiran da yake min ma yana damuna balle kuma har nai wata magana da shi, zauna nai bakin gadon ina ta mamakin dalilin kiran da oga Dahiru yake yawan min a duk lokacin da yake bukatar wani abun, shin yana manta cewar ni ma ina da aure da iyali kamar shi, ban san miyasa yake son kira akan abunda be kai ya kawo ba, ba kira kadai ba har wasu abubuwna da yake min bana jindadinsu, domin duk abunda na ke ina kokarin kare mutuncin aure da kuma na yayana da mijina.

“Momy ni dai gobe idan mun dawo daga scul gidan zan dawo ba zan je gidan Baba Sadi ba”

Namra ce ta shigo tana wannan maganar tana wani bata fuska kamar zata fashe da kuka.

“Saboda me?”

“Bana son zawa can Momy dan Allah”

“Ki yi hakuri Mamana, idan kun dawo nan gidan ba wani abun za ku yi ba, kuma kin ga ba girki balle ku ci, amman can Momy Hassana tana girkawa, za ku samu ku ci”

“Momy to ki daina zuwa aikin nan pls ko kuma mu rika zama a gida a haka muna jiranki ki dawo”

“Mamana akwai abunda ake miki a gidan ne da baki so?”

Ta girgiza kai alamar aa sannan ta kwantar da kanta jikina.

“Cikin ya daina ciwo?”

“Eh amman yana min kadan-kadan ba sosai ba”

“Zai daina In-Sha-Allah, na zubo miki abinci za ki ci?”

“Za mu ci tare Momy zan wanke hannuna ba zan saka miki datti ba”

Murmushi nai mata sannan na mike tsaye na fito daga dakin na sauko downstairs. Ban samun Abban Namra a falon ba, daman kuma ban saka rai ba domin ba kasafai yake dawowa da wuri ba, idan kuma har ya dawo to sai idan wani abun zai yi ko zai dauka amman dai ba haka nan kawai zai dawo gida da wuri ba ko kuma ya wuni ba. Tuwon da na girka dazun kamin na fita na zubo miyar kuka sannan na fito bakin kofar kitchen rike da abincin ina kiran Adnan domin bana son sai na zauna ya zo yace min zai ci abincin.

“Adnan Aiman za ku ci abinci yanzu?”

Babu wanda ya amsa ni a cikinsu balle kuma har su sauko kasan da sunan cin abincin, sai Amal da ban kora ba.

“Ommy Ommy zan ci abinci”

“To zo ki ci yar autana”

Na fada ina karasa fitowa falon sannan na zauna kasan carpet din na zaunar da ita saman kafafuwana na soma bata.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now