29

1.4K 200 29
                                    

“Baby Namra....”

Jin maganar tasa nai kamar daga sama, ban san lokacin da na doshi kofar fita da gudu ba, har sai da Inna ta riko ni.

“Tsaya ki saka hijab dinki”

Sai na koma cikin gidan da gudu na shiga dakin Mama ban tsaya neman hijab na janyo zanen da nai arba da shi a saman gadonta na lufe kaina kamar wata tsohuwa na fito hankali a tashe. Yan mata gidan mu na biye da ni, rijiyar da na sani a unguwar mu na nufa sai Adnan yace min ba ita ba.

“Momy ba ita ba, rijiyar malam ya'u”

Tsayawa nai cak jin ya ambaci rijiyar da na manta when last a dibi ruwa a cikinta, rijiyar da ake cewa har ma sha ruwa akwai a ciki.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, miya kaiku gurin rijiyar malam ya'u”

Sai na maida dubana gurin Salma wacce tai maganar.

“Namra ce ta ce muje can mu yi wasa”

A nan ma kallon Adnan nake, kamar wacce bata da makoma haka na zama, jikina yai sanyi ga uban sara da kaina ya soma yi. Tafiya nake ina jin kamar ana mayarda ni baya ina tafiyar ina jin kamar ba kasa nake takawa, sam ban lura da babu talkami a kafafuwana ba sai da na isa bakin rijiyar kafafuwana suka taka sanyin ruwan da ke gurin. Leka rijiyar da nai ma sai da wani jiri ya kama ni saboda hudunta da kuma dadewarda tai ba a bude ta ba. Wasu mazan unguwar mu ne suka shiga ciki suka daukota a yanayin da na ganta na sam abu ne mai wahala ta rayu, ta ji ciwo a kai a fafafuwanta ma ta samu rauni hannunta har zubar da jini yake.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Shine abunda kawai na iya furta na saka hannu biyu na dauke, abun ka da marar karfi ga kuma rashin kuzari na tashin hankali sai na fadi a gurin tare da ita, har sai da kanena suka zo suka dauketa ni kuma na bi bayansu hankali tashe, har na isa gida kuka nake ina jin mutane na tambayar ko mi ya kai su can, garin ya suka fada a wannan tsohuwar rijiyar, sam ni kam ba tambayar ce a gabana yanzu ba ceto ran yar mutane ne a gabana. Muna shiga gida na dauko hijabi da jakar kudina na saka takalmi na muka nufi titi ni da kanena kusan rabin unguwar suna biye da mu wasu na fadi bata da rai wasu na tambayar yadda abun ya afku. Napep muka shiga kai tsaye muka nufi asibitin fmc, mun tararda mutane da yawa a emergency kuma sai mu ka yi rashin sa'a babu likitoci da yawa kasancewar yau Saturday. Sun karbe ta domin duk wanda ya ganta a dole ya tausaya mata, sai dai duk da sun karbe ta din hankalina be kwanta ba na kasa zaune na kasa tsaye, zuciyata ta na ta raya min cewar bata da rai ganin tun da aka cirota daga rijiyar bata motsi bata numfashi ga raunukan da ta ji.

“Anty ki zauna”

Salma ce ta dafa ni tana fadin haka, sai na girgiza mata kai ina kuka domin ba zan iya ba.

“Ko ki kira yaya Abdallah...”

Salma na fadin haka zuciyata ta raya min yes na kira shi maybe he can help, jaka na lalaba ban ji wayata ba sam ban lura da jakar kudi ce kawai a hannuna ba har sai da Salma ta miko min ta ta wayar.

“Gashi ki yi magana”

Da na karbi wayar sai na rike na rasa yadda zan yi da ita.

“Ya dauka fa”

Sai nai saurin karawa a kunne.

“Hello....”

“Wake magana”

Muryar Suwaiba ce da alama wayar tana hannunta ne.

“Ni ce Halima ce Ina Abdallah”

Ta dade bata ce min komai ba har sai da nai zaton wayar ta tsinke.

“Hello”

“Bachi yake”

“Ki taimaka min dan Allah ki tashe shi, ina cikin matsala yarinyar da..... ”

Ban gama fadar abunda zan fada ba ta tari numfashina da masifa.

“Haba Halima ya kamata ki gane Abdallah fa kanen mijinki ne, duk da ya rabu da ke be kamata wata alaka na shiga tsakaninku ba, ki shafa matsa lafiya dan Allah”

“Yanzu ma in cikin matsala ne shiyasa na kira shi...”

Na fada domin kawai ta fahimci akwai dalilin kiran ba hakan nan kawai nake kiransa ba.

“To bachi yake”

Ta tsinke wayar. Kwallar idona ta hanani ganin komai, hayaniyar mutanen da suke emergency sai na ji kamar ina wata duniyar, tabbas ina jin bakina yana motsi amman ban san me nake fada ba, Salma ta karbi wayarta ko na bata ko jefarwa nai duk ban sani ba, sai kuma na ji wani na tambayar ina yayen yarinyar nan, wata kila da mu yake wata kila kuma ba da mu yake ba duk ba zan iya ganewa a yanzu wani hudu ne ya rufe min ido ga idon a bude amman na kasa ganin komai.

“Anty.....”

Can cikin a na ji muryar Salma ta kirani kamar tana wata uwa duniyar. Tassssss na ji saukar wani azababben mari a gefen kumatuna, marin da ba a taba min irinsa ba tun da uwata ta haife ni a duniya, wani zafi na ji ya mamaye min ilahirin fuskata kamar wuta, a take kafafuwana suka kasa daukata.

“Ku rike ta....”

Shine abunda na iya jiyowa shi ma kamar daga can wata uwa duniyar, ji jai na buga hannuna a wani abun mai kamar karfi sai dai ko kadan ban ji zafin ba har numfashin da ke jikina yai gaba abunsa...


GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now