GN-10

1.8K 204 15
                                    

Ba mu dawo gida ba sai 6pm na yamma, domin bayan mace ta min wankin mara sai da likita ya bani damar hutawa na awa biyu da rabi zuwa uku sannan muka dawo gida.
  Da dare Hajara ta kawo min ziyara ta nuna min damuwarta da kulawa sosai kamin addu'arta ta biyo baya, mun dade muna fira da ita sai goma na dare mijinta ya zo ya dauketa. Bayan tafiyarsu da kamar mintuna talatin Abdallah ya kirani a waya har na yi kamar ba zan daga ba sai dai tunawa da bana da aure a yanzu ya yake min hanzarin kin daukar da nake yi a baya, wata kila ma Namra ce take son magana da ni ko Aiman.
Da nai picking ban ce masa komai ba, ko sallama da hello da ake idan an kira mutum ko kuma shi ya kira wannan karon bance ba, sai kawai nai shiruna ina jiran ya fara min magana. Shi kuma ya gagara cewa komai kamar wanda ya kira domin kawai yaji saukar numfashina, jin hakan yasa na kashe wayar na mike tsaye na nufi dakina ko kuma nace dakinmu ni da kannena. Tufafin jikina na canja na saka marar nauyi saboda yanayin garin da nake gani da kamar akwai hadari saboda zafin da yai yawa. Amal kuma na saka mata nata kayan bachi na kwantar da ita ina lallaba tai bachi sai ta fara min kukanta na banza daya saba yi wani lokacin idan za tai bachi.

“Ai da an sani a bawa Ya Abdallah ya hada da ke ya tafi mu huta”

Cewar Kanwata Haulat tana hararar Amal daman can basa shan inuwa daya da juna. Ni kuma nai murmushi na mika hannu na dago Amal na rumgumeta ina rarrashinta.

“Ya Abdallah yazo dazun lokacin kina asibiti”

“Ya kawo su Namra ne?”

Na tambaya ina kallonta.

“A a ba da su ya zo ba, shi kadai ya zo yana tambayarki sai Inna ta fada masa kina asibiti za a miki wanki mara”

Tana rufe baki kiran wayarsa na shigowa a wayata, nan ma sai dai nai kamar kar na dauka sai kuma wata zuciyar ta hana ni, picking nai na kara a kunne tare da sallama. Be amsa min ba kuma be ce min komai ba sai dai daga cikin wayar ina iya jiyo yadda yake ja da aje numfashi da karfi. Katse kiran nai na kwantar da Amal sannan nima na kwanta bayanta ina ta tunanin Kabir ko a wane hali yake ciki a yanzu inata auna zafin barin da na da kuma kafarsa da aka ce ta cire da gaske ma ta cire din ko kuwa dan karawa labarin magi dagishiri yasa tace haka? Number wayarsa na gwada kira da fari ta yi ringing har aka daga sai dai ina yin sallama sai aka kashe kiran na sake bugawa na ji wayar a rufe. Damuwa sosai ta shiga raina, ko ba komai ai mun yi zaman mutunci da Kabir idan na tsallake ko kuma na cire son tana jikin ko yi min maganar banza da Kabir yake kokarin yi ban san shi da wani hali na assha ba, tun ba jiya ba yana yawan damuwa na al'amurana, duk wani abun da ya dame ni zai nuna damuwarsa sosai a kaina, idan kuma akan wani laifin ne a gurin aiki to zai yi kokarin tare min ko ya wanke ki ko a gurin waye ne. Ko a kan wannan kadai ya kamata na damu da Kabir balle kuma saboda yaje siyo min abinci wannan abun ya same shi, ko da ciwon kai ne ya same shi ta dalilina dole na damu balle kuma hadari, abun sai ya hade min a guri daya har na rasa wanne zan fara tunani bayan damuwar da ke cina yanzu kuma wani abun ta samu Kabir ta dalilina.
Har garin Allah ya waye Kabir na cikin raina ban jidadin rashin zuwa ganinsa da ban samu yi ba, kusan rabin mafarkin da nai na Kabir ne sai dai ba zan iya fahimtar sakon mafarkin ba, kuma na alakanta hakan da kwanta da nai ina tunaninsa.
Duk da bana sallah haka ba be hana ni tashi da asuba da wuri ba kamar yadda na saba, ko bana sallah na kan yi addu'oina na safe idan ina lokacin period ne.

ABDALLAH POV.

Da gangan yake yai magana ya yi shiru yana ta sauraren yadda numfashinta ke fita fuskarsa na yalwantuwa da murmushin da shi kadai ya san sikarsa, bayan ta kashe wayar ya sake kira sallamar da tai masa ta saukar masa da natsuwa da kwnaciyar hankali daman can muryarta kawai yake son ji, domin ba shi da wani abun da zai ce mata, bayan son yai mata jajen ɓarin da tai ta waya, ɓarin kuma ba karamin dadi yai masa ba, domin ya kusanto masa da nesa kusa zuciyarsa na raya nasa a yanzu yana cikin ko wane mataki da zai iya nunawa Halimatu soyayyah, domin bata da auren a yanzu kuma ta cika idda indai har jinin ya tsaya mata. Kansa ya daga sama yana kallon tauraren da sukai ma sararin samaniya ado. Sannan ya maida wayar aljihunsa tare da zuba duk hanneyensa aljihun wandon, Halimatu ba zata so shi ba, ba zata taba amincewa da shi kai tsaye ba, domin yayi kuskuren nuna mata kauna a lokacin da take da igiya uku ta aure akanta har ta koma biyu har da zama daya, shi yake yawan fada mata mijinta yayi kaza ya yi kaza, yana yawan nuna mata Aminu ba irin mijin daya dace ta aura ba ne, ya dade yana jira zuwan wannan ranar ya dade yana addu'ar Allah ya raba auren Aminu da yar'uwarsa Halimatu saboda kawai shi ya aureta, yana ji a ransa kuma yana yawan rayawa a zuciyarsa cewar shi kadai ya dace ya zama mijin Halimatu, domin shi ne mutumen da zai iya nuna mata kauna zallarta ya kare mutuncinta ta martaba, and he know exactly how to lighten the candle of happiness in her life. Tun daga lokacin da ya dawo kasar nan tare da iyalinsa ya kyalle ido ya ga Halima sai Allah ya dauki sonta mai tsanani ya saka masa, har ya zama bashi da sukuni da walwala idan ban ganta ba ko be ji daga gareta ba, tun yana kokarin cire abun a zuciyarsa ya kawarda komai har ya gagareshi, har yake ji da ace ya san lokacin da take budurwa ko kuma yayi arba da ita tabbas da Halimatu bata da wani mijin bayan shi, domin tana da siffar da yake so a jikin mace komai na rayuwarta burge shi yake, the way she dressed, yadda take tafiyarda rayuwarta ga hakuri da kawaici ga magana ma so calmly, even simple makeup din da take burge shi yake.
Daga lokacin da ya gano kalar mijin da take aure kuma sai tausayinta ya samu muhalli a zuciyarsa, kuma ya samu makamin yaki da igiyar aurenta.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now