GN-06

1.9K 195 24
                                    

Office dinsa ya shiga da ni, sai ya saki hannuna ya sauke Namra daga saman kafadarsa ya zaunar da ita a saman kujerarsa sannan ya rufe kofar office din ya sake rika hannuna ya zaunar da ni a dayar kujerar dake kusa da kofar, sai ya zauna shi ma yana ta kallona ya kasa cewa komai, ni ma shi nake kallo amman ba kallo na ainahin kyausa ko wani abun daya shafi jikinsa ko fuskarsa ba, kallonsa nake a zahiri amman a badini zuciyata tana can gurin tunanin yau da kuma GOBENA, har yanzu na kasa yarda ba mafarki na ke ba, har yanzu hawayen ba su daina sauko min ba, har yanzu ban daina jin sautin muryar Namra na maimaita kanta a kwakwalwata ba, ji nake kamar yanzu take ba ni labarin nan, rumtse ido nai na kulle gam ina jin kamar idan na bude zan ga komai be faru ba, ji na ke kamar ace idan na bude idon zan farka daga mummunan mafarkin da nai yi ne.

“Halima”

Can cikin kaina na ji kiran Abdallah da sauri na bude idon ina kallonsa har nunfashina na rawa kamar wacce ta farka daga bachi, da gaske ji nake kamar ace mafarki ne ba gaske ba.

“Miya samu Namra?”

Ya tambaya fuskarsa na nuna tsantsar damuwa da ganin hawayen. Nuna masa Namra din nai na kasa cewa komai, bakina nai nauyi sosai kamar an saka min dutse a ciki, wata kila kalaman da zan furta a duniya sun kare ne, domin ina jin idan har bakina zai bude da sunan magana a yanzu to kuka ne kawai zai fito amman ba magana irin wacce ko wane lafiyayen mutum yake ba. Kai nake ta daga masa alamar ita din ce ita dince kamar wanda ya sake tambaya, shi kuma ya tattara hankalinsa ya maida akaina sai yawo yake da idonsa a fuskata.

“Bana son zubar hawayen nan na ki Halima, ki bude baki yi min magana maybe i can help”

Ya fada yana dauke kansa daga barin kallona ya dafe da hannunsa yana sauke numfashin da karfi, can kuma ya mike tsaye ya nufi gurin windows din ya tsaya yana kallon waje kamin ya buga hannunsa da karfi jikin ginin gurin.

“Matsalarki duk ba zata wuce ta shegen mijin nan na ki ba, can you pls talk”

Ya fada yana juyowa ya kalleni, yunkurin bude baki nai da zimmar magana da gaske sai na kasa maganar har kuma lokacin ban daina hawaye ba kamar an rubuto min ranar kawai domin kuka. Teburinsa ya nufa ya dauko takardarda biro ya aje min a gabana.

“Rubuta idan ba zaki iya min magana ba”

_So na ke a duba min Namra fyade akai mata_

Haka na rubuta a takardar na mika masa, yana karantawa ya zaro ido ya kalli Namra da sauri sannan ya kalle ni.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, garin ya?”

Nan ma kasa magana nai sai dai na bude bakina ba kamar dazun ba da dantse har da hakorana. Barin gurin da nake yai ya nufi gurin Namra.

“Namra wa yai miki haka? Fada min ya akai hakan ya faru?”

Tana kallonsa sai ta fashe da kuka daman tun da muka shigo take alamar kukan ganin nima kukan na ke yi. Sauko tai daga kan kujera ta rugo a guje inda nake zaune ta rumgume ni tana wani irin kuka mai taba zuba zuciya, ni ma fashewa nai da kukan mai sauti na rumgume yata kankan a jikina ita kuka ni kuma, sai a lokacin na fara tambayar kaina ina tunanin abunda nai wa Sadi da zai yi ma yata haka? A kullum burina da mafarkina na tsare mutuncin kaina da na mijina da na yayana, amman yau wani a cikin familyn mijina ya keta yadda yata, ya rusa min komai.

“Miyasa zai min haka? Mi masa a duniyar nan? Me zai ji a jikin karamar yarinya kamar Namra? Kuma yar dan'uwansa? Mi yasa zai saka mu a wannan halin ni da ita?”

Magana na ke ina kallon Abdallah kamar shi zai ba ni amsar duka tambayoyina. Mikewa nai tsaye rumgume da Namra na fara zagaye dakin.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now