18

1.7K 185 7
                                    

Sai da na gyara Amal na gasa mata jikinta sosai da ruwan dumi wanda hakan yasa ta dan kara sakewa har na hada mata tea ta sha ta rike yankan biredin a hannu sannan na shiga gyara ko'ina na gidan.
Duk kuwa da kasancewar barayin ba su mana barna ba ko barin wata alama da zata saka a gane cewar sun shigo cikin gidan ba, ba su balla mana gate ba balle kofa ba su yi harbi ba balle su tafi da wani abun, babu ma wanda zai shigo cikin gidan ya yarda wani ya shigo da sunan sata.

Sanin cewar Abdulhamid na son sakwara yasa na dafa da miyar agusi, bayan na gama na shiga nai wanka na dawo palo na zauna rumgume da Amal jikinta da dan zafi sai dai ba kamar jiya, ni kuma zuciyata cike da zafi fiye da ko yaushe har bana iya controlling hawayena. Sai daf da magariba Abdulhamid ya dawo sai da na wanke fuskata sannan na fita na bude masa gate, iya kar kokarin da zan iya yi na boye damuwa na yi amman hakan sai ya ci tura saboda damuwar da ke raina a yanzu mai girma ce.
  Tun daga muryata da kin son hada ido da nake da shi ya fara karantar damuwata.

“Kin fada sosai Haima idonki kuma ya kumbura gaba daya ba ki cikin natsuwarki, na fada miki zan taso daga Abuja zuwa nan amman ba ki kira kin tambayi lafiyata ba bayan ba ki saba haka ba”

Cikin rashin natsuwar da kirkirar irin karyar da zan masa na kalleshi ina hade yawu, sai a lokacin na tuna cewar yunin ranar ban saka komai a cikina ba sai ruwa shi ma ba da yawa ba, a rayuwar yau na manta da an taba halittar yunwa a cikin duniyar nan.

“Hankalina ba kwance ba Amal ba lafiya”

“Subhanallahi miya same ta?”

Ya fada yana rufe motarsa ya matsa kusa da ni ya kama hannuna yana murza yatsuna a hankali. Dagowa nai ya kalleshi a maimakon na amsa masa sai hawaye suka sauko min.

“Je ki dauko mayafi na kai ki ki ganta yi sauri”

Ya fada cike da kulawa a zatonsa Amal tana gida ne ba a gidansa ba.

“Tana nan a falo jiya na dauko ta... ”

Saurin sakin hannuna yai ya nufi kofar falo, wanda hakan ya ba ni damar share hawayena na bi bayansa, ina shiga na same shi kusa da Amal zaune yana taba jikinta fuskarsa dauke da murmushi, a hannun kujerar na zauna ina ta kallon bayansa, a zahiri bayansa na ke kallo a badini kuma makomar aurenmu na ke hangowa a tsakanin fada masa gaskiya da kuma boyewa, idan na fada masa zai jure? Zai zauna da ni a haka? Idan ma na boye mi ye amfanin boyewar? Wace iri zan ci?

“Ashe ma da sauki kike ta kuka haka har kin tada min da hankali”

Ya fada yana juyowa ya kalleni ba karamin jihadi nai ba na aron murmushin da ban san da zaman sa a duniyata ba na yafa a fuskata.

“Al-hamdulillah amman dazun jikinta kam akwai zafi sosai, kuma ina ta fargabar rashin fada maka da ban yi ba na dauko ta ka yi hakuri”

“Karki damu ai lalura ce”

Ya ba ni amsar yana maida hankalinsa gurin Amal. Ni kuma na tashi na shiga bedroom cikin rashin kuzari na hada masa ruwan wanka ina mikewa tsaye na ji an rungume ni ta baya.

“I love you so much Haima, kuma na zo miki da albishir In-Sha-Allah ina daf da samu lafiya ko yau kamin na baro Abuja sai da na ga wani likita kuma kwarare ne, ki cigaba da hakuri very soon za ki zama kamar ko wace matar aure”

A hankali na sauke ajiyar zuciya sannan na share hawayena na juyo ina fuskantarsa wasu hawayen na sauko min fuskata kuma da murmushi har na bude baki nai masa magana sai ya rumgume ni a zatonsa hawayen murna ne. Mun dauki lokaci mai tsawo a haka kamin ya sake ni ya shiga wanka ni kuma na fita na hado masa abinci na kawo masa dakinsa.
  Bayan sallah isha'i na fara shirye shiryen mai da Amal gida gurin Mama saboda nasan Amal idan har tana ganina ba zata iya kwana ita kadai ba ko kuma ita da wani ba, kamar yadda nake zaton Abdulhamid ba zai min lamanin kwana shi kadai ba ni na kwana da yata, na yi zaton zai ce na barta ta har na wani lokaci ko kuma gobe amman be ce min komai ba be hanani ba kuma be ce min na kai ta ba.
  Bayan na gama shiryata nai masa magana cewar ya kai ni a motarsa na maida ita gida, ga mamakina sai ya saka hallabiyarsa ya dauko makullinsa ya bude mana mota muka shiga ni da ita, abun ka da yaro sai ta kara lafewa a jikina har da saka hannayenta ta rumgume ni ta bata fuska sosai kamar zata fasa kuka. Ban ce masa komai ba har muka isa gida duk kuwa da kasancewar shi din yana ta min fira sama sama. Wani abun mamaki tun da na shiga gidan Namra ba ta yi na'am da ganina ba, kallo na ma sau daya tai ta dauke kanta bata sake kallon inda na ke ba, Aiman dai na tarar yayi bachi Adnan ne kawai ke kwance tsakar gida rike da karamar wayar Haulat yana kallo. A lokacin da na aje Amal sai ta fara kuka alamar bata son rabuwa da ni da sauri Namra ta zo ta dauke ta ta nufi dakin Inna da ita ba tare da tace min komai ba. Raina ya sosu ba kadan ba, kar dai ace yayana sun fara tunani ko na zabi wani ne na bar su? Babu ubansu a kusa da su kuma ni na na tafi na bar su. Har muka dawo gidan ban sake na yi walwala yadda ya kamata ba, sai dai ko kadan hakan be damu Abdulhamid ba saboda a tunaninsa ina son saka damuwar yara a raina ne.

GOBE NA (My Future)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora