53

2.4K 333 262
                                    


ABDALLAH POV.

Misalin tara da yan mintuna ya shigo gurin Hajiyarsa kana kallonsa kasan yana cikin damuwa. Yayyen Hajiya ya tarar a falon wato Hajiya Altine da Hajiya Rukaiya, sai da ya gaishe su sannan ya wuce dakin mahaifiyarsa, yadda ya same ta zaune saman carpet rike da carbe fuskarta da damuwa sai ya kara jefashi a cikin nasa damuwar. Kusa da ita ya zauna bakin gado yana kallonta da Fuskarsa da ke bayyana damuwarsa karara.

“Hajiya barka da dare”

Ta dago ta kalleshi kana ganin idonta ka san ta sha kuka.

“Barka dai Husaini, ya aikin”

“Alhamdulillah, Hajiya ki rage saka kanki a damuwa, In-Sha-Allah za a ga Abdulhamid”

“To Allah yasa ni abun yanzu har tsoro yake ba ni, jikina yayi sanyi sosai, idan na duba sai na rasa abunda Abdulhamid zai yi wa wani da zai cutar da shi mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, Allah yasa ba yan fillar kai ya hadu da su ba, domin na san masu neman kudi fansa da su suka kama shi da yanzu sun kira sun fadi abunda suke bukata”

Jimmmm Abdallah yai kamin ya kalleta a natse ya ce.

“Hajiya zaki iya tuna lokacin da akai yi Halima fyade?”

“Na sani”

“Mutumen da yai mata fyade wani kirista ne, kuma abokin Abdulhamid ne, ban san miya kai shi gidan ba har yai ma Halima fyade, a yanzu kuma ina kyautata zaton kamar da sa hannunsa gurin dauke Abdulhamid”

Cikin tashin hankali Hajiya ta kalleshi.

“Kamar kai ya akai ka sani?”

“Halima ta fada min mutumen ya dawo yana sonta, saboda cikin da tai shi kuma haihuwa yake nema, bata aminta da shi ba amman ya dage yana son ta aure shi, shiyasa na fada mata gaskiyar cewar shi yai mata fyade, sai dai ita bata san yana da alaka da Abdulhamid ba, ni kai dai na sani nima kuma saboda na taba ganinsu tare har hotuna sun yi tare, shi mutumen police”

“To me zai saka ya dauke Hassan?”

“Saboda ni na fadawa Abdulhamid gaskiyar daya kasa yarda da Halima a lokacin da abun ya same ta, ke da shi kuna ganin kamar ta aikata zina ne, yayi ta bakinciki yana fadar cewar shi Abraham zai ciwa amana, wata kila yai masa magana ko yai masa wata barazana shi kuma Abraham din ya dauke shi”

“Amman miyasa baka fadi wannan ba? Sai yan sanda su bincike shi mutunen?”

“Hajiya idan baka iya kama barawo ba, sai barawo ya kama ka, shi Abraham din police ne kuma da na bincika sai na samu labarin cewar baya cikin garin nan a office dinsa ma har an saka wani, amman mu saurara na kwana biyu tukuna tun da mun kai report din gurin Police kuma ana Addu'a, ko minene zai bayyana In-Sha-Allah”

“Amman irin wannan ai kama shi za ayi a bincike shi ko kuma ita Halimar, waya sani ko ma ita ta saka shi ya sace shi saboda ta dauki fansa balle ta ji zai yi aure, kuma ta ga shi Abraham din yan sonta”

“Haba Hajiya wane irin Halima kuma?”

“Zata iya yin komai wannan yarinyar da kake gani, ni sam ban yarda da ita ba ma”

“Babu hannunta a cikin nan, kuma na fada miki ki bari nan da kwana biyu idan ba mu ga wani abun ba, sai mu fada musu wanda muke zargi”

“To ko ma dai minene Allah ya bayyana shi”

“Amin”

Yayi kusan awa daya a dakin sannan yai mata sallama ya fice. Aiko kamar fitarsa take jira ta fito falo ta labartawa yan'uwanta abunda ya faru dukansu sun cika da mamaki.

GOBE NA (My Future)Onde as histórias ganham vida. Descobre agora