49

2.2K 293 199
                                    

A lokacin daya fito falon ya samu Mahaifiyar Aminu da wata yar'uwarta da dan'uwan mahaifinsa.
  Ganin Ahmad yasa suka kara marairaice fuska, shi kuma ya mikawa namijin hannu suka gaisa. Sannan ya amsa gaisuwar da mahaifiyar Aminu ke musu.

“Case din ba a hannuna yake ba, kuma ba ni aka jiwa ciwon ba, so if ita Halima tace ta yafe then ur son is free”

“To yanzu ita zamu je mu roka kenan?”

“Definitely”

Hajiyar Aminu ta marairaice fuska.

“Dan Allah dan Annabi ka taimaka mana, a saki Aminu hankalinmu duk a tashe yake”

“Haba Hajiya me kike so nace miki dan Allah? Idan Halima ta hafe masa Wallahi ba ni da matsala ni”

“Idan kai baka san ni ba ai ita Hajiya ta san ni, dan Allah kira min ita Yarinyar”

Ta karasa tana kallon Siyama, ba musu Siyama ta tashi ta nufi sama, bata dade ba ta sauko tana latsar waya.

“Gata nan zuwa”

Ba a bata lokaci ba Hajiya ta sauko ta zauna saman kujera, tana yi ma Hajiyar Aminu kallon rashin fahimta.

“Hajiya ina wuni?”

“Lafiya kalau ya gida?”

“Alhamdulillah Hajiya ba ki waye ni ba?”

“Wallahi ban gane ba, kila an kwana biyu”

“Be ke kika yi Shugabar lamurran mata ba, a lokacin Gwanna Garba Doru?”

“Eh Haka ne”

“Ni kuma ai na yi bawa matar Gwanna shawara a wacan lokacin”

“Allah sarki kin san abun da yawa, ya kwana biyu”

“Alhamdulillah, dan Allah Hajiya alfarma nake nema ki saka baki dan ki ya sako min da na Aminu, ance yana hannun sojoji dazun sun kira ta wayarshi suka sanar mana suka ce wai ya samu matsala da dan wajenki, shi kan shi Aminun na san be san Gwarzo ba da ba zai yi fada da shi ba Wallahi”

Hajiya ta kalli Ahmad.

“Wani abun ya hada ku ne?”

“No ba komai, kawai dai ina tare da Halima ne dazun mun je yin wani abu, sai ya fito a titi yana mana ihu kamar mahaukaci, kamin nai wani abu ya buga ta da mota, that's why na kira Faruk yasa a aka dauke min shi”

“Subhanallahi, to ita Halima ta san shi ne daman?”

Hajiyar Aminu ce ta amsa mata.

“Eh shine baban yayanta, tsohon mijinta ne da kaddara ta raba”

“Allah sarki, Gwarzo ka kyale shi dan Allah”

Ta karasa tana kallon Ahmad, shi ma kallonta yai.

“Ba ni da matsala Hajiya, kawai taje ta bawa Halima hakuri ita akai wa laifi idan ta hakura, shikenan ai ba matsala ba ce”

Hajiya ta sake kallonsu.

“To kuje ku ji ta bakinta idan ta amince a sake shi, ba matsala ba ne, tunda ita a kaiwa laifin yana da kyau aji ta bakinta”

“To Hajiya, bara muje indai Halima ce ai bata da matsala”

Cikin rashin jindadi Hajiya ta tashi tare da yan'uwanta suka fice. Siyama kamar jiran take su fita sai ta kalli Ahmad da sauri.

“Yaya ina kuka je hala?”

Kallonta yai yasan ba komai ke cinta ba sai gulma, ashe duk abunda ake hankalinta na gurin amman ta fake da latsar waya.

“Wani guri”

GOBE NA (My Future)Onde histórias criam vida. Descubra agora