24

1.5K 190 8
                                    

A yanzun ma ina bukatar wani ya tsaya min? Har a yanzun ma akwai wata hujja da nakr bukata kamin na gamsar da Abdulhamid ko wani da yake kusa da ni cewar an shigo gidanmu? Bayan fasa min baki da sukai ga kuma halbi da balle kofar falo, ashe har da gate din gidan suka fasa mana, sai dai maganin bachin da na sha bachin da na sha be bar ni na ji bude gate din ba sai na kofar falo.
  Sama sama nake jin maganar da su Mama da sauran kanena mata na yi, ban bude idona ba balle na iya tantance dare ne ko safiya ko kuma rana, sai dai a haniyar da nake ji kusa da ni har da Abdallah da wata macen da nake jin suna ta kira da Doc Safiyya.
 
“Halimatu....”

Macen ta kira sunana, sai dai ban iya amsawa ba saboda ban yi zaton akwai sauran magana a bakin da nake jin kamar babu shi a sauran halittar jikina, saboda zugin da na ke ji. Kamar a mafarki na ji ta taba bakin ba shi na bude ido na zabura na tashi zaune da sauri.

“Sannu...”

Shine abunda ya fito daga bakin Abdallah yana kallona da mugun tausayi. Ban san yadda bakin nawa yai ba amman ina jinsa kamar ya min nauyi ga wani uban zugin da yake min kamar an cireshi. Fita yai ya bar mana dakin likitar ce ta gyara min bakinta ta saka min bandeji sannan suka canja min daki zuwa wani.
  A lokacin da aka shiga da ni a na kiran sallah asuba, tun da na lumshe idona ban bude ba har Abdallah ya shigo yana miki min waya.

“Mijinki yana son waya da ke”

Ban bude idona ba ban kuma yi wata alama ta zan bude din ba, har ya gaji ya maida wayar a kunnesa ina jin yana fada masa cewar bachi na ke. Yana fita Mama ta shigo da shesshekar kukanta ta zauna a kujerar da ke kusa da gadona, a lokacin ne na bude idona na kalleta idonta sun yi ja sosai alamar kuka tai da yawa.

“Sannu Halimatu...”

Daker na gyada mata kai sannan na sake maida idon n lumshe, ban sake budewa ba sai da rana ta soma haskowa cikin dakin. A wannan karon ba Mama na gani ba Inna ce zaune a mazaunin Mama.

“Sannu”

Nan ma kan na gyada mata ina jin ya min nauyi kamar ba nawa ba. Da kanta ta je ta kira wani likita namiji ya zo ya duba ni ban samu matsala ta ko'ina ba sai ta bakina shi ma kuma gindin bindigar da suka buga min ne, kamar wata karamar yarinya haka na zama duk yadda aka so na ci abu sai na kasa saboda zafin da bakin ke min. Ruwa kawai na sha shi ma kadan, sannan na tashi na shiga bandakin da ke cikin asibitin nai alwala na gabatar da sallah asuba. Ina sallame sallar abunda ya faru ya dawo min, a wannan karon ban samu wata shaida kmar wacan karon da na samu zoben mutumen ba wanda na ganshi a hannun Abdallah, a yanzu abunda nake ta kokarin shine siffanta surar mutumen ko zan iya gano waye ne yake min haka, idan an siffanta shi da Abdallah sai idanuwa su nuna min kamar Abdallah ya fi shi jiki, wata kila kuma dimaucewa ce ta sa ba zan iya tantancewa yadda ya kamata ba.
Idan ba Abdallah ba waye? Wana tarewa wani abu? Amman miyasa zan yi ta zargin Abdallah? Saboda shi ya saka ki a gaba ya hana ki rawar gaban hantsi, ita ce amsar da zuciyata ta ba ni.
  “Ba mu san cewar mijinki baya nan ba, wannan karon ba gurin mijinki muka zo ba, da gaske akwai ciki a jikinki?”

Su ne kalmomin da ke ta maimaita kanta a cikin kwalkwalwata, dalilinsu na ke bukata, da gaske ba su san cewar mijina baya gari ba? And idan ba a gurin Abdulhamid suka zo ba, me za su zo su yi gurina? Fyaden suka sake zuwa su min ko kuma wani abun dabam? Ban raba dayan biyu ba Hajiya tai sallama ta shigo tare da yar autarta wato kanwar su Abdallah, Inna ce ta amsa mata, ni kuma na juyo daga saman carpet din da nake zaune na kalleta. Ba shakka na ga tausayi a fuskarta tana ta min sannu ina gyada mata kai domin har lokacin ban yarda wata kalmar ta fito daga bakina.

“Ta ci abincin?”

“A a ruwa kawai ta sha shi ma kadan”

Inna ta bata sai ta sake cewa.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now