20

1.7K 195 18
                                    

DEDICATED THIS PAGE TO Mai Dambu, Allah kara miki lafiya Gwanata❤ son so Fisabilillahi💞😍

                  ***        ***      ***

Kamin mu isa gidan har wani jiri nake jin yana dibana, zuciyata kam kamar ta fashe ga wani uban zafi da kirjina ke yi, kaina sai sarawa yake.
   Ko parking din kirki be yi ba na bude motar na fita na shiga cikin gidan cikin tashin hankali kamar yadda su ma na tararda su cikin tashin hankali, gaba daya ban tarardar yan mata gidan mu ba da samarin biyun duk sun fita neman Namra Baba na tsakar gida rike da sandar damuwa kara a fuskarsa. A bakin balcony na zauna na dafe kaina. Inna na min bayanin yadda abun ya faru da guraren da aka je nemanta bata can. Mahaifinta ne ya fado min a rai.

“Ko Aminu ya dauke ta ba a sani ba?”

Na fada ina kallon Mama, a yayinda Abdulhamid ya shigo yana gaisawa da su.

“Mi zai saka Aminu ya dauke ta, mutumen da tun da ya bata baya be sake dawo ko tambayar lafiyarsu ba”

Cewar Inna sai Mama ta karba mata.

“Nima dai shi na gani, kuma a ina ma zai ganta?”

“Ko tana gidan Abdallah?”

Na fada ciki ina hawaye.

“A a bata can tun dazun da shi ake ta nemanta, shi ma yace kar a fada miki saboda kar hankalinki ya tashi, yanzu yanzu ma suka fita da Samira har.... ”

Baba ne ya tari numfashin Inna da ke maganar yana fadin.

“Ku ba Allah cigiya In-Sha-Allah za a ganta, idan ba dan sake irin na Hafiza ba taya zaka fita da yaro ka ce ya same ka titi bayan yaron be san gurin ba”

Komawa nai na zauna a gurin na fara rare musu kuka, idan ba kukan ba ban san abunda zan yi a yanzu ba.

“Bari naje na duba makarantarsu...”

Cewar Abdulhamid yana kokarin juyawa sai Inna tai karaf tace.

“Ai har can Abdallah ya tafi....”

Baba ya sake saurin tarar numfashinta.

“A a be je can ba, islamiyarsu dai yaje, zaka iya zuwa can ka duba”

Sai da Abdulhamid ya fice sannan Baba ya hau yi ma Inna fada wai ta cika tsoma baki a maganar da babu ruwanta. Ni kam sam ban ga illar maganarta ba kamar yadda ita ma kanta da Mama ba su ga haka ba, wata kila kuma akwai abunda Baba ya hango.

“Mama zan je gidansu Aminu na duba ko tana can”

“To da Abdulhamid din be wuce ba ai sai ya karaki”

“A a shi yaje can din ni zan duba gidansu Aminu”

Na bawa Mama amsar ina mikewa tsaye.

“Mi zai kaita can ma”

“Nema ne ai Mama”

Ban tsaya na jira su kara kashe min jiki ba na zari jakata na fito cikin gidan kamar wata mahaukaciya. Kamin mai napep din na kai ni gidan su iyayen Aminu har na matsu abunka da wanda je cikin tashin hankali. A bakin gate ya tsaya ni kuma na shiga cikin gidan da sallama. Kana gani na kasan hankalina ba a kwance yake, ba Hajiyar Aminu ba ko kanensa sun yi mamakin ganina a cikin gidan, ban musu magana ba kamar yadda suma suka saki ido suna kallona kamar wata bakuwarsu. Har cikin falon na shiga na gaishe ta ita ta amsa min da dan mamaki sannan na tambaya ko Namra tana nan.

“Namra da kuka kekashe kasa ke da yan'uwanki kuka ce ba za ku bayar ba, bayan kun gama ikirarin an bata ta mi za mu dauko ta tai mana? Ai mun yafe miki ita ki dafa ki ci ko ki saida babu abunda za mu da ita”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now