52

2.3K 310 178
                                    

Garin daukar cingan din naji na taba wani abu mai kamar karfe, da na ciro cingan din na duba da kyau sai nai arba da makullin mota.
  Ba shiri na mike tsaye ina dubawa duk da bani da motar ina kallon wannan makullin na san cewa na mota ne, wani irin faduwa gabana yai sai an rasa abunda zan yi kuma na kasa yarda cewar makulin motar ne, yana sane ya saka min shi ko? Ko dai ba da gangan yai ba. Maida makullin nai na dauki box din na nufi office dinsa.
  Tsaye na tararda shi jikin fridge ya kafa gorar ruwa a bakinsa yana sha, ganina yasa ya sauke ruwan ya juyo yana kallona.

“Ina....ina tunanin ka yi mantuwa a box din na ga wannan”

Na fada ina budewa na dauko makullin na nuna masa. Sake cika bakinsa yai da ruwan sannan ya aje ruwan ya rufe fridge din.

“No ina sane na saka, na yi ta tunanin abunda zan ba ki as birthday gift, sai na ga babu abunda ya dace a yanzu nai miki kyauta da shi kamar mota, saboda zuwa aikin da kike sai ki huta da hawan napep”

“No i can't accept this”

Na fada ina nufar teburinsa na aje makullin.

“Lims why”

“A'a Halima dan Allah, ranka ya dade kana min abunda ba a cikin dokikin kamfanin nan yake ba, ko da kana taimako ina tunanin kana taimako na ne saboda Allah, ba zan iya karba kyauta mai girma irin wannan ba, bana son alakar mu da wuce haka”

“Why? Kina tsoron an sake shiga rayuwarki? Saboda Aminu ya cuce ki? Abdulhamid ya juya miki baya? Abraham ya yaga rigar mutuncinki? Dukansu maza ne ko ba haka ba? Kina tsoron ki sake komawa wani hali ko? Kina tsoron kar wani yace yana son ki wata rana ya juya miki ba right? Kina da gaskiya kuma kina da hujja kuma dole ayi miki uzuri....”

Ya matsa kusa da ni sosai yana kallon cikin idona.

“Duk abunda nake miki, ina yi ne saboda na ga na faranta miki rai, ba ke kadai kika cancanci farinciki ba, nima na cancanci farincikin, amman na danne nawa na manta da nawa, na danne duk wani bakin rai da damuwa da suke raina, saboda ke na sama miki farinciki, daga lokacin da samu labarinki sai nai kokarin mantawa danawa kin san saboda me? Saboda tausayinki ya cika min zuciya”

Ya kara matsowa daf da ni.

“Dukan abunda nake miki ina yi ne saboda zan iya kuma saboda na fi karfin abun, ba zan taba yi miki wani abu dan kawai ya tambayi so daga gareki ba, zuciyata bata taba raya min na siye soyayya kowa ba, balle kuma ke, ban taba jin cewar nai miki wata kyauta ko wani abun jidadi dan na tambayi soyayyarki da shi ba, Lims ina son shiga rayuwarki na taimake ki na taimaki yayanki da yan'uwanki”

Na yi saurin kaucewa ina aje numfashi.

“Ni ban shiryawa aure ko soyayya a yanzu ba, duka mazan nan da suka yaudare ni babu wanda be nuna min so na gaskiya ba, amman daga baya komai ya canja, kai mai gidanane be kamata alakar mu da wuce haka ba, indan har da gaske taimako na zaka yi to ka taimake ni saboda Allah kawai”

Dayan hannunsa ya saka aljihu, ya juyo yana kallona.

“Ni ma ba zan bari kiyi yanka akan danye ciwo ba, ai baki gama warkewa daga ciwon ba, ke kike kokarin saka kanki a so ba ni ba, na kai ki a restaurant din da nake cin abinci ne har na zaunar da ke a kujerar da kike zargin wani abu ne saboda na yarda da ke, na daukeki yar'uwa ne shiyasa na tura miki sakon cewa I'm not just your friend, na aika miki da sakon birthday ne a gidanku saboda kina daga cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata, dukan abunda nake miki saboda kawai ina tausayinki ne kuma ina son ki samu farinciki, idan zan siye soyayyarki ba ta wannan sigar zan biyo ba, shim fada min na taba furta cewar ina son ki? Ko na taba zuwa gidanku da sunan zance? Idan zan nemi aureki a gurin iyayenki zan tafi ba a gurinki ba, domin ni kallon budurwa nake miki yar 18, ba zan yi magana da ke ba har sai da izinin iyayenki, amman abubuwan nan da nake yasa kin fara tunanin son ki nake? Ashe son ki yana da arha da yawa”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now