GN-07

1.8K 231 19
                                    

Hawayena na share na tashi na shiga dakina nai alwala na soma gabatar da sallah azahar, ina Sallah shiedan na ta kawo min wasu abubuwan da be kamata nai tunaninsu a lokacin da nake a gaban Ubangijina ba, sai dai na yi nasarar fadawa Allah bukatata kuma na kai masa kuka. A lokacin da na sallame sai addu'a ta subuce bakina saboda tunanin da ya taru yai min yawa. Ida har na hakura na bar rayuwar Namra ta tafi a haka ni tawa rayuwar zata inganta kuwa? Taya zata inganta bayan yata zata kasance cikin kunci? Kyale Baba Sadi zai canja mishi hali ne daga abun yake? No sai dai ya kara masa kwarin guiwar yin hakan saboda an kyaleshi, hakan kuma ba zai saka Aminu sauya halinsa ba, miye ma amfanin zama da mutumen da ke mu'alama da wasu matan a waje, wanda har ya zama silar lalacewar ta wa yar? Shin yin shiru zai amfanin wani abu ne? Jin bugun kofar falo ne ya dawo a ni daga duniyar tunanin da na tafi. Tashi nai sanye da hijab da nai sallah na nufi kofar falon, ina budewa na ga Abdallah tsaye rike da hannun Adnan dayan hannunsa kuma rike da leda fara irin babbar nan ta pharmacy, Aiman kuma na gefensa, sam na manta da zancen dauko su daga makaranta sai yanzu.

“Be kamata ace har yanzu kina barin kanen mijinki yana zuwa dauko yaranki daga makaranta ba, domin idan be samu mace ba mazan zai iya lalata su tun da duniyar ta canja ba maza ba mata”

Shine abunda ya fada min kai tsaye, ni kuma na kwara bude kofar falon.

“Adnan ku shigo ciki”

Da sauri suka shiga falon ni kuma na fito na tsaya bakin kofar falon na janyo kofar na rufe.

“Kin yi kuka da yawa Halima ga fuskarki nan ya nuna, kina tunanin kuka zan canja komai ne? Kina tunanin kukam zai saka Kanen mijinki nadamar abunda yai? Ko kuma mijinki zai fasa neman matan da yake ne yana gallaza miki? Haka zaki saka ranki a kunci kina ta damuwa?”

Kasa nai da kaina ina jin wasu hawayen suna kokarin cika min ido.

“Na je gida na kai miki yaran na yi tsammani kina gida, sai suka ce kin zo kin tafi, tun da na ji haka na san cewar sun karya miki kuiwa ko? Su baki shawarar rufe sirrin saboda kar wani yaji, Kanen mijinki ya ci bulus kenan? Bayan ya ci amanar dan'uwansa, rayuwar aure ba rayuwar kunci ce ba Halima, saboda kina neman lahirarki ko kuma kina son kyautata rayuwarki be kamata kullum ki yi zama da kunci kina tauye kanki ba, musulunci ma be yarda da irin wannan auren ba, yaushe rabon da ko kusantarki mijinki yai?”

Hawaye ya fara sauko min, tabbas Abdallah yana da gaskiya akan dauki wata daya biyu wani lokacin har uku kamin Aminu ya zo min da bukatarsa.

“Ba sai kin fada min ba na sani, namiji mai neman matar sosai kamar yadda Aminu yake baya iya kula matar gida, duk abunda zaki yi ba zaki burgeshi ba saboda idonsa sun bude akan wasu matan na waje kuma ya yarda sun fi ki komai, so baki da wata daraja da kima a idonsa, yana yawan fadar baya son mace mai irin siffarki halittarki bata burge shi, kuma kin tara masa yayana yana da kananan shekarunsa a lokacin da yake bukatar hutu ke kuma kika son hana shi jindadin rayuwa, shiyasa yake gallaza miki”

Dagowa nai na kalleshia fusace na ce

“Kana ta fadin karya da gaskiya akan mijinki, tsayawa a ina saurarenka ba shi yake nufin na yarda da kai ba, baka san komai akan mijina ba babu ruwanka da rayuwarsa”

“Kwarai na san komai akansa, da yawa daga abokansa ina hulda da su kuma kin sani mazinata basa da sirri, har jinjirin cikin da kike dauke da shi na sani Halima, babu wanda be san irin zaman da Aminu yake da ke ba a cikin abokansa, saboda mijinki ba shi da sirri, ban san taya akai ma kika auri Aminu ba Halima sam ba mijin daya dace ki aura ba ne”

“Baka isa ka shigo har cikin gidana ka ce zaka fada min wata maganar banza akan mijina ba, ka fice”

Cikin wani irin tsawa na nuna masa gate raina na bace, daman ya saba a duk lokacin da muka hadu da shi sai ya fada min wata maganar marar dadi akan Aminu. Murmushi yai ya tabe baki ya miko min ledar hannunsa.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now