48

2K 305 170
                                    

Tun daga yanayin tafiyata zaka fahimci ina cikin wani irin nishadi marar misaltuwa,  na fito daga cikin gidan na nufo inda motar Ahmad take fake ya sauke gilashin motar yana kallona har na karaso, da kansa ya miko hannunsa ya bude min motar, na shiga ciki na zauna ina gyara jakata. Sai yai motar key muka hau titi sannan ya kalleni.

“Happy?”

Na gyada masa kai idanuwana suna kokarin cika da hawayen jindadi.

“Yes”

Sai yai kyakkyawan murmushin daya karawa fuskarsa kyau.

“Thank You”

“No thank you da kika amince, hop dai kin fada musu ke za ki yi ba ni ba”

Na yi shiru ina kallon gorar ruwan daya dauka zai sha.

“Sun jidadi sosai, kuma sun yi supporting”

Murmushi kawai yai ya kalle ya karasa kurbe ragowar ruwan, ba mu yi wata tafiya mai nisa ba ya faka gefen titi yana kallona.

“Bari na karbo ruwa shagon can, bana iya zama ba ruwa a mota”

Bude motar yai ya fita, da wani irin kallo na bishi na jindadin daukar nauyin duba lafiyar Kabir da yai, haka Allah yake lamarinsa idan ya zo taimaka maka sai ya maka hanyar samun abun ko ta ta silar wani ne, and farincikin dana gani a fuskar yan'uwan Kabir a yau da naje musu da labarin ya kara faranta min rai fiye da kima. Wata farar mota ce ta faka gaban ta Ahmad sam ban kawo komai a raina ba, har sai da na hango Aminu ya fito daga cikin motar a fusace ya nufo inda nake, ganin hakan yasa na bude motar na fito na rufe tun kan ya karaso.

“Halima me kike a cikin motar nan?”

Haka ya aiko min da tambaya kamar wani ubana.

“Ban gane mi nake a ciki ba?”

“Abunda kike be dace ba, tun dazun na hango ki a cikin motar nan ina biye da ku har kika shiga wani gida kika fito, ya kamata ki san abunda kike fa wannan ba muharramin ki bane, kuma ki rika tunawa cewa kina da yara”

“Wace irin magana kake yi haka Aminu?”

“Kin san me nake nufi”

Ya fada yana kara hade fuska, sai wani huci yake kamar ba shi ba.

“Ya akai?”

Ahmad ya tambaya yana kallona hannunsa rike da gorar ruwa biyu.

“Ba komai”

Na fada ina dauke idona daga barin kallon Aminu.

“Oh ba komai za ki ce masa? Malam akwai komai wannan mata ta ce, miye hadin ka da ita?”

“Who's this?”

Ahmad ya tambaya yana kallona. Sai Aminun ya amsa masa da kansa cikin fusata.

“Mijinta ne uban yayanta”

Wani kallon uku saura kwata Ahmad yai masa.

“Sannu Uban yaya, da alama dai kana shaye shaye, domin mai hankali ba zai yi abunda kake yi ba”

“Ba shaye-shaye nake ba, ciye ciye nake, ka fita hanyar tun kamin dare yai ma, domin matata ce”

“Babu wani abu a tsakanina da shi Aminu, boss dina ne a gurin aiki, kuma kai baka isa ka hanani magana da wani namijin ba, domin babu igiyar aurenka a kaina”

“Amman akwai yaya a tsakaninmu ko?”

Ya fada cikin daga murya mutane har sun fara mana taro, Ahmad ya bude min front seat.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now