21

1.9K 210 17
                                    


ABDALLAH POV.

Yayi parking daidai da lokacin da yake sauke wayarsa daga kunne. A natse ya bude motar ya fita ya nufi kofar shiga falon. Da sallama ya shiga falon kamar yadda ya saba, Suwaiba ta amsa masa murya kasa kasa ba tare da ta kalle inda yake ba sai aikin latsa waya take. Kusa da ita ya zauna yana sauke gajiya idonsa na kan matarsa.

“Kawo min ruwa”

Ya fada bayan ya kai hannu ya fisge wayar daga hannunta, facebook take kan wani page na Real Life Diaries, sannen shafi ne da yake wallafa matsalolin mata da mazan ma aurata domin samun mafita ta addu'a ko shawara ko taimako idan ta kama.
  Sama sama ya duba labarin page din wani gurin yai dariya wani abun kuma yai tsaki musamman idan ya leka comment section.

“Gashi”

Ta mika masa ruwan fuakarta ba yabo ba fallasa bayan ta bata yan mintuna kamin ta kawo masa.

“Ni na manta when last na leka page din nan, wani lokacin post din mutane bata min rai yake wallahi”

“Wani lokacin kuma ana samun mafita ai, shiyasa ake yin posting din”

Ta fada tana kokarin zama kusa da shi wato a inda ta tashi dazun. Kallonta yai kamin ya kai ruwan a bakinsa ya shaye gaba daya sannan ya aje kofin ya kai hannunsa ya janyota ta kwanto jikinsa.

“Ya akai Subee? Fada min matsalar ki”

“Babu komai”

Ya fada still fuskarta na nuna akwai damuwa.

“Ba mu saba boyewa juna damuwa ba, fada min matsalarki”

“Ba komai”

Ta sake maimaitawa. Wayarta ya mika mata yana fadin.

“Ba ki tambaya ko anga Namra ba?”

“Ai na san an ganta, da ba a ganta ba da ba zaka dawo gidan nan ba”

Kallonta yai for few seconds sai kuma yai murmushi as usual.

“Shine abunda ya bata miki rai?”

“Tun safe ka fita gidanan baka dawo ba sai yanzu, ko rantsuwa nai ba zan yi kaffara ba wata kila ko aiki baka je ba, ka tashi hankalinka gurin neman yarinyar nan wanda na san ko Inteesar ta bata ba zaka tashi hankalinka kamar haka ba”

Wannan karon raba jikinsa yai da nata ya juyo da kyau ya kalleta yana karantar yanayinta.

“Yar yar'uwata ce ta bata fa, ita ma din kamar yata ce”

“Ta ma fi yarka ai, gatan da kake musu baka ma yayanka wannan gatan, makarantar da ka saka su Inteesar 60,000 ake biya duk bayan wata uku amman Namra makarantar da aka saka su dubu 130,000 ake biya duk term”

“And...?”

“And ba su da wanda zai dauki dawainiyarsu ne sai kai Abdallah? Why kai why?”

“Amman ai kin san mahaifinsu ya rabu da Halimatu ko? Kuma yaran nan a yanzu abun tausayi ne suna bukatar tallafi a rayuwarsu, kuma Halimatu yar'uwata ce kin fi kowa sanin haka”

“Dan ya rabu da ita sai dawainiyarsu ta dawo kanka? Miyasa Abdulhamid b dauki dawainiyarsu ba? Be fika kusanci da mahaifiyarsu ba?”

“Abdulhamid babu ruwansa da yara kin sani, ba sai an fada miki ba”

“Amman ita kadai ce mai yaya a familynku? Miyasa ba kai wa wasu ba sai ita? Komai daga ita sai familynta? Lokacin da Hafiza ta zo nan ta fada maka Namra ta bata kuka fita tare ko magana ba ka min ba”

“What are you try say?”

“Dawaniyar ta maka yawa Abdallah, kai mata kai wa iyayenta kai wai yayanta kai wa yan'uwanta why?”

GOBE NA (My Future)Όπου ζουν οι ιστορίες. Ανακάλυψε τώρα