GN-13

2K 214 23
                                    

“Kamar baki da gaskiya Halimatu...”

Sai da na kalli Mama sannan na kalleshi.

“Bana da gaskiya kamar ya? Wannan wace irin magana ce Abdallah?”

Ya dan tabe baki yana ta wasa da hannun Amal kamar ba shi yai maganar ba. Kamar an daki hannuna sai na yi yai min majiyar, ban san lokacin da na saki wayar hannuna ta subuce ta fadi kasa, a take ta watse a saman tedar da ke falon kamar abar da aka taka da mota ko aka sakawa dutse aka daddaka. Subhanallahi Mama ta furta ni kuma na risina a gurin ina kallon wayar ina jin kamar na fasa kuka tuni idona suka cika da kwalla, har ga Allah na tsani na rasa wani abun da na ke matukar so ko yake da muhimmancin sosai a rayuwata, na san phone ce amman ina jin babu dadi domin samun irinta a yanzu ba abu mai sauki a gareni a lokacin da na ke gidanmu dawainiya ta zata min yawa yanzu fiye da, ga kuma zuwan da Abdulhamid zai yi ban san abunda zai kawo shi ba wata kila ma baya son kowa ya san da zuwansa.

“Ya akai wayar ta fadi?”

Mama ta tambaya sai an amsa mata muryata na gargada alamar ina daf da fashe da kuka.

“Ban sani ba Mama a hannu ta zame ta fadi”

“Laa shikenan wayar Momy ta fashe bamu da wayar game”

Namra ta fada tana wani bude baki, Abdallah kam ko dago kai be yi ya kalleni ba sai wasa yake da yatsun Amal kamar be san abunda ya faru ba.

“Momy yanzu da wace wayar za mu rika game...?”

Wani bakin haushi na ji ban san lokacin da na dakawa Namra wacce tai maganar tsawa ba.

“Da wayar ubanki... ”

Sai a lokaci Abdallah ya dago ya kalleni sai kuma ya kalli inda wayar take ba ce min komai ba sai dai fuskarsa ta nuna alamar bachin rai, mikewa yai tsaye yana saa dayan hannunsa a aljihu.

“Mama ni zan tafi, kuma yaran nan a yi kokarin saka su makaranta domin barin su hakan nan ba zai yiyu ba ya kamata a san abun yi lokaci na ta tafiya”

Wata uwar harara na watsa masa saboda haushinsa da na ke ji, wacce be san ma ina yi ba domin be kalli inda na ke ba da Mama yake ta maganarsa, ita kuma tana nanata masa cewar za a saka su makarantar, hannu ya saka aljihu ya ciro kudin da ban san ko nawa ne ba ya aje mata a hannun kujerar da take zaune sannan ya karaso inda na ke duke ina ta kallin wayar da na gagara tattarawa na kwashe ya ce.

“Halimatuuu mu kwana lafiya”

Har na yi kamar na bude baki na aika masa da bakar magana sai kuma wata zuciyar ta hanani ganin a gaban Mama ne da kuma yara. Tare ya fita da Amal da Namra Aiman ma ya bi bayansa.

“Halimatu kina jin yana miki sai da safe amman kika gagara karba mishi miye haka?”

Mama ta fada cikin yanayin damuwa da rashin amsa masa da ban yi ba.

“Mama ba ki kohi yai min wayar ta fadi ta fashe ba”

“Kohin zai saka waya ta fadi har ta fashe? Ai naga ko kallon ki be yi ba kuma ba wata maganar ta bacin rai kika masa ba balle ace, abu ne dai da Allah ya kawo”

Ban sake cewa komai ba na tattara wayar na mike tsaye na nufi dakin Mama na zauna bakin gadonta kamar wacce aka kwashewa tunani a kwakwalwa, babu komai a raina sai bacin ran faduwar wayata, ina zaune a gurin yara suka shigo da yan dari biyar biyar a hannu wai Uncle Abdallah ya basu, ni dai ko kallonsu ban yi ba balle har na karbi kudin na adana musu saboda bakin haushin Abdallah da na ke ji.
Ban yi dabarar na karbi wayar daya daga cikin yan matan gidanmu na kira Abdulhamid ba sai da aka sallame sallar isha'i, a lokacin kuma yan zaman majalisar kofar gida sun soma shimfida tabarsu su zauna. Idan ma nace zan yi magana da shi sai dai na koma ta kofar gidan makotan mu wanda hakan ba zai min dadi ba domin a hanya ne.
Ban yi kasa a guiwa ba na karbi wayar Hafiza na lalabo number Abdulhamid a wayarta na aika masa da kira, kamar jira yake a take tai picking din call din yana rangadamin sallama, bayan na amsa na koro masa da bayanin wayata ta fadi har ta fashe.

GOBE NA (My Future)Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu