32

1.6K 216 23
                                    

Barka da Sallah Allah ya maimaita mana 🙏❤

Hannu na kai na rufe bakina, wannan karon ba kuka ido da baki kawai nake ba har da zuciya da kwakwalwa da jikina amsa amo yake. Kuka nake ta ko'ina irin kukan da ban taba yi ba, irin kukan da ban taba sani yana tare da ni ba karkawar nake kamar wacce ta shekara a cikin kankara hakorana na hadewa da juna suna wata kara, wani kalar hayaki nake ji a cikin kaina.

“Ashe har yanzun kukan be kare ba Halimatu”

Mama ce tai maganar sai na dago na kalleta tsaye take jikin kofar dakin da nake ita ma kuka take kamar ni. Kai na gyada mata kamar wani abun arziki sai kuma na ji ana fisgata kafafuwana suka kasa daukata, wani farin haske ya baibaiye idona tashin hankali da nake ji a yanzu bana jin cewar ko daya daga cikin yayana ne ya mutu zan samu kaina a yadda na samu kaina a yanzu.

“Ki ce Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un”

Mama ce take fada min abunda zan fada, ba dan ina ganin fuskarta ba, ba fuskarta kadai ba komai bana iya gani a yanzu sai dai ina jin hannunta a jikina tana rike da ni. Unkuri nai da zimmar na bude bakin na furta abunda ta umarce ni sai bakin yai min nauyi kamar ban taba magana da shi ba. Daga lokacin ban sake sanin inda nake ba sama nake kasa nake duniya nake ko a lahira ban sake sani ba, sai duniyar ta duburce min hankalin ya tafi numfashin ma yai min dogon zango....

AHMAD POV.

Tun bayan da aka kai Baby Namra a gidanta na gaskiya be sake zama a aje ba, duk wanda ya kira wayarsa ko ya zo gidan da sunan masa gaisuwa ba zai dauka ba ba kuma zai fito ba. Wani abu yake ji a tare da shi shi ba tsoro ba ba kuma fargaba ba, baya son ayi masa gaisuwar mutuwar yarsa, har yanzu kuma ya kasa saka komai a bakinsa bayan ruwa, ya kuma kasa jin komai a game da mutuwarta. Ita kanta Hajiya a yanzu tafi shiga tashin hankalin da gwarzo yake ciki fiye da jimamin mutuwar Baby Namra, ta fi kowa sanin danta yana da hakuri da juriya, sai dai wannan karon ta kasa banbance hakurin ne ko kuma damuwa? Ta san yadda yake son mahaifiyar yarsa balle kuma ita yartasa.

Yana tsaye gaban madubin dakinsa Hajiya tai sallama ta shigo jiki a sanyeye damuwa da bakinciki karara a fuskar uwa mai damuwa da ciwon danta. A bakin gadonsa ta zauna tana kallonsa har ta bude baki tai magana sai ya tari numfashinta.

“Hajiya Allah kadai yasan irin ihun da Baby tai kamin ta mutu, ita kadai ta san irin ciwon da ta ji”

Idonta ya cika da hawaye tana masa kallon tausayi.

“Ka fara jin zafin mutuwarta kenan”

Juyowa yai ya kalleta.

“Har yanzu dai, kawai na rasa dalilin da zai saka a kashe min ƴa ne”

Kallonsa Hajiya take da uwar ramarsa da rashin kuzari da yake fama da shi.

“Na kasa yarda cewar matar nan zata iya tura yarka a rijiya ta mutu bayan kai ka ceto ta ta yar, kullum mahaifinta da yan gidansu sai sun zo gaisuwa a gidan nan, babu yadda mahaifinta bw yi ba akan ya ganka amman saboda kace baka bukatar ayi maka gaisuwa na hana, ita kanta matar da kake zargi sun fada min cewar tana asibiti bata san inda kanta yake ba sanadin wannan abun”

Dan murmushi yai kadan na takaici.

“Hakan yana nuna da ganganta ta aikata, saboda ta ji nace zan daureta ne  shiyasa ta shirya ciwon karya”

Zuwa yai ya zauna kasa kusa da Hajiya ya dora kansa a saman cinyarta sai wasu hawaye masu zafi suka soma sauko masa.

“Hajiya kina iya tuna lokacin da take cewa bata son ta mutu ita kadai? Idan zata mutu zata tafi tare da ni da ke?...”

“Tana yawan fadar cewar bata son ta sha wahala idan zata mutu”

Hajiya ta karasa masa.

“Ta yi mutuwa mafi kaskanci Hajiya, ta samu rauniya ka dama, Allah kadai yasan wahalar da tasha kamin ta mutu”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now