57

2.7K 311 331
                                    

“Ban san abunda Hassan yake nema a duniyar nan ba, ban san wani abu da ya rasa ba, ban san kadarar da ta kai shi fadawa wannan mummunar sana'ar ba, na jama kansa masifa... Wata kila a kashe su wata kila a barsu su kasara rayuwar gidan kaso, amman ko da an sake su an kunyata su tun da an bayyana fuskokinsu kowa ya gansu, a lokacin da ya kamata ace ya samu farinciki sai kuma wannan kaddarar ta fado masa...”

Hajiya ce take wannan maganar hawaye na fitowa daga idonta, wani irin abu ta ji ya tsaya mata a zuciya tun daga lokacin da gaskiya ta bayyana har yau yana nan tsaye ya tokare mata kirji. Abdallah ya sauke ajiyar zuciya, shi kanshi shi jidadin halin da dan'uwansa da mahaifiyarsa suke ciki ba, no matter how bad your blood is, jininka jininka ne, and idan akwai wanda zai yi blame me a yanzu Ahmad ne domin shine silar faruwar hakan, duk kuwa da yasan abunda Abdulhamid yake ba abun kwarai ba ne, amman yana tunanin ya tona masa asirine saboda ya saka Halima ta so shi kuma ta guje Abdallah, miyasa da ya gano haka ne be fadawa Halima a sirrance ba sai a san yadda za a bullowa lamarin, amman ya zabi ya tozarta shi haka wanda silar hakan ga mahaifiyarsa a kwance tana fama da jinya. Idan har Ahmad zai iya kitsa cuta a zuciyarsa kamar haka then be yi deserve ya aure Halimatu ba, domin shi ma ba a san iya abunda yake sakawa a zuciyarsa ba kuma ba a san abunda yake a karkashin kasa ba, ya fada masa sai ya nuna masa shi din ba kowa ba ne a gurin Halima that's for sure sai yayi, duk abunda yai ko zai yi zai tashi a tutar babu ne, ko mazan duniyar nan sun kare he don't think zai bar Halima ta auri Ahmad, rayuwarsa tana nuna masa babu wanda ya cancanci Halima sai shi, duk da ya san Hajiya ba zata bari ba a yanzu wata rana zata bari, so zai jira har zuwa lokacin da zata yarda but right now all what he want is yai magana da Halima. Tun da har Ahmad ya saka bakinciki a zuciyar mahaifiyarsa shi ma sai ya saka a tasa zuciyar, sai ya nuna nasa kudinsa da wata isarsa ba su isa su siya masa soyayyar Halima ba.

“Duk yarinyar nan ce taja komai nasadinta komai ya faru, sam babu alheri a tare da ita, bata nufar mu da khairan ai sheran”

Hajiya ta fada tana kokarin dora laifin akan Halima a ganinta sanadinta ne asirin Abdulhamid ya tonu har haka ya same shi, domin shi mutumen daya shige gaba akai bincike aka tona asiri saboda Halima yai dan haka komai ma ya faru ita ce sanadi. Abdallah dai be ce komai ba sai saurare kukan mahaifiyarsa yake.

“Da na san haka zai Faru Wallahi da tun farko ban bar shi ya aureta ba, Halima ta zame mana fitina a cikin iyali, ta lalata mana komai na rayuwa Allah ya isa tsakanina da ita, ban san me nai mata ba ta tattara duka farincikin nawa ta dauke, ta tarwatsa mana komai har ta kai yau ga ni kwance saboda bakincikinta”

Sai a wannan karon Abdallah yace.

“Laifin wannan dan iskan ne, shine yai komai ai”

“Amman ai sanadin ne ko? Waya sani ko ita ta saka shi ma”

“Amman ai ba ita ta saka Abdulhamid a wannan harkar ba”

“Ko ba ita ta saka shi ba, asirinsa saboda wa ya tonu? Allah yana son mai rufawa dan uwansa asiri, idan ba dan su kunyata mu ba taya za su nemi yi masa wannan cin mutuncin”

Shiru yai yana jin tsanar Ahmad tana kara hauhauwa a zuciyarsa.

AHMAD POV.

Be taba yarda da gaske yana son Halima ba sai yau, domin farinciki da yake ji a tare da shi ya wuce misali. Taya zai kwatanta yadda yake jinta a zuciyarsa na amincewarta kawai ashe daman tuni ba tausayinta kawai yake ba har da son ta, driving yake amman gaba daya hankalinsa yana gunta after every one minute sai ya kalleta with smile on his face. Wani irin abu yake jin yana masa zillo a zuciya babu abunda yake ayyana aransa sai idan ya kai kasance a mijinta ya zai tsinci kansa? A hankali ya busar da iskar bakinsa ya kalleta wannan karon idanuwansa sun samu masauki a cikin idonta, sai tai saurin kawardar idonta shi kuma yai murmushi ya cigaba da tukinsa har suka iso cikin unguwar.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now