GN-12

2.4K 247 24
                                    


“Wallahi Anty karuwarsa ce kuma saboda ita wannan hadrin ya same shi, yanzu kuma dan rashin kunya har ta sako kafarta ta zo ganinsa? Haba Anty da wanne zan ji da ciwonsa ko da ganinta”

Ta fada cikin kuka ni kan tuni jikina yai sanyi jin abunda ya same Kabir jinin ya taba kwakwalwarsa, abun ya tsorani sosai kuma ya jefani a cikin wata duniyar tunanin da fargabar yadda gobensa zata kasance. Takawa na fara yi ina tafiya na nufo gate din fita daga asibitin gaba daya ba tare da na sake cewa komai ba, kallo daya za ka min ka fahimci akwai damuwa a tare da kamar yadda tunani ya kawo min ziyara a yanzu. Kar dai ace saboda ya rabe ni hakan ya same shi? Kaddararta ta fara wuce iya ni kawai har ta fara taba yayana da mutanen da suke kusa da ni? Tambayar da na yi ma kaina kenan tambayar da ban san wanda zai amsa min ita ba. Guri na samu kusa da gate din na zauna a saman wani guntun dakali idona cike da kwalla, ban samu kaina a cikin tausayin wani mutum wanda ba jinina kamar yadda tausayin Kabir ya dirar min a zuciya yai min kawaya a ruhi, ya nemi jijiyoyin jinina da jiki ya rike.

“Halimatu”

Muryar Abdallah ce ta hankalto ni har na dago kaina na kalleshi hawaye na min zuba.

“Zama kikai a guri kamar wannan har kina kuka a public? Mutane fa suna ta kallonki”

Cikin wani irin sanyin muryar da natsuwa yai min maganar da sautin da ni kadai zan iya ji da kuma fahimtar kalmomin da yake furta min. Sauke kaina nai daga kallonsa zuwa kallon titi ina ta yawo da ido.

“Abdallah ina tunanin Gobena ne, ya zata kasance? Miyasa abubuwan nan za su faru ta dalilina? Na farko yata? Na biyu kuma abokin aikina? Abunda ya faru da Namra kamar jiya ne, ban sammaci wani abun da zai taba zuciyata kamar haka zai sake faruwa ba, idan wani abun nai nauyi ya sake faruwa da ni ina jin kamar ba zan iya jure ba”

Risinowa yai gabana yana kallon fuskata.

“Share hawayenki zo muje a mota ki min bayani maybe zan sama miki mafita”

Sai na sake dago kai na kalleshi a karo na biyu, a yau Abdallah yai magana ta hankali da nuna kulawarsa a kaina, ko da yake a can baya ma ai yana nunawa sai dai wacan karon ina ganin rashin dacewar hakan saboda akwai igiyar aure a kaina, kuma a baya duk wata magana da zai min ta Aminu ce da abunda ya shafe shi.

“Abdallah zan iya rikon ka kamar dan'uwan? Abokin shawara? Wanda zan labartawa damuwata ya nema min mafita? Dan Allah?”

Sai ya kasa ce min komai, ba dan komai ba dan sai dan ya san inda manufata ta dosa, daga lokacin da zai rike ni a matsayin yar'uwa to babu zancen soyayya ko aure a tsakaninmu, ni kuwa abunda na fi so kenan, domin ban tana yi ma Abdallah kallon so ko kauna ba balle har ta ga kai ga aure! Mikewa yai tsaye ya nufi inda motarsa take, sai a lokacin na lura da inda ya faka ta, tashi nai na bi bayansa ba tare da na share hawayena ba. Na bude front seat ma shiga shi kuma ya tashi motar ya koma da ni cikin asibitin, a daya daga cikin guraren da aka tanada domin likitoci su faka motocinsu ya faka motarsa sannan ya juyo ya kalleni.

“Idan har hakan zai faranta miki rai Halima zan yi, amman ki sani zan cutu domin ba abunda nake so kenan ba, sai dai zan jira har lokacin da zaki fahimci da gaske na ke, fada min minene damuwarki?”

“Abokin aikina yayi hadari saboda ni, kuma yanzu na ji cewar akwai yiyuwar jimin ya tana kansa wata kila ya haukace ko ya manta komai ko ya mutu”

Na fada kai tsaye ina share hawayena. Sosai ya nuna min damuwarsa.

“Subhanallahi miya same shi haka?”

A take na labarta masa komai har zuwa fadan da mukai da matarsa. Na yi zaton ko zai tausaya masa ne sai na ga murmushi a fuskarsa.

“Kin kasa yarda cewar kina da kyau da kan iya jan hankali wasu mazan izuwa gareki saboda Aminu yana yawan fada miki cewar baki da kyau ko? Kina da kyau Halima seriously kina da jikin da ko wane namiji zai so ki kasance a tare da shi, ina tunanin abunda ya ja hankali abokin aikinki kenan har ya kai ga mallakar hotunanki da sakawa sunanki spacial saboda ke din ta musamman ce”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now