61

2.9K 344 197
                                    

Ta waya nake labartawa Hajara abubuwan da suka faru, ba laifi ita kam yaba min tai akan abunda nai wa Abdallah.

“Daman can ni dai hankalina be kwanta da wannan mutumen ba, kuma taya zaki auri yaya ki auri kane dukansu suna raye, yanzu wannan abun da kika yi har Mahaifiyarsa ta kara shiga tsakani ai dole ya kyale ki ki samu kwanciyar hankali, ko ba komai kuma ta ji abunda Abdallah yai ma dan'uwansa ko dan haka ai dole ta daina kin ki”

Na tabe baki kamar tana gabana na ce.

“Haka dai kike gani, amman a iya tunanina abu ne mai wahala Hajiya ta iya so na, kiyayya ta riga ta shiga”

“To can ta matse musu mu ai ba mu da case da su a yanzu, za mu je mu ci amarcin ma a waje ma ba a kasar nan ba”

Ta fada tana keto wata shegiyar dariyar jindadi.

“Wani irin amarci kuma Hajara? Jinya dai ko?”

“Ke kar ki maida ni yar iska mana, idan kun je jinyar sai ya saka miki ido yana hadiyar yawu? Mazan yanzu? Ko kana gidanku ma ya ka kare balle ana tare? Make sure dai kim gyara kamin ku tafi”

“Jinya fa zamu je hajara, kuma gobe zamu wuce ina wani zancen gyara”

“Ko yanzu dai lokaci be kure ba, ai ba dole sai kin yi wani shegen shaye-shaye nan ba, bari Abban Afrah ya dawo idan ya amince min zan je gurin Hajiya Bilki na karbo miki wani set da take badawa na amare, sha daya ake amman aikin shekara yake, kuma idan kika sha baki bukatar kara shan komai da sunan gyara, kuma ba wani da yawa bane ba sai kin wahala ba, amman fa ki shiryawa aiki dan ni kaina wallahi sai da na ci kwakwa balle kuma ke da kika kwana biyu ba a hadu ba”

Daga ni har ita dariya muka saka, daman can Hajara ta san irin wadannan abubuwan shiyasa kullum gidanta baya rabo da su har mamaki take a lokacin da ina auren Aminu amman bana sha kamar ita.

“Amman fa gaskiya kusan 32k take bada shi, kuma kudin da ke hannuna ba zai wuce 14k ba idan ma yayi, kin ga bikin nan naki ma ya fado min gaf amman dai kamin a tare na san na shirya In-Sha-Allah kuma na san ba zata yarda ta bada shi a akan bashi ba domim bata da yarda sam duk sabonka da ita”

“Karki damu turo min account dinki zan miki transfer yanzu”

“Shegiya amarya ki ce har kin ji dala? Ehhen”

Dariya nai na watsa da carbin da ke hannuna.

“Ba na shi ba ne, wannan kudin ya dade ban baki komai ma a ciki ba kin ga sai na hada na turo miki”

“A a lalai ba ni da case matar Amadu ki ce abun akas yake... ”

Sai da tai ta wasa da zolayarta ta da saba sannan mukai sallama ta turo min account din na tura mata kudin da kuma dan ihisanin da nai iyar yi mata. Sannan na aje wayar na janyo akwatina ina hada kayan da nake son zuwa da su, sai da na gama sannan na tashi na shiga na yi wanka na saka atamfa na shafa yar hoda kadan na saka hijabi na nufo dakin Mama.
  Fada na samu tana yi ma Aisha sai na samu guri na zauna har ta gama sannan na ce.

“Mama zan koma asibitin”

“To jikin na shi dai da sauki ko?”

“Gaskiya da sauki sosai, domin ya daina jin zugin tun jiya, yanzu nauyi ne kawai yake masa, tafiyar ma dan mahaifiyarsa ta ki yarda ne shiyasa da an fasa”

“Ai kara a aje din ko ba komai hankalinta zai kwanta, za ta fi samun natsuwa, Allah ya kara masa lafiya”

“Amin Mama kin kara yarda aikin Abdallah ne ko?”

“To akanki Halima waya isa ya taba dan gidan Hajiya?”

Da karashe da murmushi ni kuma nai dariya ina mikewa tsaye, sai da nai mata sallama na shiga nai ma Inna sannan na fita, direban da ya dawo da ni dazun dan nai wanka ne na samu a waje.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now