55

2.2K 313 168
                                    

Idan na ce zan iya fadar kulawar da na samu a gurin Ahmad da mahaifiyarsa na yi karya, domin a kwanan da nai asibiti kullum sai na yi bachi yake tafiya gida, mahaifinyarsa kuma sai tavaiko mana da abinci safe, rana da na dare, sau uku tana zuwa duba ni asibiti, a duk lokacin da ta zo tana yi min kalaman da suke kara min kimarta a idona kuma su kara kwantar min da hankali. Tana yawan fada min cewar nai hakuri, kuma na cigaba da yarda da kaddara kamar yadda nake, kar nai tsammanin Allah ba zai sake jarabata ba, kuma kar na tsammaci sake samun wata kadarar a gaba, na kyautata zaton kuma nai ta addu'ar, haka zata zauna tai ta fira da Mama ko Inna kamar ba matar babban mutum ba ko kuma na ce uwar babban mutum, da aka salleme mu a asibitin ma sai da ta kira ta ji muryata.
Yau kam na kara yarda da maganar mutane da suke cewa duk abunda ya baka tsoro wata rana zai baka tausayi, duk kuma abunda ya baka tausayi wata rana zai baka mamaki.
Idan nai na hada kalubalen rayuwar da na fuskanta da na Aminu da Abdulhamid, sai na gane cewar ni din ban ga komai ba, domin a halin yanzu Allah ya min mafita kuma ya wanke ni, wani kalubalen a farkon rayuwa yake wani a karshe, wani a tsakiyar rayuwarsa, ba duka arziki ne na halal ba, na kuma ko wane arziki ne na haram ba, ba duka talauci ne kunci ba, ba kuma duka kunci ne takauci ba, saboda ina cikin takauci ba shi yake nufin ba zan jidadi rayuwa ba, idan kuma ina da arziki baya nufin aki jarabbatata.
Ta wani bangaren na kanyi mamakin abunda ya kai Abdulhamid aikata wannan mummunan abu, ko da yake ko wane bawa be isa ya wuce kaddararsa ba. Kamar yadda ban wuce komai ba sai da ya same ni. Ba ni kadai nake cika da mamaki ba har da Mama da Inna, da duk wani wanda ya san waye Abdulhamid, mutumen da magana ma bata sha masa kai ba, dole kowa yayi mamakin wannan abun, wata kila Abraham ne yaja zuwa ga mummunar rayuwa, wata kila kuma shi yaja Abraham din, gaskiyar abun yana a tsakaninsu sai kuma bincike idan ya tabbatar.

Dago kaina nai daga kallon wayar Hafiza da nake wacce ke dauke da hotunan su Abdulhamid, da Abraham da wani wanda ban wayance shi ba, an saka musu handcuffs, police na tsaye a bayansu an jarida kuma nata aikinsu. Na mika mata wayar ina fadin.

"Abdulhamid ya ban tausayi"

"Tausayi? Tausayi fa kika ce Halima? Haba mutumen daya sakeki har wani tausayinsa zaki ji, ke dai Wallahi kina da matsala"

Na yi shiru domin na san ba zata taba fahimta ba, sai dai abunda ya fi tsaya min a rai shine shin Abdulhamid ya san cewar Abraham ne yai min fyade? Da saninsa akai? I need to know, na fada ina sauke ajiyar zuciya a hankali. Na unkura zan tashi kenan sai ga su Namra sun shigo da gudu kowanensu rike da leda a ko wane hannu, ledan kuma ba karama ba irin babbar ledar nan ta super market.

"Momy Guess what...?"

Aiman ya fada yana wani irin murmushin jindadi.

"What it's?"

Na tambaya da mamaki a fuskarta.

"Wannan Boss din naki, baban su Baby Namra ne ya dauke mu daga school ya je da mu wani katon shago yace mu dauka duk abunda muke so"

Wannan karon Adnan ne yake magana, sai Namra ya kyalkyale da dariya.

"He say we should called him Daddy, wai yana jiranki a waje yana can cikin mota"

Kana kallonsu kasan suna cikin farinciki, jin cewar yana waje yasa na dauki Hijabina na saka na leka kofar gidan, sai ko na ganshi daf fa kofar ya faka motarsa. Ganina yasa ya sauke gilashin motar yana miko min murmushi.

"Lims how far"

Dan murmushi nai nima

"Mun gode Allah ya saka da alheri, kana ta dawainiya da yara"

"Bude back seat din nan akwai na ki"

Ya fada yana dauke fuskarsa kamar baya son nai masa godiyar. Na yi kamar yadda ya umarta na bude gidan baya na dauko katuwar leda na fito da ita.

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now