GN-09

1.8K 231 20
                                    

“Wannan kaddararen aure yau Allah ya kawo karshensa, ni ban ga abun kuka ba ma balle wata damuwa”

Shine abunda ya fito daga bakin Abdallah, Mama kam kasa cewa komai tai har lokacin tana dafe da kanta nima na kasa daina hawaye zuciyata tana min wani mugun zafi.

“Ummi rikata ki shiga da ita daki mana”

Cewar Abdallah yana kallona kamar ya taso da kansa din ya rikani. Salma ta taso ta zo ta rika daga tsayen da nake muka nufin dakin Mama tana rike da ni kamar yadda Abdallah ya bukata, muna shiga dakin na zauna bakin gado sai ta zauna kusa da ni tana kallona idonta taf da hawaye.

“Ki yi hakuri Anty Halima haka Allah ya so, ki dauka wannan ma yana rubuce a cikin abunda Allah ya rubuto zai same ki”

Na gyada mata kai ina ta kokarin taushe kukan da ke cina, Amal ce ta shigo ta zauna saman kafafuwana ya lafe kamar zatai kuka sai kace wacce ta san abunda ke faruwa. Salma kuma ta tashi ta fita ta barni a dakin daga ni sai Amal a nan na samu damar yin kukana iya yadda raina yake son, ina cikin kukan Mama ta shigo ta zauna bakin gado na yi zaton zata fara tambayar abunda ya faru ne ko kum ta tausaya min ko ta karfafa min kuiwa akan abunda ya faru, amman sai na ji wani abu dabam na fitowa daga bakin.

“Ai ga irin ta nan kin kashe aure tun ba a aje ko'ina ba kin fara kuka, ina amfanin wannan abun? Kin saka kanki da yayanki a cikin matsala bayan kuma kin san saki daya ya rage ba wani gyara a tsakaninku? Halima rayuwa zatai yi? Yanzu duk maganar da muka miki muka ce ki rufe abun nan sai da kika tona shi?”

Daga kaina nai na kalleta, ban san abunda take hango min ba na kokarin hanani yin komai akan abunda akaiwa Namra, na san tana gudun zaman gida a gurina kuma tana jin kwatankwacin zafin da nake ji na baro yayana a wani gidan, amman har yanzu na kasa gane dalilin na son boye maganar, indai na janyo ma yayana tsanena ina ganin kamar ba hujja ba ce.

“Ko wace Uwa Mama tana goyon bayan abunda yayanta suke aikatawa ko da kuwa abun nan marar kyau ne, na kasa ganin kuskure abunda nake son aikatawa, na san kina min tunanin mutuwar aurena ne, amman tabbas aurena mutu ko da ta wannan dalilin ba, duk yadda kike jin zafi idan wani abun ya same ni haka nake jin zafi idan ya samu Namra, saboda nima uwa ce, kin taba fada mana cewar saboda mu kika zauna da Abbah a cikin lalurar da yake ciki ta rashin lafiya, mama ya dan Allah ki fahimta nima saboda Namra ne, kuma ba dan bana son aurena ba sai dan ganin kamar mutuwar auren a yanzu zata fi sauki sama da idan yayana suka girma, Mama Aminu ya sake ni akan be yarda da abunda na fada ba, ba wai ma ya roki na boye sirrin ba ko kuma ya roki kar na kai kotu ba, mahaifiyarsa har ikirarin cewa tai sai an kaiwa Sadi Namra ya rikata sai dai na mutu, Mama ina kuke son na saka kaina na ji sanyi? Me kuka son nai a duniyar nan?”

Wannan karon hawayene yake zuba a idon Mahaifiyata, na sani kalamaina sun ratsata matuka kuma ta fahimci inda na dosa.

“Kwatarwa yarki hakki abu ne mai kyau Halimatu, amman kwatar hakki a inda kwatar yafi rashin kwatar alheri to barin shi ya fi, idan kika kai maganar nan kotu kin sani Sadi da yan'uwansa ba yarda za su yi ba, kuma za su yi komai dan su wanke shi ciki har da mijinki tunda kin ce be yarda da abun ba, daga haka maganar zata tashi sama kanki ankaro an fara buga ku a jaridu ana fira da ku, kamin a kwato miki hakkin ki sai kin sha wahala, idab kikai nasa a hukunta na shekara daya ko watanin kadan me akai kenan? Idan kuma ba ki yi sa'a ba sai a kori kararku  bayan na gama fadar kin batawa yarinya suna, irin wannan abun Halimatu rufewa ake saboda rayuwar yar ki a nan gaba wa zata aura? Wa zai aureta? Mi zata je ta tarar? Ina hango miki abunda zai zame miki matsala ne nan da wadansu shekaru masu zuwa wanda ke ba zaki gani ba a yanzu, zaki batawa yarki sunane kawai a cikin kawayenta yan'uwanta da kuma wandanda zata hadu da su nan gaba, ke da Hafiza da Doc Abdallah kun kasa fahimtar abunda nake nufi ne kawai wata kila sai nan gaba, shi ma abunda ya zo yana min magana akai kenan? Wa be kamata a kyale wannan maganar ba, ni kuma na fada masa indai da yawuna za aje kotu da wannan maganar a matsayina na mahaifiyarki ban yarda ba!”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now