51

2K 293 80
                                    


Ina godiya sosai Maman Sayyed,  sakonki ya riske ni, Allah ya bar kauna kuma ya ba ni ikon yi kullum 🥰

        Gaisuwa ga duk makarantan labarin Gobena a duk inda suke Allah bar kauna 🥰🌸❤️

***     ***    ***     ***    ***   ***

Wani lokacin Allah yana mana talala mu yi ta aikata zunubi har sai idan ya tashi kama mu sannan yai mana damkar da zata saka mana nadama da dana sani, a duniya kenan da Aminu ya fara haduwa da sakamakonsa, to ina kuma a lahira? Sai dai ina kyautata masa zato kasancewarsa musulmi kuma ya gane kuskurensa ya tuba, Allah yana son bayinsa masu tuba.
   Na shiga gida da tunanin Aminu a raina, ba ma ni ba a halin yanzu Aminu be isa ya tunkari wata mace yace yana sonta ba, sai idan mai dauke da irin lalurarsa ce ko kuma idan boyewa zai yi, wata kila ma yayan da yake aibantawa yana cewa na haifa masa yara da yawa zam tsofar da shi sune kadai yaran da Allah zai ba shi. A ranar na kudirta a raina cewar ba zan fada musu cewar mahaifinsu yana dauke da cuta ba, fada musu ba zai haifar musu da komai ba sai tashin hankali duk kuwa da kasancewar akwai kurciya a tare da su, ba lallai ne su fahimci komai ba.
  Har ga Allah na jidadin da cutar ta kama Sadi da Sa'adatu ko ba komai dukansu sun ci amanar aure kuma sun ci amanata, Sa'adatu kawata ce ta zabi tai mu'amala da mijina bayan kuma ita ma din tana da aure da yara, sadi kuma ya ci amanar dan'uwansa yai ma yar dan'uwansa fyade, ko da yake har da sakacina a wasan lokaci na barinsu da nake suna kebewa a tare yawan shige masa da take ban taba hanawa ba, saboda ban kawowa zuciyata komai a kansa ba, ko da yana zina ban tana ayyanawa a raina cewar zai iya lalata yar dan'uwansa ba, ashe duniyar ta dade da canjawa daga sanin da nai mata, a yanzu babu yarda a tsakanin yaranka da kowa, domin bayan Namra na yi ta ganin labarai masu sosa zuciya wasu uncles dinsu zasu lalata su wasu kuma ubansu na ciki ko makota, kai har malaman makarantar boko da islamiya ba a bari ba, hakan yasa na kara saka ido akan duk wani motsi na yayana ba mata kadai ba har mazan domin suma ba a yanzu ana lalata su, mun kai wani zamani da babu aminci a zukatan mutane kowa kokarin cutar da kai yake.
A washe garin ranar sai na tashi kamar wata marar lafiya, ba labarin Aminu kadai daya saka jikina sanyi ba har da tunanin Ahmad abunda ban tana ba, ko da dai rana ban tana kwantawa ko tashi da tunaninsa ba. Sai dai jiya na raba dare da tunanin abunda yai min da wasu alamomi da sai a yanzu nake fahimtar inda ya dosa.

“Hello Lims fatar kin tashi lafiya Happy birthday”

Shine farkon abunda ya fara shigo min a waya, kamin na bank dina su turo min. Ni kan har na manta da wani zancen birthday sai yanzu.
  Aje wayar nai na fito tsakar gida na debi ruwa na shiga daki na juna a electric kettle, haka na bi yarana na zuba musu ruwa sukai wanka sannan suka karya suka saka uniform. Zuwa nai na gabansu na risina ina kallonsu wani irin farincikin marar misaltuwa ya lullube ni lallai yara rahama ne, no matter how suke rashin ji ko suke cutar da junansu.

“Allah yai muku albarka ya shirya ku da duk yaran musulmi, ya tsare ku.”

Duka suka amsa da amin, daya bayan daya na busu da addu'a ina dafa kansu ina karantawa har na gama sannan school bus dinsu ta iso, da gudu suka fita daga gidan kowa yana kokarin ya riga dan uwansa gwanin sha'awa. Da kallon kauna na bisu zuciyata cike da shauki ina murmushin jindadi da yi ma Allah hamdalla. Ina juyawa sai ga Namra ta dawo tare da Adnan suna rike da wani katon kwali wanda daker ma suke iya daukarsa, an nade kwalin da fata jar leda mai kyale.

“Momy Momy gashi inji direban Bus yace wai a baki”

Jin hakan yasa nai saurin tashi na karasa na karbi kwalin.

“To Momy bude ki sam mana abunda ke ciki”

Namra ta fada jikinta har rawa yake.

“Kin san abunda ke ciki?”

GOBE NA (My Future)Where stories live. Discover now