Twelve

1.7K 143 7
                                    

Jin wani irin nishad'i yake, da farin ciki da ya mamaye mishi zuciyar shi, wanni in ya ganshi zaiyi zatan farin cikin da yake bai wuce na zama ango ba amma shi yasan sam sam ba haka abun yake ba, dad'in da yake ji ba na komi ba illa na ya cimma burin sa, ya kuma sami abunda yake so, ko sati biyu da suka wuce da abba ya same shi na cewar sunusi zubair ya shawarce shi da dan Allah su d'aga bikin sai nan da sati biyu abun ba k'aramar d'aga mishi hankali yayi ba, a tunanin shi a lokacin ko kawun yarinyar ya gano me yake k'ulla wa, ya shiga tsan tsan tashin hankali sai da ya zauna sosai yayi tunani da ba wanda ya gaya wa abunda ke cikin zuciyar shi kuma bai nuna hakan ba shima a fuskar shi sannan ya sami sauki.

Bayan sun dawo daga d'aurin auren da ya gudana a ranar bayan sallar juma'a, suna zaz zaune a makeken parlor d'in abba da manya manya abokan shi kuma mayan y'an siyasa, abinci burjik a gaban su, Kamal da imran suma na gefe dan shi imran ne kad'ai abokin shi, shi dai yayi shiru a wurin yana kawai wasa da teaspoon d'in da ke cikin mug d'in hanunshi me d'auke da tea, jin muryar sunusi zubair yayi da ya saka shi saurin d'ago idanun shi da maida su kanshi,

"Tunda an riga da an d'aura aure, gobe kawai kaje ka d'auki matar ka, kuyi kano, dan barin ta a gida bashi da wani amfanin a wurina"

Tun kan ya k'arasa zancen ya k'ara jin wani mugun dad'i ya kama shi, maida idanunshi kan abba yayi wanda yake faman d'aga kai dan yaji me zai ce,

"Gaskiya kam, tunda gidan da zasu zauna already ya gama had'uwa, zaman ta a gidan bashi da amfani"

Kamal bai san lokacin da ya saki murmushi ba tsabar farin ciki, har sai da imran ya ganshi ya zungurar mishi k'afad'a sannan yayi dariya tare da girgiza kai, abunda ya k'ara ji daga bakin abba ne ya d'an saka jikin shi yin sanyi,

"Amma ni dai a gani na, tunda ko wace yarinya mace aka tashi kaita gidan miji ana had'a ta da y'an uwa da abokan arziki sugano d'aki, why not itama a had'a ta da maman su kamal da kuma matar ka, ko su biyu ne suje su gano d'akin nata, na tabbata haka zaiyi mata mutuk'ar dad'i"

Ina kuma abba ke zuwa, dan Allah kawai a kyalle shi yaje ya d'auke ta su tafi, shi baiga me su mami zasu je suyi ba,

"Haka ma yayi, sai goben su tafi tun flight d'in safe, yarda zasu samu su dawo a goben"

Maganar da sunusi zubair yayi ce ta d'an sami shi sanyi a ranshi, da sauki dai tunda ba kwana zasuyi ba, haka suka saka wata hirar har sai da la'asar ta gabato, sannan kowa ya mik'e dan yin haramar sallah.

---------

Tunda take a rayuwar ta bata tab'a zatan mutum zai iya kwana a zaune yana raira kukan da ba sausaci sai akan ta, ita da mommy jiya kwana sukayi a zaune tsabar tashin hankali, ba irin rarrashin da mommy batayi mata ba amma ta kasa daina kuka, wani irin rad'adi da ciwo zuciyar ta ke mata, wani irin jin zafin muguntar da daddy yayi mata take ji a duk sashi na jikinta, jiya tasan daddy bai d'auke ta a matsayin y'arshi ba, ji ya tasan ita ba kowan kowan daddy bace soboda yarda ya nuna mata k'arara a matsyin y'ar ruk'o ya d'auke ta, wani sabon kuka ne ya sake k'uboce mata, ina ma iyayen ta nada rai, ina ma suna doran k'asa da tasan baza ta tab'a shiga cikin irin wannan bak'in cikin ba, sau uku tana fakar idanun mommy tayi hanyar gate dan ta gudu ta bar gidan amma daddy ya baza sojoji a haraba da wajan gidan yadda baza ta tab'a iya guduwa ba, ita kuwa ta shiga uku, ina zata saka ranta taji dad'i.

Ko da aka turo k'ofar dak'in aka shigo bata d'aga idanunta taga wane ba, amma jikin ta ya gaya mata mommy ce, sai da ta isa wurin ta, sannan ta d'ago da kanta wanda yake mak'ale akan cinyar ta,

"Haba sakeena, kukan ya isa haka, in kika cigaba da wannan kukan da ba sausaci za kiyi cuta ne, ba nace miki ba ki dunk'a addu'a ko kuma ki d'auki qur'ani ki karanta, shine zaki samu nustuwa"

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now