Six

1.8K 189 3
                                    

Sakeena na ajiye faiza da faheema a hotel d'insu tayi hanyar gida bayan sunyi sallama sosai, tana isa tayi parking ta fito, ta fara takawa zata shiga cikin gidan tayi kicibis da daddy, yana zaune a compound d'in da newspaper a hannunshi alamun karantawa yake, ji tayi gabanta ya fad'i dan bata gaya mishi zata fita ba mommy ta gaya ma, ta sauri tayi ta k'arasa inda yake ta tsgunna har k'asa ta fara mishi barka da rana, jin muryar tan da yayi ne ya dakatar dashi daga karatun jaridar da yake, gyara reading glasses dinshi yayi sannan ya mai da idanunshi kan Sakeena wace ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, tambaya ya shiga yi mata daga ina take, gabanta ne ya k'ara mummunar fad'uwa ta tabbata in har yasan daga wurin su faiza take sai ranta yayi mugun b'aci, tunda kanta na k'asa bazai gane bata da gaskiya ba ta shirya mishi k'arya cewa wani aiki taje ta k'arasa a office director d'in yace lallai da gama kan gobe wato ran littinin, ta ko ci sa'a ya yarda, maida duban shi yayi kan jarida tare da mata nuni ta tashi ta shiga ciki, Sakeena hamdallah tayi sannan ta mik'e tayi cikin gidan.

D'akin mommy ta fara yi wato matar kawun ta dan ta sanar mata ta dawo, tana bud'ewa ta ganshi wayam alamun bata nan, yin hanyar kitchen ta shiga ta baya wurin masu aiki, taga blessing me aikin su a kwance, tambayar ta tayi inda mommy take, me aikin sanar da ita tayi bata dad'e da fita, Sakeena girgiza kanta tayi, mommy kwata kwata bata gajiya da yawo, kullum tana cikin fita, ficewa tayi tai hanyar d'akin ta, tana shiga ta fara rage kayan jikinta tayi closet d'inta ta d'auko wata riga mara nauyi iya gwiwarta ta saka, sannan ta fad'a kan gado bayan ta lalumu wayar ta da take cikin handbag d'inta.

Fuskar wannan mutumin da ta gani a cilantro ta shiga tunawa, ita dai bata tab'a ganin irin kama haka ba a rayuwar ta, gaskiya tasan duk yadda akai mutumin ya had'a jini da Kamil dan kamar tayi yawa, ajiyar zuciya tayi sannan ta d'aga wayar ta me k'irar iphone 11 pro max dadai fuskarta, wayar na bud'ewa ta kai kan number d'in hamida da danna sannan ta saka a kunnan ta, wayar bata dade da fara ringing ba aka d'auka, nan suka fara gaisawa ita da babbar aminyar tata, sai da suka d'an yi hira sosai sannan Sakeena ta fara cewa a hankali,

"Naga mai kama da Kamil yau"

Shiru akayi daga d'ayan b'angaran tasan k'awartata mamakin ta take yi da ta ambaci sunanshi, ita kanta tayi mamakin kanta, amma gani tayi in har bata gaya ma wani ba baza ta tab'a samun sukuni ba, hamida tayi kamar baza ta amsa ba, can kuma tace,

"Ban gane kinga mai kama da Kamil ba?"

Sakeena k'ara wani ajiyar numfashin tayi, ta ina ma zata fara yima k'awartata bayanin abunda ya faru da ita yau, jin muryar hamida ta k'arayi

"Ki amsa ni kinyi min shiru"

Lumshe idanunta tayi, ta dad'e a haka sannan kuma ta fara bama babbar k'awartata labari, tunda ta fara hamida bata katse ta ba, sai da ta tabbata ta gama zancen ta tsaf,

"Wannan wace irin kama ce haka har kikyi zatan shine Kamil bayan kinsan..."

Hamida saurin dakatar ta kanta tayi, tasan ta k'arasa zancen Sakeena zata iya rikice mata yanzun nan, shiru suka k'arayi, hamida ita ta k'ara bud'e baki ta fara magana,

"Ko dai wani d'an uwanshi ne, bai tab'a gaya miki yana da wa ko k'ani ba?

Girgiza kanta tayi kamar k'awartata na kusa ta ita sai kuma daga baya tayi saurin ce mata a'a,

"Duk rayuwata dashi ban san kowa nashi ba, ya dai cemun bashi da kowa scholarship ne ma ya kawu shi karatu garin"

A hankali tayi maganar kuma daga karshen zancen ta kana ji yarda muryar tayi rawa, k'walla ce ta cika idanunta, shi yasa ko kad'an bata son tuna shi dan ranar zata nemi sukuni ta rasa shi, sa hannu tayi ta fara goge hawayen da suka zubo fuskar ta,

"Bazan gaji da gaya miki kin yi babban kuskure, taya za ace baki san komi akan shi ba amma har kika yarda kika afka cikin soyyar shi"

Yanzu Sakeena kuka take wiwi, ta gaji da gaya mata gaskiyar da hamida take, itama tasan tayi kuskure, amma ya zatayi, lokacin so ya rufe mata idanunta da kunnanta bata ji bata gani, sosai take kuka tana jin hamida tayi ajiyar zuciya,

"Ni ba kuka nace kiyi ba, Dan Allah kiyi shiru" haka hamida ta ci gaba da rarrashin ta har ta samu ta rage kukan, sai da ta tabbata nustsuwa tazo ma sakeena,

"Kinsan surname d'in Kamil?"

cema tayi a'a, hamida shiru tayi, sai can tace da tasan surname d'inshi da ta saka Saleem wato mijinta yayi musu background check akan shi, da yake babban soja ne, su gano ko yana da y'an uwa ko ma shi y'an biyu ne tunda tace suka kama sosai, Sakeena dariya tayi da taji abunda k'awartata tace,

"Abun yayi zafi haka harda su background check?"

Hamida ma dariya ta saki, nan sukayi ta wasa da dariya suka ajiye zancen Kamil da mai kama dashi a gefe, sunyi hira sosai sannan sukayi sallama, Sakeena na kashe wayar ta tashi ta d'auko hijab tayi hanyar kitchen dan ta d'ora lunch tunda daddy na gida, baya cin abinci masu aiki sai da ita ko mommy su girka, a lokacin jinta take sakayau kamar bata da wata damuwa, shi yasa take bala'in san hamida, ta iya kwantar mata da hankali, a haka har ta shiga kitchen had'e da fara haramar d'ora abinci.

Bayan ta gama girki ta saka a flask ta jera ma daddy akan dinning sannan tayi hanyar d'akin ta, bathroom d'inta tayi direct dan ta watsa ruwa tayi haramar salla, bata jima ba a ban d'akin ta fito d'aure da towel a jikinta ta, bayan ta zauna a gaban dressing mirrior d'inta tayi shafe shafen ta da ta saba tayi hanyar closet d'inta da dauko wata doguwar riga ta material tare da dauko saban hijab komawa cikin d'akin ta tayi ta saka doguwar rigar had'e da hijab da d'auko abun salla ta fara harama, sai da ta idar tsab tayi aduoin ta data saba sannan ta mik'e komawa kan gado tayi sannan ta jawo bedside drawer d'inta ta d'auko book, ta bud'e zata fara krantawa kenan wani tunani yazo mata,

Sau da yawa in har suna fad'a da shaheeda (y'ar kawun ta) tana yawan gaya mata tana soyyya amma bama tasan wanene saurayin ta ba, tasan shaheeda tasan wane kamil, tasan asalin shi ta kuma san komi game dashi saboda shaheeda akwai san jin kwakwaf amma pride d'inta bai tab'a sawa ta tambaye ta ba, wai ma me ya saka Kamil ya b'oye mata komi tattare dashi, bayan ita ta fayyace moshi komi da ya shafeta, ba abunda ta sani game dashi in har ba sunan shi ba, da suna makaranta bata tab'a ganin shi da wani aboki ba, ko yana dashi bai tab'a kawo mata shi sun gaisa ba, dab da abun zai faru dashi suka fara samun sab'ani yawanci kullum suna cikin fad'a saboda har ga Allah boye mata asalin shi da yake yana yi mata ciwo, ko da ya dawo nigeria sunyi wani fad'a kaca kaca har sukayi sati basa ma juna magana, sai daga baya yazo ya bata hakuri tare da mata alkwarin in har ya dawo turkey ko in har ta dawo nigeria sai gaya mata komi game dashi bazai bar komi ba, amma Allah bai yarda ba, kwalla taji ta cika mata ido tayi saurin kulle idanunta, sai da taga kwallar ta koma sannan ta d'auko wayarta da take gefan ta ta kai kan number d'in shaheeda, dukda basu tab'a shiri ba a rayuwar su yau tana san jin asalin Kamil kuma ta lura ita kad'ai ce zata iya gaya mata, danna kan sunanata tayi tare da saka wayar ta a kunnenta.

(Waya tace ta samu problem shi ya saka banyi updating da wuri ba...

Anyways dont forget to vote and share)

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now