Forty four

1.7K 191 55
                                    

Yana zaune akan makeken gadon d'akin shi, hannunshi a d'ore akan kanshi, yayin da idanunshi suka zamana a lumshe, kanshi ne ke sara mishi kamar zai rabe gida biyu, bayan jin wani irin azazaban sanyi da ya lulub'e shi, amma duk basu ne ke a gaban shi ba, shi kadai yasan me yake ji a yanzu, shi kadai yasan irin tashin hankalin da yake ciki.

Abba fushi yake dashi ya mak'i sauraron shi, be ma bashi fuskar da zai mishi maganar sakeena ba, shine sanadiyar saka kamal shiga cikin tsan tsan damuwa fiye da jiya, in har da gaske abba ya raba shi da ita ya tabbata shine abunda zaiyi sillar ajalinsa, dan baya hango rayuwa ba ita.

Hawaye ne ya fara d'iga a fuskar shi, tsabar ciwon da yake ji a tattare dashi, ko ina a jikinshi ciwo yake mishi, ga ba inda zai kai kanshi ya ji dad'i, ko ganinta da yayi yanzun nan kwata kwata bai kwantar mishi da hankali ba, sai ma k'ara jin wani sabon rad'ad'i yake ji a cikin zuciyar shi da ko wane sase na jikinshi in ya tuna zata iya kasan cewa ba matar shi ba.

Hawaye ne suka cigaba da kwarara, kamal kuwa bashi da shirin share su, kyale su yayi suyi ta zuba wai ko ya sami sauki a ranshi, yana wannan yaji an turo k'ofa tare da sallama, muryar mami sarai yaji amma bashi da k'arfin d'ago kanshi koma bud'e bakin ya amsa sallamar ta, yana ji ta iso inda yake ta tsaya a gaban shi.

Tafi mintoci a tsaye bata ce mishi komi ba, kamal ma yayi shiru a wurin har lokacin bai motsa ba, da yaga mami bata da shirin kulashi ya saka shi d'agowa da kanshi a hankali, dukda yana jin tsoron ganin abunda ya gani d'azu a idanunta, baya san fushin mami, amma ba yarda zaiyi dan gaba d'aya ya bat'a ma iyayen nashi rai kuma fushi dashi shi kad'ai ne yarda zasu hukunta shi.

Suna had'a ido a take yayi dana sanin d'agowa, kallon da tayi mishi d'azu shine dai a fuskar ta, wata kwallar ce ta sake zuba, garin yaya yakai kanshi zuwa ga halaka haka, me ya saka son zuciyar shi ya saka ya aikata abunda ko wane me sunshi yake wadai dashi a yanzu, iyayen shi ba abunda suka fi so a rayuwar su irin farin cikin shi, kullum burin su su dad'ad'a mishi, amma da abunda ya saka musu kenan.

"Kamal me ya saka?, me ya saka zaka d'auki wannan d'anyan hukunci?, me baiwar Allah nan ta tab'a yi maka"

A sanyeye cikin sanyin muryar mami duk ta jero mishi tambayoyi, wata kwallar ce ta sake zuba yayin da ya maida idanunshi k'asa dan bazai iya jure kallan fuskar mami ba, be san me zai ce mata ba dan a yanzu bashi da wani kwakwaran dalili.

"Gidan karuwai fa kamal, baka barta haka ba sai da kasa aka aikata abu mafi muni akanta, ka saka aka mata fyad'e, fyad'e fa, kayi mata tabon da har duniya ta nad'e ba wanda zai iya wanke mata shi, yau da kausar ko kamila aka kwatanta yi ma haka na tabbata sai inda k'arfin ka ya k'are amma wai kai da kanka ka aikata haka"

Lumshe idanunshi yayi, dan maganganun mami ba k'aramin k'ara girgiza shi suke ba, suna jefa shi cikin wani irin tashin hankali da rud'ani, ya kasa ma bud'e baki balle ya kare kanshi, ya kasa komi ba abunda yake ji sai ciwon kai me azaba da ya addabi kwakwalwar shi, tuni ya saka hannu ya k'ara kama kanshi, yayin da hawaye masu zafi suka cigaba da kwarara akan fuskar shi.

Mami na ganin yanayin shi tayi saurin mik'a mishi maganin da ta shigo dashi da ruwa, kana ganinta gaba d'aya hankalin ta a tashe yake ganinshin da tayi a haka, mutuk'ar tausayin d'an nata take, amma ta dake, ko kad'an bata nuna ba, dan kada ma ya zata bayan shi take bi, abunda yayi dole a hukunta shi, duk son da suke mishi dole su nuna mishi yayi ba daidai ba.

"Ungo, yi sauri kasha, ka tashi muje dan abban  ku ne ya aiko ni kiran ka, dashi da iyayen sakeena na parlor na jiran ka"

Tana fad'a taga yayi saurin d'ago da kanshi, ba zato taga ya saka hannunshi da sauri ya kama hannayen ta, duka guda biyun, ya saka ta sakin magani da ruwan da suke hannunta, sannan ya fara girgiza kanshi,

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now