FINALE

2.7K 198 52
                                    

A sati d'aya da faruwar al'amarin aka cafko jabir, da akayi bin cike an gano harda had'in bakin samuel me gadin su sakeena, shi ya bud'e mishi ya shigo, sannan sakeena ta k'ara tabbatar ma da y'an sanda shine, an zuba police wajan neman shi da Addu'a kuma Allah ya saka aka kamo shi cikin sauk'i, da kamal yaji labarin an kama shi, a guje yayi police station d'in, ranar da ba'a ruk'e shi ba da tabbas sai yayi kisan kai, dan ya daki jabir kamar Allah ya aiko shi, police d'in suma kyale shi sukayi ya daki banza, sai shigowar imran da su abba ne ya saka suka kamo shi da ciro shi daga kan shi, ya kumbura mishi fuska har wasu hak'oran sai da suka zube, abunda ya k'ara bama kamal haushi yarda baiyi nadamar abunda yayi ba, sai ma ce mishi da yayi dan yana santa ne shi ya saka ya kasa kashe ta, yana sane be zurma wuk'ar ba yarda zata tab'a kayan cikin ta, ko ya c'aka a zuciyar ta yarda zurmi d'aya zai kaita har lahira, nan kamal ya k'ara haukacewa yayi kanshi, sai da police sunkai biyar da imran suka kama shi aka fitar dashi daga wurin yana ta huci idanunshi sun k'ad'a sun koma jajaye, farar fuskar shi haka ga jijoyin jikin shi suma sun mik'e tsbaar b'accin rai, yanzu an jefa shi kota, suna saka ran za'a daure shi na shekaru goma da hard labor.

———————————————————

B'angaran sakeena kuma sai da babyn yayi sati uku a incubator sannan aka fito dashi, zoka ga murna a wurin ta, barin ma da aka dank'a mata shi a hannun a karo na farko ta d'auke shi, wani irin san shi taji na ratsa ta, so irin na d'a da uwa na shigar ta, yayin da yaran kamar sa da kamal ta k'ara fitowa, ko kamal ya d'auki so ya d'ora my babyn, likiti ya gaya musu komi ya daidai ta, tare da k'ara dadaja musu su gode ma Allah.

Babyn yaci sunan shi ADAMU, sunan kakan su kamal ana kiran shi da ADAM, sakeena itama a sati ukun nan jiki yayi kyau, domin tana samun kulawa sosai a gurim kowa, daga likitocin, nurses y'an uwanta da kuma mijinta, sai da suka k'ara sati d'aya a asibitin bayan fito da adam daga incubator sannan aka sallame su.

Ansha drama da kamal yaji labari ba gidan shi zata wuce me gidan su zasu wuce domin a k'ara kula da ita tayi kwari kafin ta dawo, da sakeena ta gaya mishi  cewa yayi.

"Wane ya yanke hukun cin?"

Murya a had'e, fuksar shi itama, kallon shi tayi sannan tace mishi mami ce kuma daman shine abunda ya dace, ba sai mutum ya d'auki fushi da ita ba wai Allah dole da had'in bakin ta, daman ita take san zuwa ta barshi, ita dariya ma ya bata, yanzu ko kula ta baya yi, in har yana asibitin to sai dai yayi ta kula d'anshi adam, ba ruwanshi da ita, itama da taga haka ta d'auke shi ta jefar a shara, in ya sauko sa sasanta.

Sosai abun na damun kamal danshi bega dalilin da za'a dauke mishi iyalen shi ba, in kula dasu ne yasan zai iya, in ma bazai iya wasu abubuwan ba ai kawai mami ta basu wata tsohuwan tunda ta sansu da yawa su dunk'a taimaka mishi.

Wani kallo yake binta dashi me cike da takaici da harara yarda yaga tana ta dariyar ta dasu faheema da shaheeda, ita wato kwata kwata abun me dame ta ba, wani haushi ne ya kamashi barin ma yarda ya lura yanzu sam sam bata bin takan shi, sai yayi awani a zaune bata ce mishi k'ala, ko su kad'ai ne a d'aki haka zasu zauna jigum, ga shi dukda yana jin haushin ta bazai iya nisantar kanshi da itama ba, amma kuma baya san yayi mata magana in har suna tare domin yasan fad'a zasuyi, haka zasu zauna suyi ta sacen kallon juna, ko ince yayi ta satan kallon ta, domin ita harka gaban ta kawai take abunda ke k'ara k'ular da kamal kenan.

Da ya gaji haka ya tattara ya tafi wurin mami domin neman mafita dan Allah yasan bazai iya jure har wata d'aya matar shi bata kusa dashi ba, zai kwaru ba d'an k'arami ba, yana isa parlon mami bata nan, haka ya zarce bedroom ya ganta zaune ita da kausar, wani kallo yayi ma k'anwar tashi me ciki da harrara sannan yace ta fit ta basu wuri, ba musu sum sum ta tashi domin ta lura kwanakin nan zuciyr shi a sama take ba wuya kayi laifi, kausar na fita ya tsugunnan ya gaishe da mami, tana gama amsa shi tace.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now