Thirty six

1.5K 152 15
                                    

Tana fitowa daga d'akin kamal ta gansu sun wani k'ara bajewa a cikin parlor d'in, sarah har da kunna tv da kwanciya akan 3 seater, ita kuwa ummeeta ta had'e k'afa d'aya kan d'aya tana danna waya, sai dai suna jin d'uriyar ta sukayi saurin mai da hankalin su kanta, sakeena murmushi tayi musu, sannan a hankali tace

"Kuzo in kaiku inda zaku zauna"

Bata k'arasa zancen ta ba sarah tayi saurin mik'ewa, harda wangale hak'ora dan anga wurin zama, ummeeta kuwa wani kallo ta bita dashi, sannanta k'ara gyara zama,

"Ina zaki kaimu? Dan ni banga wani d'aki ba in banda way'annan guda biyun"

Ta nuna d'akin kamal da sakeena, da suke kusa dana juna, sakeena kuwa maida idanunta kan d'akunan tayi sai da ta k'are musu kallo sannan ta maida kan ummeeta.

"Basu kad'ai ne d'akuna ba a gidan nan, akwai inda muke sauk'e bak'i"

Ga mamakin sakeena sai ji tayi ummeeta ta tuntsire da dariya,

"Banda abinki, ai tunda kinsan dalilin da ya kawo ni gidan nan ai be kamata ki nisantar dani daga mijin ki ba, kamata yayi na dunk'a jin d'umin shi a kusa dani, in dunk'a jin duk mostin shi dan nayi saurin samu hankalin shi ya dawo wuri na, ko ya kika ce sarah?"

Sarah dake tsaye ta saki baki kamar shasha tayi saurin d'aga kai alamun eh, sakeena kuwa itama bakin ta hangame dan abun yayi mugun d'aure mata kai, ummeeta na nufin ita ta sadaukar da d'akin ta kenan ta koma d'akin bak'i ta bar mata nata, har zata bud'e baki tayi magana sai taga umeeta ta ta tashi, rarumo handbag d'inta tayi, sannanta matso dab da sakeena, sakeena kuwa d'aga kai tayi tana kallon ta dan ummeeta akwai mugun tsawo, sai da ummeeta ta nuna d'akin kamal, sannan ta nanad'e hannunta akan k'irjinta tace,

"Mijin ki yanzu ya fito daga wancan d'akin, dan haka ni a na kusa dashi zan zauna, ma'ana hak'ura zakiyi ki bar mun d'akin ki, in yaso na koma d'akin shi da kwana nan da ba da dad'ewa ba sai ki dawo"

Mamaki ne ya kama sakeena, lallai ma wannan, dan kawai ta barta tayi yarda take so shine har ta fara nuna mata isa a cikin gidan ta, ji tayi ummeta ta k'ular da ita, amma sai tayi sauri ta kauda b'accin ranta gefe, ummeta ce kad'ai zata iya raba auran ta da kamal dan hak dole ta bita tayi duk yarda take so, murmushi ta sakar mata, sam sam bata nuna musu ranta a mugun b'acce yake ba, sanna ta furta abinda ya k'ara d'aure masu ummeeta kai,

"In d'akina kike san zama, then fine, zan bar miki ni kuma in koma guest room, yanzu ku ja akwatin ku kai ciki"

Tana maganar tana musu nuni da suyi gaba ummeeta baki a hangame, sarah ma haka haka suka jaa, akwatin su suka shige d'akin sakeena wacce ita tabi bayan su, tana shiga d'akin tayi hanyar closet d'inta ta d'auko k'aton akwati ta ajiye shi a k'asan closet d'in sannan ta far loda mishi kaya, sai da ta cika akwatin tsaf ta abubuwan da zata buk'ata duk abinda take idanun su ummeeta akan ta, tana kulle akwatin ta fito daga cikin closte d'in.

"Ga d'aki nan, ni bari naje na ajiye kaya nan sannan na fito na d'ora muku abinci nasan kun kwaso yunwa"

Tana gama maganar bata jira me zasu ce ba ta fita daga d'akin, tana kulla k'ofar, sarah ta kalli ummeeta,

"Meeta anya yarinyar nan nada hankali? Wani abu be sami kwakwalwar ta ba? Wannan wane irin rashin wayo ne ke d'awainiya da ita"

"Ke da Allah kyale ta kinji, ai ni nafi san tayi ta rashin wayon dan zai saki na cimma burina cikin sauk'i da kwanciyar hanakali"

Tana maganar ta tashi ta fara rage kayan jikinta, tana fad'in bari ita tayi wanka daman ta kwaso rana, sarah kuwa tayi shiru a wurin da ita ta kasa gane lamarin sakeena, abunta na mutuk'ar bata mamaki ba d'an kad'an ba, tayi sakwani a haka sai can ta mik'e, tare da cewa ummeeta,

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now