Fifty nine

1.4K 180 72
                                    

Wani irin mrk'ususu da fara har lokacin hannunta na sakale akan d'anta, ga wani numfashi da take fitarwa a hankali da kyar, tashi take so tayi ta gudu amma ta kasa, tsabar wata azaba da taji tana ratsa k'asuswan ta, kan kice me ta fara ganin biyu biyu, amma a haka ta kafa su akan jabir har ya iso inda take, cikin muryar da da kyar take fita ta fara rok'on rayuwar d'anta,

"J-jabir b-baby na zai m-mutu"

Maganar da tayi kamar k'ara tunzura shi ta tayi, dan idanunshi k'ara kad'awa sukayi suka dawo kamar barkono, cikin muryar da bata d'auke da ko d'igo d'aya na imani, yace.

"Abunda nake so kenan dan bazan tab'a bari ki haifi jininshi ba"

K'afa ya saka ya saisaici  dai dai cikin sannan da k'arfi ya buga ta akai, wata k'ara ta k'ara saki wacce yanzu bata fita ba tsabar azabar da take ji, ko numfashi be tsaya ta maida ba yayin da ya kama tsakiyar kanta ya fara jan ta a k'asa, haka cikinta yayi ta gogar k'asa har suka isa wani d'aki, me kama da guest bedroom da yake a gefan parlon k'asan, dunk'ulewa tayi a wuri d'aya, dan har kuka ta kasa yi, addu'a kawai take a k'asan ranta da Allah ya ceci ran d'anta.

Tsugunawa yayi a gabanta, yayin da ya maida gashin kanta gefe, sannan cikin wata murya da har sai da tsigar jikinta ta tashi kamar zai saka kuka ya fara fad'in.

"Me ya saka kikai mun haka?? Ni nake sanki tsakani da Allah me ya saka kika zab'e shi akan ni"

Ko maganar da yake da kyar take ganewa balle har ta iy bashi amsa, wani irin ciwo ne ke d'awaniya da ita, yayin da ta k'ara damk'e cikin ta, rayuwar d'anta kawai take ji dan gaba ki d'aya ta ji ya daina mosti, tna jin d'anta zai mutu a cikin cikinta amma ba yarda zatayi, wasu siraran hawaye ne suka fara zubowa a fuksar ta yayin da ta shiga addu'a da Allah ya saka wannan mumunar mafarki ne, tana farkawa zata ga kamal ya kawo mata breakfast d'inta har gado kamar harda yake kullum kan ya tafi office.

"Ba kalar wulaqanci da biki yimun ba akan shi bayan ni na cece rayuwar ki, kin kyauta abunda kikayi ?"

Nan ma shiru bata ce komi ba, dan gaba d'aya ta fara fita daga hayyacin ta, ga goshin ta sai zubar da jini yake ta sanadiyar fad'owar ta daga kan stairs, da alamun shirun ta k'ara kular da jabir yayi, dan yarda ya fusgi fuskarta dan ta kalli inda yake tare da matse ta wuri d'aya.

"In ina miki magana ki amsa ni"

A hankali yayi maganar amma cikin muryar da zata saka ka jik'ewa da gumi, ita kanta tana san amsa shi amma ta kasa bud'e baki tayi magana, sai faman ajiyar zuciyar da take da wani irin numfashi me zafi da take fitarwa,

"Ki amsa ni"

wata gigtacicyar tsawa ya daka mata da ta saka ta lumshe idanuta da k'ara kundundune wa wuri d'aya, yayin da ta tsananta addu'a a ranta, dan ta lura jabir baya hankalin shi, Allah ne kad'ai zai cece ta da ran d'anta.

"Nayi nadamar ceton ki da nayi a baya, da na aikta abunda nayi niyar yi da yanzu cikina ne a jikin ki ba nashi ba, da yanzu ni dake muna tare muna jin dad'in rayuwar mu, amma ya ruguza mun komi tare da shiri na"

Cikin fad'a da b'accin rai ya cigaba da gaya mata, tare da k'ara matse fuskarta da sakar mata farcen shi akai kamar yana y'akushin ta yarda yasan zai mata zafi, da zai baka tabbacin baya tare da imani a lokacin, sannan can ya d'an rage ruk'un tare da fara shafa fuskar ta, fuskarshi d'auke da wani yanayi wanda ya k'ara hardasa tsoro a zuciyar sakeena.

"Amma yanzu bata b'aci ba, dan nashigo gidan nan domin in nuna miki ni dabban da kika kira ne da yarda jaki zai iya raba ku da farin cikin ku, zan kasha d'an cikin ki naga uwar abunda mijin naki zai iya yi"

ZAFIN RABO ✔️Kde žijí příběhy. Začni objevovat