Two

3K 182 9
                                    

K'arar horn d'in da taji tunda ga wajan gidan ne yayi firgit da ita, da sauri ta ajiye book din da take karantawa ta duro daga kan gadon tayi cikin bathroom d'inta a guje, cire kayan jikinta ta fara yi sannan ta shiga yin wanka, bata dad'e da fara wankan ba ta ji an turo k'ofar d'akin ta an shigo da mita, dariya ta dunk'a yi amma mara sauti yadda ta cikin d'akin baza taji ta ba, sai da ta gama wankan ta tsab sannan ta fito, jikinta d'aure da towel, tana shiga d'akin tayi sallama da ita tana daka mata harrara harda rik'e kugu, dariya ta saki yanzu dan ta bala'in bata dariya, bata kula ta ba tayi wurin dressing mirror d'in har lokacin k'awartata harara take mata, kallon ta tayi ta cikin mirrior ta sakar mata murmsuhi,

"Kina yin dai dai abun da kike?, tun nawa na kira ki ma nace ki shirya" k'awartata ta fad'a mata,

Ita kuwa ci gaba tayi da abunda take bata kula ta ba, sai da ta gama shafa mayuk'anta tsab ta mik'e tayi wajan drawer d'inta, ta fito da kayan da zata saka, wata doguwar riga ce ta atamfa, tasha stones,

"Aw Ina miki magana ma baza ki kula ni ba, kinsan Allah zan daina biyo miki irin way'annan abun dan kullum kina cikin saka mutum yin letti" k'awartata ta ci gaba da yi mata mita,

Juyowa tayi ta kalle ta, sai a lokacin ta fara shirin yin magana,

"To me zance, ko nayi magana baza ki daina mita ba na riga da nasan halin ki"

Ta fad'i mata tare da fara shirin saka kaya, tana jira taji k'awartata tayi magana taji shiru, itama k'ara share ta tayi ta ci gaba da shiryawar ta, bayan ta saka rigar ta koma gaban dressing mirror d'in ta fara shafe shafe a fuska, ba wata kwaliyar zafi tayi, d'ankwalin kayan ta d'auko ta d'awra akanta, sannan ta feshe jikinta da turare masu laushin k'amahin wanda sai ka matzo kusa da ita zaka ji,

Tayi kyau sosai, kayan sun mata kyau, tana da jiki amma ba sosai ba ga dirin ta masha Allah, shi ya saka bata cika sa kayan ta zasu matse ta ba, kullum tana cikin saka free kaya, kayan da za su saka ta zama comfortable, bayan ta k'ara duba kanta tsab a mirror ta juya wurin k'awartata,

"Shall we" tace mata

Hamida, mik'ewa tayi itama, suka yi hanyar fita daga d'akin bayan ta d'auki mayafi da haka, tambayar ta tayi ko mommy na nan dan ta l'eka ta gaishe ta, cewa tayi a'a ta fita, haka suka k'arasa motar suka shiga, Hamida ce ta kalle ta bayan sun gama saka seatbelt ta kunna motar tare da yin horn dan a bud'e mata gate,

"Kinsan Aliyu zai je reunion d'in?" ta tambaye ta,

Wani irin kallo tayi ma k'awar tata, a lokacin Hamida ta saka hancin motarta tabar haraba gidan,

"Dan Allah dan annabi me yasa kike gaya mun?, me ruwa na dashi"

Girgiza kanta tayi, shegen taurin kai ne da ita, gaba d'aya ta daina kula ko wane namiji tun bayan shi, ta rufe zuciyar ta ruf da kwad'o da muk'ulli ta hana kowa shiga, tak'i bawa kowa chance, haka take son k'arasa rayuwar ta ne, ta tambayi kanta a zahiri ma tambayr tayi mata,

"Wai ke haka kike sun gama rayuwar ki ba namiji ba aure, duk friends d'in mu sunyi aure nima nayi aure, so kike ki zauna ke kad'ai"

D'aga mata kafad'unta tayi,

"Ance dole sai kayi aure ne?, Ina san yadda rayuwa ta take, ba wani tension daga ni sai ni"

Hamida shiru tayi a wurin, sunyi maganar nan ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, kuma kullum the same answer take bayar wa, tana ji baza ta tab'a canza ra'ayinta ba, tana mutuk'ar yiwa babbar k'awartata kwad'ayin gidan miji dan tana son ta mallaki gidan kanta da kanta, ta mallaki yay'anta ta kuma raya sunnar manzo, amma sam sam duk way'annan basa gabanta, k'ara sacen kallan ta tayi ta gefan idanunta taga hankalinta nakan titi,

"Har yanzu baki manta dashi ba? Har yanzu baki hak'ura kin fitar dashi daga ranki ba"

K'ara sacen kallonta tayi, taga ta lumshe idanunta, can ta bud'e su, shiru shiru bata ce komi ba, tayi zatan haka daga wurin ta,

"Shekara takwas yanzu SAKEENA, ai ko wani irin abu kike ji a zuciyar ki yaci ace yanzu kin manta, kinyi moving on"

Nan ma shiru, bata bata amsa ba, sun d'an dad'e a haka sai can ta juyo da sauri ta nuna ya da d'an yatsa,

"Don't spoil my mood, Allah kika k'ara yin maganar shi zan bud'e k'ofar nan na dirga"

Yadda tayi maganar she's very serious, Hamida dariya da saki hade da yin alamun zipping bakin ta, tana bala'in son aminyar ta, tana son farin cikin ta, ta san ta ciki da bai, tana ji ma duk duniya ba wanda ya santa kamar ta, shi ya saka take d'an d'aga mata k'afa wani lokacin, ba wanda ya k'ara cewa komi har suka isa harabar restuarant d'innan me suna Tulip Bistro da yake a wuse 2,

Class mates d'insu duk na waje na jiran kowa ya gama isowa tukunnna, suna parking, suka fito, matan suka fara iho suna rugume juna, yadda dai mata suke in sunga k'awaye, ga dama an dade ba'a had'u ba da wasu,

SAKEENA Kallon Hamida tayi,

"And you were complaining munyi letti, gashi da yawa basu gama zuwa ba"

Share ta k'awartata tayi, ta ci gaba da gaisawa da abokan nasu, SAKEENA kawai girgiza kanta tayi, basu dad'e a tsaye ba wasu suka k'ara zuwa a lokacin kawai sukayi deciding su shiga ciki su jira suaran, daman sunyi renting gaba d'aya wurin.

Bayan anci an sha, suna zaune suna hira wasu na d'aukar pictures, ita dai sai jefi jefi take magana dan bata cika san surutu ba, ga a tukure take saboda ta lura idanun wani tunda suka shiga yana kanta, fuskarta a d'aure take sosai dan kadama ya sami damar yi mata magana, Hamida ce ta tab'a ta tare da yi mata rad'a na Aliyu ya kasa sauke idanunshi daga kallanta, daka ma k'awarta harara tayi, duk had'e fuskar ta da take yi a banza, dan kawai ganin mutum tayi a gabanta yana sosa k'eya, k'ara shan kunu tayi ta had'e girar sama da ta k'asa,

"Dan Allah d'an minti d'aya"

Wani irin haushin shi taji a lokacin, eh tasan sunyi soyayya da suna secondary school amma a ganinta a lokacin soyyayyar yarinta sukayi, kowa ya manta yanzu yana harkar gaban shi, dan kawai ita kad'ai ce bata da aure a cikin su bai bashi damar da zai zu ya fara yi mata maganar banza ba, baza ta tab'a gane maza a rayuwar ta ba, ita ta manta dashi wallahi dan sun dad'e rabon su da juna, da taga dukda tayi shiru tayi banza dashi bai bar kanta ba, ta d'aga kai ta kalle shi cikin kwayar idanunshi,

"Ajiya ka bani da kake son gani na?,"

Kowa na wurin saida ya bar abunda yake yi saboda yadda tayi maganar ya juya yana kallan su, wurin yayi tsit, har shi na tsayen shima yayi shiru ya kasa bud'e baki yayi magana, k'ara kafa mishi idanu tayi tana jiran amsar shi, da taga bashi da niyar yin magana, da k'ara da cewa,

"In baka da amsa zaka iya matsawa daga kaina, dan zaka samun ciwon kai"

Tare da yin alama da hannunta na ya matsa, sauran y'an wurin sakin baki sukayi suna kallonta, tasan wane shi kuwa, yaro da kud'i wanda matan abuja ke rububi, AK kenan Aliyu Kabeer, yaro me wasa da naira, tsabar yadda abun ya bashi mamaki dariya ya saki, sannan ya bita da wani mugun kallo ya fice daga wurin, tana gani mazan wurin suka bishi suna bashi hakuri, yana ta zuba iho a wajan wurin yana cewa,

"Ni zatayi embarrassing??, ni zata wulaqanta a gaban mutane, wallahi zan nuna mata ni wane"

Banza tayi dashi, ta d'auki lemonade d'inta ta tayi sipping, ita a ganin ta ba wulaqanta shin da tayi, kawai ta gaya mishi abunda ke cikin ranta, Hamida kuwa hankalinta a tashe tana ganin ya hau motar shi ya jaa ya bar wurin ta kama hannunta sukayi waje suma bayan tayi wa sauran abokan nasu sallama.

(Anyi intro d'in KAMAL anyi na SAKEENA, next chapter sai a fara littafi)

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now