Forty eight

1.8K 194 48
                                    

Tana kwance akan gadon ta, rigar bacci da wandon ta na 3 quarter yayin da wayar ta na hannunta, tunda ta dawo daga gidan hamida awa uku da suka wuce bata tab'uka komi ba, in banda sallar da tayi, sai kuma faman dannan waya, wataninta takwas bata shiga duniyar social media ba, dan haka yau baza tayi bacce ba har saita ga komi da tayi missing.

Dukda rabin tunanin ta na wurin had'uwar ta da kamal d'azu, ga ba abunda take so irin ta manta shi, ko da tana gidan hamida sai da ta tambaye ta me ya same ta dan gaba d'aya hankalin ta na wani wuri, da kyar dai ta samu ta shirga mata k'arya da ta saka ta kyale ta.

Kamal ya raba ta da nutsuwar ta yau, ya raba ta da sukunin ta, ta tsinci kanta acikin yanayi da baza ta gab'a iya misaltawa ba, bata tab'a sanin, haka ya iya zaro zance ba sai yau, daman duk shiru shirun nashi da miskilanci nashi na munfinci ne, ashe shima idanunshi a bud'e suke yasan yarda zai raba mace ta hankalin ta, shi ya saka ashe mata ke rububun shi da hauka akan shi, ji tayi wani haushin shi ya kamata ta, me za'ayi wa wannan bakin nashi ya dena bud'e shi dan duk maganar da zata fiti daga cikinsa bata lafiya bace ba a wurinta.

K'arar da wayar ta tayi ce ta dawo da ita daga duniyar da take, saboda yarda k'arar tayi mata ba zata bata san lokacin da ta saki wayar ba ta fad'o mata akan fuska, mik'ewa tayi daga kwanciyar tana mulmula goshin ta sabida yarda taji zafi, bak'uwar number d'in da ta gani ya saka ta yin durus dan bata san numbar ba, a hankalinta d'auka ta saka a kunnenta, tana shirin taji anyi magana daga d'aya b'angaran dan ita bata da shirin magana saboda bata san wane ba, amma sai taji tsit, an kusa minti d'aya a haka har sakeena ta d'aga wayar daga kunenta dan dubawa ko layin ya tsinke, amma taga still kiran na tafiya, tsaki taja zata kashe dan a zatan ta wani d'an ranin hankalin ne amma sai ji tayi ance.

"Bakiyi bacci ba"

Tana jin muryar gabanta yace dum, zuciyar ta ta fara bugawa, mutum d'aya ne duk fad'in duniyar nan zai iya magana cikin salon nan, da zai saka zuciyarta a take ta burkice tare da saka ko wace gab'a a jikinta sagewa, da kyar ta iya tattaro nustuwar ta, sannan a hankali tace,

"Ina ka sami number d'ita?"

Ji tayi yayi wata ajiyar zuciya, yayin da itama ta saka hannunta a k'irjinta wai ko zuciyar ta zata daina hauka,

"Kin manta kausar da kamila k'anne na ne, suna da number d'inki"

Lumshe idanunta tayi, yanzu ta shige su dan tasan tana ruwa da ya sami number d'inta, haka zai ta dunk'a kiranta yana mata maganganun da wannan muryar tashi me suburbud'a jama'a, ga a waya ma ta taji k'ara wani irin fitowa da k'ara zama deep da dad'in sauraro, saurin girgiza kanta tayi da taga ta fara tunani da zai tayar mata da hankali,

"Me ka kira ce mun?"

Cikin fad'a fad'a da tsiwa tayi tambayar, dan ta fara gajiya da shi, da sababbun abubuuwan da take ji a can cikin jikinta game dashi, shiru yayi kamar bazai amsa ta ba, sai can taji yace,

"Me ya saka d'azu biki wuce gida direct ba kika ce kausar ta sauke ki a life camp, wurin wa kika je?"

Oh daman kiranata yayi ya tutsiye ta, saboda bata sanar dashi inda zata ba?, wani takaici da haushin shi ne ya k'ara kamata, lalai ma wato, ita kuwa baza su tab'a shiryawa ba in har yace wannan halin nashi zai cigaba dayi, na juyata kama y'arshi dan a ryuwarta ba abunda take so irin mutum ya dunk'a bata space yana respecting d'inta, ji tayi kamar an k'ara tunzura ta.

"Dole in zanje wani wuri sai na gaya maka?"

"Kin manta har yanzu ni mijin ki ne?, dole ki tambaye ni na baki izini in zaki fita"

"Ka manta zaman ka mijina yana hannun na, kowa jira yake na yanke hukunci game da kai"

Tana kai ayar maganar tayi saurin cizar l'ebanta, dan ita kanta tasan baya san irin maganganun nan, tana jin ya fara fitar da wani numfashi ta wayar, alamun ta kunno shi, yafi minti biyu yayi shiru yak'i cewa komi, ba abunda take ji a kunnan ta in banda saukar numfashin shi, alamun ranshi a mutuk'ar b'ace yake, sun dad'e a haka ba wanda ya cewa kowa komi, sakeena kuwa cikinta fal yake da dana sanin abunda ta fad'a, dan tasan abunda tace yayi mutuk'ar yi mishi ciwo, amma ai shine, ya san yarda zaiyi ya b'ata mata rai ya saka ta fad'i abunda batayi niya ba, tana jiran taji yace wani abu kawai taga ya kashe wayar.

ZAFIN RABO ✔️Où les histoires vivent. Découvrez maintenant