Nineteen

1.4K 135 10
                                    

Banka k'ofar palor yayi yana isa gida, har lokacin jin wani irin k'unar rai yake, ga zuciyar shi da bata bar tafasa ba, maganganun da ta gaya mishi sai yawo suke yi a kunnan shi, ta bala'in raina mishi hankali, yana shiga bedroom dinshi ya fara cire kayan jikin shi sannan ya fad'a bathroom ya watsa ruwa ko ya rage jin abunda yake ji, yana fito wa kug'un shi dauke da towel d'aya kuma a hannunshi yana goge jikin shi har ya isa makeken standing mirror d'inshi, kallon kanshi ya shiga yi, idannunshi basu dawo kalar su ba har yanzu a jaa dinsu suke, ga fuskar shi itama da har lokacin a had'e take, alamun ranshi har lokacin a b'ace yake, wani irin wurgi yayi da towel d'in hannunshi tare da d'ora hannunshi akan sumar kanshi, ya jaa da k'arfi, shi ta kalla ta gaya wa wannan maganganun, haka ya fara yin yawo a cikin makeken bedroom dinshi, tunani ya shiga yi me zai yi mata da zai mutar mata da wannan taurin kan nata tunda yaga abunda ya saka a mata kamar bai girgizata ba, can wani abu ya fad'o mishi, sauri yayi yayi wurin daya jefar da kayan shi tare da d'aukan su da fara laliiban wayar shi, yana d'auka yakai kan lamabar hajiya maimuna, bai dade da fara ringing ba ta dauka,

"Dawo da ita gida, yanzu zan yi miki sending address d'in"

Yana gama fad'a ya kashe wayar tare da shiga cikin closet d'inshi, bayan ya aika mata da address d'in, ya d'auko wata farar riga da wani farin sweatpants ya saka sannan ya feshe jikin shi da turararuka masu dad'in kamshi, yana gama abunda zaiyi ya fito yayi hanyar parlor, ya kunna tv yana jiran news da kuma jiran daowar ta, daman yayi sallar isha dinshi a masallaci, bai ayi awa biyu ba a zaune sai ga horn, kamal a hankali ya mik'e yayi wurin window d'in da yake kallan gate d'in gidan, yana gani security ya tashi ya bud'e k'ofar, sannan motar ta cuso kai har tayi parking a gefan tashi, yana gani hajiya maimuna ta fito, maida kallan shi yayi front seat d'in motar yana jiran yaga fitowar ta, amma shiru, har yaji k'arar doorbell, a hankali ya fara takawa har ya isa ya bud'e kofar amma har lokacin hankalin shi na kanta, so yake ya koma ya cigaba da kallanta ta window yaga taurin kanta zai barta ta fito ko kuma a'a,

"Gata na kawo maka ita, ga kuma wayar da ka kawo mun d'azu"

Kamal kawai d'aga kanshi yayi, had'e da mata nuni ta ajiye wayar akan center table, yana ji ta matsa ta ajiye wayar, ya cigaba da jiran fitar ta amma yaji shiru, d'auke idanunshi yayi daga kallan da suke ma sakeena da take cikin motar tare da maida su kanta, ya fara mata kallon me kike har yanzu a cikin gidana, can wani abu ya fad'o mishi, kud'in ta take jira ne?

"Kan ki k'arasa gida zan aika miki da balance d'in kud'in ki"

Yana gama maganar ya maida kallon shi waje, har yanzu bata fito daga motar ba, tana zaune a ciki tayi shiru, haka ya cigaba da zuba mata kallo maganar da hajia maimuna tayi ce ta dawo dashi daga duniyar da yake,

"Wai dan Allah na tambaye ka?"

Bata jira amsar shi ba ta cigaba da cewa,

"Me ya saka kake wa yarinyar nan haka ne, me tayi maka?"

A hankali kamal ya juyar da kanshi tare da sauke mata wata muguwar harara, fuskar shi ta k'ara had'ewa, wacce ita da zatayi mishi tambayar nan,

"Ki fitar mun daga gida malama, nace zan aiko miki da ragowar kud'in ki"

Murya a had'e yayi magana, ko hajiya maimuna da take babba sai da ta d'an ji dum, wani irin kwarjinin shi ya rufe ta, ta kasa k'ara bud'e baki tayi magana, haka ta juya sum sum tayi hanyar waje, kamal najin k'arar kulle k'ofa ya maida kallan shi kan window, yana gani hajiya maimuna tayi hanyar front seat, tare da bud'e k'ofar, baisan me tace mata ba, sai gani yayi ta jawo hannunta daga cikin motar ta cilla ta gefe har sakeena na shirin fad'uwa, tare da daka mata wata harara, sannan ta koma driver's seat ta bud'e ta shiga tayi wa motar key ta tashe ta ta bar harabar gidan.

K'ara nanad'e hannunshi yayi a fad'ed'an k'irjin shi, ya bita da kallo, jira yake yaga zata shigo ko kuma a'a, a tsayan da aka barta a wurin haka ta tasaya har na tsawon awa d'aya, kamal shima da yake tsaye yana kallonta har na tsawon lokacin ya dauke idannunshi dake kallan agogon dake manne a parlor d'in, sannan ya k'ara maida su kanta, yana gani ta sami wuri a kusa da wasu flowers ta zauna, da yaga ta zauna abun ba k'aramin d'aure mishi kai yayi ba har sai da ya saki murmushi, tunda yake a rayuwar shi bai tab'a ganin mace mai shegen taurin kai ba kamar ta, wato bata da niyar shigowa,

"Bari mu k'ara bata minti talatin mu gani"

Ya fad'i a zuciyar shi, a haka ya k'ara tsayawa yana kallanta har 11 na dare yayi, wata dariya ya saki da yaga lokaci, da gaske take baza ta shigo ba, ta gwamace sauro da k'waruka suyi ta cizan ta, tabbas wannan budurwa kamil ce dan irin matan da yake so kenan, matan da are very stubborn, wurin intercom yayi sanan ya danna ya kira mai gadin shi, ba kashidin da bai mishi ba da ya tabbata idanunshi nakan ta in har bata shigo ba, kada ya saki yayi bacci in ba haka ba a bakin aikin shi, yana gama wa ya koma bedroom d'inshi ya fara shirin bacci.

Ko bayan yayi sallar asuba da ya fito baiji alamun ta ba, mamkinta ne ya k'ara kamashi, a hankali ya taka har ya kom wurin window, tana nan a zaunen da ya barta jiya da daddare, wani abu yaji ya taho tunda ga tafin kafarshi har kanshi, ko shi da yake namiji baya ji zai iya kwana a zaune a kuma waje, duk taurin kanshi yasan bazai iya ba, haka yaga ta k'ara kudundine jikinta ta k'aton hijab d'in da take sanye dashi, girgiza kanshi yayi sannan ya koma bedroom d'inshi, tunda abunda take so kenan ai sai tai ta zama shi mene nashi, yana hawa kan gado yaja MacBook d'inshi yayi aikin da zaiyi, can kuma ya koma bacci bai tashi ba sai 12, ko da ya tashi bathroom yayi, ya tsara wankan shi ya fito ya shirya cikin wani blue jeans da gray shirt, ya feshe jikin shi da turare, sannan ya fito dan zuwa masallaci ana ta kiran sallar azahar, sai da ya k'ara tsaya wa ta window, yaga ko tana nan amma yaga wurin wayam, gabanshi ne ya fad'i, da sauri yayi hanyar k'ofar waje dan kada yaje da sami hanyar guduwa, yana bud'e k'ofar yaji an bangaje shi da k'arfi anyi cikin gidan a guje, da hannunshi baya ruk'e da handle d'in k'ofar da sai yaji shi a k'asa, haka ya tsaya ya bi bayan sakeena da kallo wacce da gudu tayi cikin bedroom d'inta.

(Sakeena ta dawo gidan kamal sai masu karatu suyi shirin kwasar drama,

Dont forget to vote, share and comment ♥️♥️)

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now