Fifty three

1.8K 174 27
                                    

Yarda ta k'ankame shi ko mosti kwakwara ya kasa yi, so yake ya tashi ya had'a musu ruwan wankan amma ta hanashi, shi kuwa ya kasa saka k'arfinshi akanta, dan yarda yake jin jikinta yayi rau da zazzabi, ga wani irin rawa da jikinta be bar yi ba har lokacin.

K'ara jawo ta jikinshi yayi yayin da ya k'ara rufa mata bargo, idanunta na lumshe amma yasan ba bacci take ba, tsabar gajiya ne da yarda jikinta ya zama extremely weak, haka suka kwanta har na tsawon minti sha biyar, ba abunda yake ce mata sai ta sumbatar gashinta da fuskarta da yake duk bayan sakwan biyu, da shafa bayan ta shima a hankali.

Kanshi ya d'aga yaga k'arfe goma ta gota, in har ya biye mata ya tabbata dare zaiyi sosai suna kwance a wurin nan, idanunshi ya maida wurinta yaga yarda ta k'ara shigewa jikinshi, ajiyar zuciya kamal yayi, sannan a hankali ya fara motsawa tare ta d'aga ta cak daga kan gadon, sai ta tayi d'an making sound kad'an na ciwon da take ji wanda da kyar ya fito sannan ta k'ara shigewa k'irjinshi, a hankali ya fara takawa tana hanunshi har suka shiga bathroom.

Zama yayi a gefan bathtub yayin da yake had'a mata ruwan zafi ko zata ji dad'in jikinta, yarda suke zaman har lokacin tana kan cinyarshi tayi lamo, ko da ya gama, ya d'aga ta zai saka ta acikin bathtub d'in bai yuwa ba, dan k'ank'ame wuyan shi tayi kamar jaririya, tak'i sakin shi still, kamal ajiyar zuciya yayi, dole ya shiga ciki ya zauna, ya saka ta a tsakanin k'afunfunshi tare da jingina bayan ta da k'irjinshi, ko ruwan ya mata zafi bata nuna alamu ba dan har lokacin jikinta na mace.

Sun zaune a haka sunyi shiru ba wanda ya cewa wani komi, kamal ya ruk'e ta gam a jikinshi shima tare da ruke hannayen ta, ga lips dinshi da basu bar kissing d'inta ba a ko wane lokaci, a cikin wani irin yanayi yaki jinshi da take jikinshi haka, wani irin masifafan abunne ke d'iban shi har yanzu be gama jinya dawo dai dai ba, amma dole ya sarara mata sakomakwon jin jikin da tayi a hannunshi, haka ya hak'ura ya danne duk wata masifa da yake ji, k'ura ma fuskarta wannan rikitatun mayun idanunaahi ko k'iftawa baya yi, wani irirn jinta yake da santa yabi ko wani kusurwa da lungu na jijiyoyin shi, ya shiga jinin jikinshi, masifar kaunar ta yaki ji a can cikin zuciyar shi, yarda yanzu ta zama baban farin cikin shi, shi ya manta yarda yayi rayuwa a baya ba ita dan yanzu baiji zai rayu in har bata tare dashi.

Sunfi minti shabiyar a haka, har ruwan ya fara sanyi, ita kuwa tayi shiru, numfashin ta ya fara yin dai dai da alamu bacci ya fara gaba da ita, kamal tab'a jikinta yayi yaji shi zafi gau, kamar ana hura wuta, wani irin tausayin ta yaji ya dakar mishi zuciyar, shi kanshi yasan tana bala'in k'okari dan ba ko wace mace bace zata iya juriyar da take.

A hankali ya fara shirin mik'ewa, dan ya canza ruwan dan wannan ya fara sanyi, ko da taji ya fara shirin barin jikinta hannun ta saka ta k'ara ruk'o shi tare da k'ank'ame shi, ta k'ara sakin wani d'an sauti me ciki da shagwab'a, gajiya da ciwon zazzab'in dake d'awaniya da ita, tuni kamal ya k'ara rikicewa, tare da k'ara janta a k'irjinshi, haka suka zauna har sai da yaji bacci nata yayi nisa sannan ya k'ara gwada mik'ewa, wannan karan kuwa ya taki sa'a, jinginata yayi ta bathtub d'in sannan a hankali ya fito daga cikin ruwan ya k'ara canza wani.

Wani nishi ta saki da taji d'umin ruwan na k'ara ratsa ta, kamal bai san lokacin da ya saki murmushi ba, dan a lokacin k'ara jin wani santa yayi shima ya ratsa shi, sai da ya gama had'a ruwan,, sannan ya koma  wurin da take, ya zauna a saman bathtub d'in sannan ya d'ora kanta akan cinyar shi, yana shafawa a hankali.

Sun kwashi kusan awa d'aya band'akin, lokacin da suka fito sunyi wankan su tare da tsarkake jikinsu, suna sanye da bathrobe, ita kuwa tana hannunshi, suna shiga bedroom d'in ya tsaya cak sakwamakon yarda yaga gadon nasu yayi kaca kaca ba daman ajiye ta anan, samun wuri yayi ya kwantar da ita akan wata sofa da take a cikin d'akin, remote ya d'auko da rage sanyin ac, sannan yayi wajan drawer da yake ajiye kaya ya rarumo wata shirt d'inshi da yasan zata iya kai mata har gwiwa, wucewa yayi wurin dressing mirror ya kwaso body oil da wasu ointment sannn ya dawo kusa da ita.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now