Twenty six

1.4K 161 19
                                    

Tana fita daga d'akin shi d'akin ta tayi a guje, tana shiga ta kulle k'ofar tare da zubewa a kusa da gadon ta, wani irin kuka me mugun abun tausayi ta saki, bayan ta toshe bakinta dan kada bak'in gidan suji, kuka take yi sosai kukan irin cin mutuncin da kamal yayi mata, ita ya kira ragowar wani k'ato, tunda take a rayuwar ta ba wanda ya tab'a bud'e baki yayi mata irin wannan wulaqanci sai shi, ba abinda yaka k'ara mata ciwo shine yarda yayi mata abinda yayi mata bayan gwaninta da hidimar da tayiwa k'ananishi, sa kanta tayi a cikin cinyoyinta ta cigaba dai rairai kukanta, ba abunda ke yawo akanta irin kalaman kamal, wanda suka tsaga cikin zuciyar ta suka shiga sukayi mata tabo mai mugun zafi, ya zatayi da rayuwar ta ne, ta lura ba abinda yake so irin ya k'untata mata, kuma yana yin aiki mai kyau dan yanzu ta manta rabon da tayi farin ciki, wasu hawayen ne suka sake zuba, haka ta k'udindina kanta tana ta kuka har bacci yayi awan gaba da ita dan tayi mugun gajiya.

Jin alamun ana tab'a ta ne ya farkar da ita, a hankali ta bud'e idanunta ta ci karo da fuskar kamal, wanda yake shirin d'aukan ta cak daga inda take a tsugunne a bakin gado, sakeena da wani mugun sauri ta mik'e har ita da kamal na buge goshi, dan suna dab da juna, ita bata ji zafin karon da sukayi ba amma tana gani shi ya kama goshin shi alamun wurin na mishi zafi, jan gefe tayi ta tsaya ta bishi da kallo har sai da ya gama murgususun shi ya mik'e daga inda yake, suna had'a ido taji wata irin tsanar shi ta k'ara bugar ta a zuciya, zaiyi magana tayi saurin katse shi,

"Me kazo yi a d'aki na bayan ka gama yanka ta da kamalan ka masu mugun dafi"

Tana gani ya lumshe idanunshi bayan ya ci gaba da mulmula goshin shi da yanza yayi jaa saboda farar fuskar shi, ji tayi yayi ajiyar zucya bayan ya bud'e idanunshi, sannan ya nanand'e hannunshi a fad'edan k'irjin shi yarda kullum yakeyi, ya fara ce mata,

"Bazai yu mu raba d'aki ba yau kinsan su kausar na gidan nan bana so..."

"Na yi musu tarb'a iya k'okarina, na kyautata musu tunda suka taka k'afar su a gidan nan, nayi musu abunda zan iya, bazan iya zuwa d'akin ka ba in kwana dan yanzu ba abunda na tsana irin ganin fuskar ka, ka fitar mun daga d'aki"

Sakeena ta katse mishi zance, yarda tayi maganar a hankali, amma cikin fad'a da tsawa, bayan hawayen da suka cika mata idanunta taf, ga k'ok'arin da take kada ta sake su, jira take taga ya juya yayi hanyar k'ofa amma taji shiru, ganin fuskar shin da take a lokacin k'ara tunzara tayi, ta tsane ganin shi, ta tsane shi, bata san lokacin da ta k'ara wata maganar ba cikin mahaukacin iho,

"KA FITAR MUN DAGA D'AKI NACE"

yanzu hawaye sun fara zuba a idanuta, ihon da tayi ya saka kamal zaro manyan idanunshi waje bayan ya juya da suari ya kalli k'ofar a tsoarace, tare da saurin yin kanta, sakeena baya ta k'ara jaa da taga yana k'ara matsowa, maganar da tayi ce ta tsayar dashi cak,

"Kana k'ara taku d'aya zan k'walla k'ara yarda k'anan ka na waje zasu ji na tabbata kasan me ake kira da sharrin y'a mace"

Zaro manyan idanunshi ya k'ara yi waje, fuksar she d'auke da abun mamaki, ita kuwa sakeena ba abunda ke zuba a fuskar ta sai hawaye masu mugun zafi, idanunta sunyi jaa ja wur ga tsana d'auke a cikin su, a hankali taga kamal ya fara jan baya, sai da ya k'ura mata ido na tsawan mintoci, ita kanta a lokacin bata san me yake tunani ba dan ya saka wannan poker face d'in tashi, sai da ya k'are mata kallo sannan ya juya zai fita, sai da ya kusa wurin k'ofa sannan ta k'ara dakatar dashi,

"Daga yau ka k'ara tab'a ni bada izini na ba sai na tona maka asiri, sai na gaya ma duniya kai wani irin mugun namiji ne, sai ko ina a k'asar nan sun san kai wana irin azalimi ne"

Duk tsanar da take mishi sai da ta saka a cikin maganar ta, a tunanin ta zai zuyi ya mata wata muguwar maganar sai gani tayi ya cigaba da tafiyar shi har ya fita daga d'akin bai juyo ya kalle ta ba, tana jin k'arar kulle k'ofa, tak'ara fashewa da wani kukan.

------------

Sai da ta shirye tsaf cikin wata straight gown me mugun kyau wacce ta fito da dirin ta ta ko ina sannan ta fito daga d'ak'in, kana ganin fuskar ta kasan ba lafiya ba yarda manyan idanunta suka kumbura suntum tsabar kukan da tasha daran jiya, duk da ta cika kwalli a idanunta kallo d'aya zaka yi mata ka gane, kitchen ta nufa ta fara fito da ganda ta d'aura a pressure cooker sannan ta shiga aikin yin breakfast, tasan su kamila na dab ta tashi, ko k'dan kamal bai fad'o ranta ba dan yanzu baya gabanta kuma ta tabbata yana office, ta kusa kamala abincin sai gani tayi an turo k'ofa an shigo, kamila ce a tsaye tana mata murmushi, itama murmushin ta saki,

"An tashi lafiya?"

Sakeena ce ta fara mik'a gaisuwar ta, kamila murmushi ta cigaba da yayi yayin da ta matso har kusa da ita,

"Ya gajiya?, ya kamal yace mana jiya kin kwanta da wuri saboda gajiyar da kikayi"

Yarda taga ta amsa ta ya bata tabbacin basu jiyo hayaniyar su ba ita da kamal jiya,

"Ina shiga d'aki bansan lokacin da bacci yayi gaba dani ba" tayi maganar tare da k'ara jaddadda k'aryar kamal,

Kamila murmushi ta saki tare da yin kusa da ita, "sannu ai mu kanmu munsan mun gajiyar dake"

Murmushi tayi, bata ce mata komi ba ta juya ta ci gaba da kwashe suyayiyar duyar da ta d'ora, tana cikin aikinta bata ankara ba taji an jawo hannunta,

"Lafiya??? Kinga yarda idanunki suka kumbura"

Kamila ta fad'i cikin tsan tsan damuwa yarda taga gaba d'aya manyan idanun sakeena sun kumburo ya bata tsoro, sakeena dariya tayi,

"Gajiya ce ta saka na kumbura, ai ni daman haka nake"

Yarda tayi maganar zaki rantse da Allah gaskiya ta fad'i, ganin haka ya saka kamila ajiye zance ta cigaba da taya sakeena hira da wasu aiyukan har suka kamala abinda suke suka kai dinning, sun fara karyawa kenan sai ga kausar ta sauko, cikin rigar da wando kanta ba d'ankwali, gaishe su tayi sannan ta sami wuri itama ta zauna, sai da itama ta tambayi sakeena idanunta, ta k'ara mata same amsar da ta bama kamila, sai da suka gama cin abincin tsab suka taya ta wanke wanke, bayan sun kod'a iya girkin ta har kamila nace wa zata zo lesson suna ta dariya dai, haka har suka dawo parlor.

Tv a kunne suna hira jefe jefe, sakeena bata cika saka musu baki ba dan tunanin da ya cika mata kanta ya ishe ta, kausar ce ta tab'o ta wacce tana can wata duniyar,

"Ya sakeena ina ta magana, tunanin me kike haka?"

Saurin saka murmushin yak'e tayi kamar ba abunda ke damunta, "ba tunanin da nake, me kika gani?"

Girgiza kanta tayi, "nace anjima zaki je gidan gaisuwa?? Ya kamal zai kaimu sannan ya ajiye mu a airport"

Ji tayi gabanta ya fad'i da aka ambaci kamal, yanzu ko sunan shi bata san ji balle wani abu ya had'a su, zata amsa da a'a kenan kamila ta ruga ta,

"Kausar wannan wace irin tambaya ce, kinsan ai zata je ba sai kin tambaye ta ba"

Shiru tayi, dan yanzu an kulle mata baki ba daman cewa a'a, kausar murmushi tayi har da y'ar murnar ta, nan suka kama wata hira yanzu kam sakeena na sauraron duk abinda suke cewa.


(Please vote, share and comment ❤️❤️❤️)

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now