Ten

1.8K 140 3
                                    

Shirye shiryen bikin Kamal akeyi gadan gadan saboda ba wani isashen lokaci, kowa yayi busy, shi kuwa ba yarda baiyi ba yai convincing d'insu ayi kawai d'aurin aure akai ta amma sam sam mami tak'i yarda, ba k'aramar drama sukayi ba da yace mata ba a abuja zai zauna ba a kano zai zauna, da ga baya ta bari da ya samu aiki a CBN, kuma branch d'in kano, ya gama plan d'inshi na tarwatsa rayuwa Sakeena, kuma insha Allah ba wanda zaiyi mishi cikas, zai kaita inda bata da kowa ya dai zaiji dad'in yi mata duk abinda ya ga dama.

Yana kwance akan 3seater d'in parlor d'inshi, remote a hannun shi yana ta canza channel, k'afa d'aya kan d'aya, yaji an banko k'ofa da wani mugun k'arfi, kai idanunshi wurin yayi yaga imran a tsaye a bakin k'ofa, yana ta huci, Kamal saurin mik'ewa yayi daga kwanciyar da yayi a lokacin imran ya shigo har inda yake, zai bud'e baki yayi mishi magana kawai yaga imran ya cillo mishi wani abu, sannan ya nuna abun da d'an yatsan hannun shi,

"Yi mun bayani me nake gani a katin nan, Kamal wa kake shirin aura?"

Da mugun ihu yayi maganar har sai da ya saka Kamal lumshe idanun shi da saka hannun shi a kunnen shi, sai can ya bud'e su ya sauke akan imran, daman yana jiran lokacin nan, lokacin da imran zai san wace zata zama matar shi,

"Gashi kana ganin sunanta b'aro b'aro a jiki, me kuma ya saka kake san in k'ara maka bayani"

Kamal ya fad'a tare da gyra zaman shi hannun shi ruk'e da katin bikin shi, duk yarda yake da imran bai isa ya ruguza mishi shirin shi ba, yana gani abokin nashi ya saka hannun shi a k'ugu tare da ciza leb'anshi,

"hanklin ka d'aya kuwa? kasan wace ita ka kuma fi kowa sanin matsayin ta a wurin Kamil amma har kake shirin ka aure ta?"

Yanzu kuma da aka ambaci sunan Kamil ya had'e fuska kama bai tab'a dariya ba, tashi yayi dan ya bar wurin saboda imran ya fara shirin b'ata mishi rai, kan ya fara taku abokin nashi ya fisgi kwalar rigar shi, wani irin mugun kallo Kamal ya sauke mishi, kana gani kasan ranshi yanzu ya b'aci,

"Daman maganar ta da kazo yi mun a gida last week abunda kake shirin yi kenan?"

Kamal sa hannun shi yayi ya fisgi rigar shi, sannan yabi imran da kallo, kallon harara yake mishi dan bala'in haushin shi yake ji a lokacin,

"Bazan matsa daga wurin nan ba sai har ka bani amsar dalilin auran ta da zakai, dan nasan ba santa kake ba"

Yarda imran yake maganar shima ranshi a mugun b'ace yake, amma duk zafin shi bai kai Kamal ba, kowa yasan yarda yake in har ranshi ya b'aci, amma dole ya a jiye duk abunda yake ji gefe ya tsara abokin nashi dan yanzu zai iya yi mishi aikin aika aika yaje ya gaya ma mami, kallon abokin shi yayi da wannan manyan idanun nashi, da sunyi jaa ja wur yanzu saboda b'acin rai,

"Sonta nake"

Imran hangame baki yayi ya bishi da kallo tsabar yarda abun yayi mutuk'ar bashi mamaki, shi kuwa Kamal in ka ganshi baza ka tab'a zata k'arya yake yi ba, idanunshi sunyi narai narai da su kamar har cikin zuciyar shi yana son sakeena, kallon juna suke shi da abokin shi yasan imran so yake ya gano in har k'arya yake mishi, abunda shi kuwa bazai tab'a bari ba,

"Tun ran da na fara ganinta, shine sanadiyar zuwa wurin ka da nayi"

Imran shiru yayi kamar yana nazarin wani abu, Kamal da yaga kamar abokin nashi ya fara yarda dashi yayi saurin samun wuri ya zauna akan kujera tare da ma abokin nashi nuni na shima ya zauna, sai da imran ya zauna sannan ya fara ba shi labari, k'arya ya shirga mishi tare da tsara shi yadda ya tabbata imran ba zai yi zargin shi ba, yarda abokin nashi ke kallan shi ya nuna mishi ya yarda, wani dad'i ne ya kama Kamal da farin ciki har tsalle yayi acikin zuciyar shi,

"Still, i dont think its right" imran ya fad'i a sanyaye,

"Kai a ganin ka wa yafi cancanta ya aure ta duk fad'in duniyar nan?, tunda baza ta tab'a kasancewa tare da Kamil ba na tabbata zai so ace ni na aure ta"

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now