Fifty five

2K 185 37
                                    

Bak'in ciki, takai ci, kishi, da ciwon cin zarafin shi da tayi duk suka had'u suka ma jabir yawa, ranshi k'una da tafasa yake, wata irin k'iyaya yake yi ma kamal wanda duk rayuwar shi be tab'a tsanar wani kamar shi ba, ganin yarda sakeena akan shi take mishi kala kalar wulaqanci, ta nayi kamar bashi bane ya kusa jefa rayuwarta cikin halaka, ta manta shi jabir shi ya ceca ta, soayyaya ta rufe mata idanu, bata ganin gaskiya.

Maganganun da ta k'ara yi ne ya jisu tamkar ana jefo mishi garwashin wuta tsabar yarda suke mishi zafi da ciwo a ranshi.

"Me ya saka son zuciyar ka ke san mantar dakai ni matar aure ce jabir, ba abunda zai tab'a shiga tskani na da kai, in har baza ka iya canza wannan banzar d'abiar taka ba ayi zaman mutunci to tun wuri na gaya maka ka fita daga harkata"

Tana gama fad'i taja hannun kamal dan subar gurin, ta tabbata dukan su sun kawa juna mak'ogaro bata san a k'ara maimaita abunda ya faru satin da ya wuce, kamal kamar bazai taka ba dan har lokacin bai bar zuba wa jabir wannan kallon me cike da b'accin rai ba, sai da sakeena ta jawo fuskar shi wurin ta tare da mishi rad'a a kunne da gaya mishi sanyayen kalamai sannan ya dawo dai dai, hannunta ya ruke sukayi wurin mota bayan yayi ma jabir kallon k'arnshe me d'auke da gargad'in da kada ya k'ara ganin fuskar shi.

Shi kuwa jabir kallo ya bisu dashi, me d'auke da tsantsar ciwon kalaman ta da ganin ta tana rayuwa da wani bashi ba, kan ya ankara ji yayi yabi bayan su, cikin murya me rawa, ihu da ciwo da zai baka tabbacin duk iskancin da shed'anancin shi, sakeena daban ce a zuciyar shi.

"Ni kike wulaqan tawa da ci ma mutunci a gaban wannan da ya kusan tozarta ki a idanun duniya??,

Ba wanda ya kula shi a cikin su duka cigaba sukayi da tafiyar su, abun ya k'ara yi ma jabir ciwo, tuni ya saka hannu zai cafko ta, amma kamal ya ruga shi, wani wawan bugu yayi ma k'irjinshi da tuni ya saka ya zube a k'asa, yana ruk'e wurin da yake mishi azaba.

Manyan jajayen idanunshi ya watsa mishi, sannan ya nuna shi da d'an yasta, cikin murya mara was ya fara zuba mishi kashedi.

"Kada ka kuskura na k'ara ganin ka kusa da mata ta dan wallahi bazan d'auka ba, in kana cike da iskanci da rashin mutunci to na fika sai na saka garin abuja yayi maka wuyar zama"

Yana gama fad'i shima ya kama hannunta, remote ya danna ya bud'e motar sannan yayi wurin seat d'inta ya cusa ta a ciki, ya maida k'ofar ta rufe sannan yayi nashi b'angaran, fusgar motar yayi yau gate din su sakeena ya fara danna horn, basu dad'e ba aka bud'e musu ya taka motar ya shige, suka bar jabir zaune a wurin yana kallon motar cikin takaici.

Suna shiga ya samu wuri yayi parking, har lokacin ranshi bai bar k'unar had'uwar shi da jabir ba, shi ya d'auka mutumin arziki ne shi ya saka ya sauka har ya tunkare shi cikin fara'a, amma tunda ya nuna mishi d'an tasha ne shi, to tabbas zai nuna mishi shima dai dai yake dashi, dan in har akan matar shi ne zai iya aikata komi.

Jin haununta yayi akan fuskarshi ta had'e kumatun shi ta dawo da fuksar shi wurin ta, murmushin da ya ga tana yi a take yaji kamar an d'auke mishi duk wani baccin ranshi, tuni shima ya sakar mata nashi murmushin wanda ya saka duka kumatunsa suka lob'a, jin lips d'inta yayi akan nashi tayi pecking a hankali, lumshe idanunshi yayi saboda wani dad'i da sanyi da ya ziyar ce, in har yana tare da ita bazai iya zama cikin b'accin rai ba.

"Ive been wanting to do this"

Tana fad'i ta saki fuskar shi yayin da ta fara shirin fita daga motar, bud'e idanunshi yayi a hankali ta suka fara canza kallar su, yayin da ya jawo ta jikin shi,

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now