Sixty

1.7K 240 56
                                    

Duk wanda ya ganshi d'auke ta ita a hanyar shiga cikin asibitin sai ya bashi wuri, yayin da wasu suyi carko carko su bishi da kallo tare da tausaya mishi wasu su tsaya suna jajantawa, wasu kuma suyi addu'ar Allah ysa rai dai baiyi halin sa, dukda ba wanda kamal ya kalle balle ya kulla, yana isa reception d'in tuni nurses sukayi kanshi yayin da suka k'arbe ta cikin gaggawa suka d'ora ta akan stretcher, yana ganin tabar hannunshi ya zube a wurin saboda yarda k'afafunshi ke a mace.

Yarda ya bisu da kallo ya kasa ko da mosti kwakwara zai baka tabbacin har lokacin baya hankalin shi, domin bai daina jin abun tamkar a mafarki ba, wani nufashi ya cigaba da fitarwa yayin da ya d'ora hannunshi da yayi kaca kaca da jini akan farar fuskar shi, tare da lumshe idanunshi, bayan ya daina hangen su ita da nurses d'in, yanzu ko kukan da yake ya tsaya, ka ganshi tamkar gangar jiki ba rai, jin kwakwarshi yake tna tafasa tsabar yarda alamarin ya mishi yawa, wani sarawar ciwon kai kamar kanshi zata rabe gida biyu, duniyar wata irin juya mishi take, tamkar zarare yake a wurin dan ba kowa bane zaizo ya zauna a k'asa a tsakiyar tafkeken asibiti baya mosti, duk wanda ya wuce shi sai ya tofa albarkacin bakin sa ko kalau yake.

Shi kanshi bai san adadin mintunan daya kwashe zaune a wurin ba, dan yanzu sam sam ba abunda ke zuwa kwakwarshi, ba abunda yake ganewa in banda k'arar bugun zuciyar shi ta yake ji a kunawan shi, da wane irin mahaukacin tsoro da firgice da bazai iya misatltwa ba, sai rad'ad'i zafi, k'una da azaba da zuciyar shi ke mishi tamkar ana soka k'onan k'arfe a cikin ta.

Ko da su abba suka shigo be lura dasu ba, suma ka gansu kasan suna cikin tashin hankali, tsintar shi da sukayi a zaune ya saka ko wannan su ya ci burki barin ma yarda suka ga jikinshi yayi yaga yaga da jini, tuni kwalla ta cika idanun kausar da yake tana da raunaniyar zuciya ba wuya abu ya saka ta kuka, yayin da mami da saki wani salati, da tsugunnawa a kusa da d'an nata, tare da shafo fuskar shi, itama kana gani kasan k'arfin hali take yi kada ta saka kukan, da judith ta kira ta tana tana cewa sakeena ta mutu kasa gasgata zancen tayi, ta zata raina mata hankali take sai da tayi tunanin yaushe ta bata fuska balle har tayi mata wannan wasan sannan, a guje suka fito bayan abba ya kira shehu ya tambayi asibtin da ya kawo su.

Kamal a hankali ya d'ago jajayen idanunshi kamar garwashin wuta ya sauke akan uwar tashi, take mami taji zuciyar ta ta tsinke, tausayin shi ya kamata, yarda yake a wurin kamar gangar jikin shi ce kadai, baya duniyar dan ko kallon mami da yake bakomi d'auke a idanunshi tamakar a mace suke, abba ne yayi karfin hali ya shiga tambayr shi inda sakeenar take, amma ina yayi sararo yana kallonshi tamkar baya gane me yake fad'a, tsoro ne ya fara kama iyayen nashi na kada wannan yayi sanadiyar rasa d'an su a karo na biyu.

A lokacin doctors har guda biyu suka tunkaro su, abba na hangen su yayi hamdala yayin da zuciyar kamal ta k'ara tsananta bugawa, barin ma yarda yaga fuskokin su ba labari, ba abunda yake aiyanawa a ranshi in banda sunzo su gaya mishi bak'in labari, ji yayi zuciyar shi ta fara azalzala tare da win irin ciwo, wani numfashi me zafi ya fara fitarwa yayin da ya k'ank'ame hannun mami da shigewa da kanshi k'irjinta sai kace jariri, domin bayan san jin masifar da zasu fad'a, ka ganshi sai ka mutuk'ar tausaya mishi tuni, kwallar idanun kausar ta mami suka zubo.

Suna isowo suka bama abba hannu cikin girmamawa domin sunsan wane ne shi, sannan wani dagan cikin su yace. "Wanene guardian d'inta?"

Abba ne ya kalli d'an nashi, yaga yarda ya dunk'ule wuri d'aya, baiji yana cikin halin da zai iya sauraron ko wane abu, amma haka dai ya nuna musu shi, tare da cewa shine mijinta, wand yayi maganar ne ya kai idanunshi wurin shi, tuni tausayinsa ya kama shi, a hankali ya matso tare da tsugunnawa a kusa dashi, kamal har lokacin be mosta ba daga wurin mami sai ma k'ara k'ank'ame ta da yayi, doctorn na gani shi a haka yasan yana cikin masifafan shock, aikin shi ya saka yaga mutane ba adadi a irin yanayin nan, wasu shi yake zama sanadiyar tab'in hankalin su, wasu kuma suma suke daga nan baka k'ara cin moriyar su sai dai a kwantar a tayar, wasu zuciyar suce ma ke bugawa su fad'i su mutu, amma baya fatan haka akan wannan, Allah ya sa nashi me sauk'i ne, kuma temporary, ajiyar zuciya yayi sannan a hankali sai kace me yiwa jariri magana yace.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now