seven

1.5K 149 4
                                    

Dukan su suna zaune a makeken parlor dake side d'in abban su da ya dawo daga tafiya, har mami ma tana zaune, Kamal na gefe a zaune yayi shiru kamar yana wani tunanin duk hankalin shi baya kansu, basu damu ba saboda sun san halin shi, magana bata cika damun shi sai in har y'an maganar sunzo kanshi, Kamal d'auke idanun shi yayi daga kallon bangon da suke ya mai dasu kan family d'inshi wanda suke faman dariya kana gani kasan suna jin dad'in hirar da suke, ci gaba yayi da kallon sund'aya bayan d'aya sannan da d'an karfi yadda zai maida hankalin su wurin shi yace,

"Aure zanyi"

Yana maganar ya katse su gaba d'aya daga hirar da suke, kamila da takai tea bakin ta bata san lokacin da ta zubo dashi ba, kausar da ta d'auki apple itama zata kai bakinta tayi mutuwar zaune, mami ta hangame bakinta tabi shi da kallo, shi kuwa abba kallon da yake mishi kallon d'auke da tambaya, gogan naku Kamal yayi kamar bashi ne yayi maganar ba, ya ci gaba da abunda yake wato kallon bango, kausar ce tayi saurin matsowa kusa dashi, ta fara ce mishi,

"Ya Kamal are you okay?"

Kamal da yake jingine da jikin kujera ya saki dariya, sannan ya k'ara bin y'an gidan nasu da kallo, d'agowa yayi daga kan kujerar sannan ya tattaru nustuwar shi ya maida ta kan Abba da Mami,

"Da gaske nake aure nake son nayi"

Shiru wurin yayi ba abunda kake ji sai k'arar tv, an dad'e a haka ba wanda yace wa kowa komi, shi kuwa abun mamaki ya bama Kamal, yarda sukayi a wurin kamar bai isa yin aure ba, sai can mami ta kalli kausar da kamila tace musu su basu wuri, suna fita daga d'akin ta maida hankalin ta kan tilon d'anta,

"Aure fa kace Kamal, ko sati d'aya da ya wuce da nayi maka maganar aure nuna mun kayi baka san maganar, ta ya akayi yanzu kan canza zancen ka?"

A hankali mami tayi mishi tambayar amma fuskar ta bata d'auke da wasa, Kamal gyaran murya yayi,

"A lokacin da kikayi mun maganar ba wata wacce naji ta kwanta mun a rai, sai da na dawo k'asar nan nagan ta naji gaskiya tayi mun kuma ina so in aure ta"

Duk zancen da suke abba bai ce komi ba sai dai binsu da kallo da yayi, mami ce ta k'ara kallon shi irin kallon tuhuma d'innan,

"dawowar ka kwana hud'u kenan amma har kaji kana son yarinyar har takai da kana san ka aure ta?"

Mami ta san halin d'an nata kamar yunwar cikin ta, tasan yarda mata basa gaban shi, aure bai tab'a damun shi amma ya canza ra'ayin shi da ya dage akai shekarar da shekaru a cikin kawai kwana hud'u akwai alamar tambaya, shi kuwa Kamal d'aga kai yayi sannan ya fara musu bayannan ita y'ar gidan wace, iyayen nashi sunyi shiru suna sauraron shi sai da ya gama tsab, Abba ajiyar zuciya yayi,

"In har y'ar gidan sunusi zubair ce to abu yazo da sauki, dan mutumi na ne, muna shiri sosai dashi, zanje na same shi nayi mishi magana, nasan ba zai k'i zancen ba"

Wani dad'i ne ya rufe Kamal, zai same ta cikin sauk'i kenan, jin zuciyar shi yayi tayi fari, wani irin farin ciki ya mamaye shi, muryar mami ce ta dawo dashi daga duniyar da yake,

"Gaskiya Alhj ban yarda da wannan abu ba, in ita yarinyar bata so fa?, ni a gani nan yaje wurin ta su fara sasan tawa tukun, in har yayi mata to, sai a fara shirin biki in har baiyi mata ba sai yaje ya sami wata, yanzu ai an daina auran had'i"

Ji yayi wuta ta d'auke mishi, bayan wani abu da ya taho ya tsaya mishi a mak'ogarun shi, kada fa mami ta ruguza mishi shirin shi, ya bud'e baki zai k'ara tsaro wata k'aryar dan ya tsara uwar tashi abba ya riga shi,

"Iyayen mu da kakannin mu auren had'i akayi musu sun mutu?

Mai da kallon shi yayi kan Kamal sannan ya nuna shi ta d'an yatsa tare da cewa,

"Ko kina so kice mun d'an naki na da mugun hali shi ya saka bakya san yayi aure?, ni banga aibin abun ba dan ba bare zai aura ba, y'ar abokina ce,"

Wani farin ciki ne ya sake rufe Kamal, yaji dad'i da abba ya nuna yana bayan shi, mami shiru tayi a wurin da taga ran mijin nata nason ya b'acci, bata k'ara cewa komi ba, shi kuwa kamal gode wa Allah ya shiga yi a zuci, mik'ewa yayi ya ma iyayen nashi sallama bayan abba ya gaya mishi gobe zai je ya sami sunusi zubair d'in su tatauna, duk abunda yace zai ji daga gare shi, haka Kamal ya fita daga parlor d'in zuciyar shi d'auke da nishad'i dan jin dad'i.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now