Five

2K 167 10
                                    

Zuciyar shi wata irin tafasa take yi, gaba d'aya ranshi a b'ace, wani irin sharara mugun gudu yake a titi kamar wanda zai tashi sama, ga yayi ma steering wheel d'in motar tashi mugun kamu sai kace wuyan Sakeenar ya kama, tsanar ta da yake ta sake nin nin kuwa, wani irin danasanin fita wurin ta yake dan yanzu ta saka mishi mugun k'unar rai,

"Dan bata da kunya bata da mutunci har ta isa sunan shi ya fito daga bakin ta?,"

Kamal ya fad'i a zuci bayan k'ara taka motar shi da yayi, yanzu zuciyar shi ta k'ara azal zala, wani irin takai ci da haushi yake ji, a haka har yazo gidan su Imran, horn ya dunk'a zubawa ba tsayawa securities d'in gidan a guje suka fito bud'e mishi gate, ana wangale gate d'in ya saka hancin motar shi ya shiga, ya so yayi zaman gida yau d'innan amma a ganin shi in har ya zauna tunani zasu kashe shi barin ma yanzu da ya ganta, samun wuri yayi yai parking motar tare da lumshe idanunshi, dama be biye wa zuciyar shi ba yaje inda take, bai tab'a ganinta ba sai yau, dana sanin saka ta a idanunshi yake, da kyar ya iya tattaro nustuwar shi ya fito daga cikin motar.

A hankali ya fara takawa har ya isa side d'in Imran, bai gaya mishi zai zo ba Allah dai ya saka yana nan, bai k'arasa tunanin shi ba sai gashi ya hango shi ta window parlor d'inshi a zaune yana kallo, wata hamdala yayi, tun kan ya k'arasa yagan Imran  ya bud'e mishi k'ofa, wato shima ya hango shi kenan, Kamal na isa inda yake ya mik'a mishi hannun suka fara gaisawa har suka isa cikin parlor d'in, samun wuri sukayi suka zauna,

Tunda Kamal ya zauna yayi shiru, kana ganinshi kasan tunani yake me zurfi, Imran shi kuwa ya bishi da kallo, yasan zuwan nan nashi ba lafiya bane, kuma yaga yadda gaba d'aya fuskar shi ta had'e ya canza kamar yana fushi da wani, haka ya k'ura ma Kamal da ke faman kallon carpet ido, can da ya gaji ya fara tambayar shi,

"Lafiya kuwa? Naga tunda ka shigo kayi shiru kana ta kallon carpet"

Yana yin maganar Kamal yayi saurin d'agowa ya kalle shi, sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin shi, shiru yayi bai bama imran amsa ba, ji yayi yana san tambayar shi wani muhimmin abu, amma kuma baya son  a tuno mishi abun da baya so ya tuna, kai zuciyar shi nesa yayi, sannan ya d'an matso daga jikin kujerar ya maida hankalin shi gaba d'aya kan imran ya fara fad'in,

"Da ni da..."

Shiru ya k'ara yi ya dakatar da zancen shi, kallon hannunshi yake da suke sark'e a cikin juna, yin maganar wuya take bashi, yin wata ajiyar zuciya yayi sannan ya maida idanunshi kan imran,

"Da ni da KAMIL da wa kafi kusa?"

Yarda yayi maganar a sanyaye kamar kwai ya fashe mishi a ciki, ko ambatan sunanshi da yayi zuciyar shi wani irin zafi take mishi, kwata kwata baya san ya tuna dashi a rayuwar shi saboda yana saka zuciyar shi mugun rad'ad'i, ta b'angaran imran kuwa abun mamaki ya bashi, yau Kamal ne ya ambaci KAMIL, gaskiya duk abunda ke damun shi ba d'an k'aramin abu bane, shima kallan abokin nashi yayi ya fara bashi amsa,

"Duka ku biyun mana, ba wanda zance nafi kusa dashi dan dukan ku nasan ku cikin ku da wajan ku har siri kan ku na sani"

Gyad'a kanshi Kamal yayi, kenan tambayar da zai mishi zai sami amsar shi cikin sauk'i,

"Tunda kace kasan siri kan mu, kasan budurwar shi Sakeena?"

Imran d'aga kanshi yayi sannan ya fara jawabin shi,

"Na santa, ba sun had'u bane da yaje masters d'inshi turkey? Ita kuma tana Shekarar farko, tunda ya ganta ya fara santa, kamar love at first sight ne, gaba d'aya zaman shi a can binta ya dunk'a yi dan ta k'arbi soyayyar shi amma bata fara kula shi ba sai dab da zai dawo Nigeria, a lokacin suka fara soyyaya me k'arfi, in har zaka tuna yak'i dawowa ma ko bayan ya gama masters d'inshi, sai da Abba yayi mishi jan idanu"

Imran na gama zancen shi ya k'ara maida nustuwar shi kan abokin nashi, wanda yayi tsit a wurin, kallon Imran yake amma ya k'ara canza wa, kana ganin shi kasan akwai tsantsar damuwa a tare dashi, tunda Imran yake a rayuwar shi bai tab'a ganin y'an biyu wanda sukayi mutuk'ar shak'uwa, bayan san junan su da san farin cikin juna kamar KAMAL da KAMIL ba,

"Nasan kaima kasan zancen nan saboda duk duniya ba wanda KAMIL ya yarda dashi kamar ka, me ya saka ka tambaye ni?"

Kamal mai da kallon shi yayi jikin bangon d'akin ya k'ura mai ido, abunda ya saka ya tambaye shi ba komi bane kawai so yake yaji ko labarin da suka sani iri d'aya ne, k'ara maida hankalin shi kan abokin shi yayi wanda shima d'in shi yake kallo,

"Ka tab'a ganin ta ido da ido?"

Imran girgiza kanshi yayi, "a'a, ban tab'a ganinta ba, amma dai nasan ba'a wurin iyayenta take ba dan sun rasu, kawunta ne ke ruk'eta SUNSUSI ZUBAIR, wannan dan kwangilar, nasan kasan shi dan a k'asar nan ba wanda bai sanshi ba,

Dakatar da kanshi yayi daga bayanin da yake ma abokin shi, yasan Kamal ya sani saboda ya tabbata Kamil ya fad'a mishi kumi dan basa boy'ewa juna abu, shima yima abokin tashi tambayar ne"

"Kai baka tab'a ganinta bane?"

D'aga mishi kai Kamal yayi, sanyi ya bud'e bakin shi a hankali ya fara magana,

"Ban tab'a ganinta ba, lokacin da yake turkey ina da wannan chorionic ulcer d'in, Mami da Abba basa bari na nayi nesa dasu, kawai dai yana bani labarin ta duk lokacin da mukai waya"

Imran dai baisan me ya saka Kamal yake ambatar budurwa Kamil ba dan wannan tsohon zance ne, so yake ya tambaye shi me ya saka yake mishi tambayoyin nan amma yana jin tsoro, a cikin y'an biyu Kamil yafi sauk'in kai da san mutane da shiga cikin su, shi kuwa Kamal opposite d'inshi ne, duk abun hayaniya da jama'a baya san su, gashi da wani irin taurin kai da miskilanci, halin su yasha bam bam ga dai su identical twins, shi ya saka mutane da yawa ba su san Kamal ba, sunfi sanin Kamil saboda shi me jama'a ne, in har ba gaya maka akai ba baza ka tab'a sanin Kamil y'an biyu bane, saboda ko makarantar da sukayi daban ne, Kamil boarding shi kuwa Kamal day, harta university d'insu wuri daban daban sukayi, Kamil yayi degree d'inshi a Dubai, masters d'inshi a turkey shi kuwa Kamal gaba d'aya karartun shi a Nigeria yayi,

K'ara kallon abokin shi yayi da yake faman kallon carpet, ko mene a ciki ranshi haka oho, gani yayi yai zumbur ya mik'e,

"Ni bari na wuce, ka gaishe mun da Ammi kace zan dawo takanas kawai dan ita"

Dariya abokin nashi ya saki, tare da tashi daga zaman da yake yayi wurin abokin nashi, d'ora hannun shi yayi akan kafad'ar Kamal,

"In har Ammi ce kunfi kusa, amma zan sanar mata da sakwan ka"

Kamal murmushi yayi, haka sukayi ta zancen su har suka isa inda motar Kamal yake, nan sukayi sallama ya shiga shima Imran yace ya gaishe mishi da Mami, ana bud'e mishi gate ya fita daga cikin gidan a guje, zuciyar shi tayi fari yanzu dan ya gano yarda zai b'ullo wa alamarin, yayi akwarin sai ya mai da rayuwarta abun tausayi bayan ya ruguza mata farin cikin ta.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now