Thirty

1.8K 178 45
                                    

Tana tafiya tana sauri, tare da zagin kamal a k'asan ranta, har ta ga wata nurse na tahowa, sakeena ta sauri ta k'arsa wurin ta, sannanta tambaye ta wane restaurant ne a kusa bayan sun gaisa, dan ita ba y'ar kano bace, bata san ko ina ba, da kyar ma ta iya kawo kamal asibitin nan, haka nurse d'in ta mata kwatanci, itama mik'a godiyar ta tayi sannan tayi hanyar fita daga asibitin.


Tura k'ofar d'akin shi tayi had'e da sallama, ta ganshi a zaune akan abun sallah, a nistse yake a wurin gaba d'aya nustuwar shi tana kan addu'o in da yake, yaso ya bama sakeena mamaki dan yauce rana ta farko ta tab'a ganin shi yana ibada, ajiye ledojin hannunta tayi akan wani table a gefe, sannan ta sami wuri ta zauna akan kujera tare da zubawa k'eyar kamal kallo.

Daman mugayen maza irin su kamal, way'anda basu san darajar mace ba sun san Allah, ai ita ta d'auka iskancin sa ya saka a gaba, ita tasan da yawon maza ba san addini suke ba, ganin shi a haka ya d'an daure mata kai, haka ta zauna tana sak'e sak'enta har ya idar da abunda yake.


Yana shafa addu'ar shi ya juyo ya sauke mata wannan murmushin nashi me mugun k'ra mishi kyau wanda duka dimples d'inshi sai da suka fito, d'auke idanunta tayi daga kanshi, kamar ba ita ke binshi da kallo ba sannan ta mik'e, ta koma wajan table d'in ta fara bud'e ledar.

"Tunda kace bana baka abinci, ga abinci naje na siyo maka"

Tana maganar tana bud'e takeaway pack d'in, ta dauko takeway d'in da yake d'auke da sauce d'in shredded chicken kenan ta bud'e shi shima, daga sama taji ance,

"Abincin ki nake san ci"

Tsabar bata zata zai zo dab da ita ba ya mata magana kamar rad'a a kunnen ta, ga numfashin shi da ya baibaye wuyan ta, bata san lokacin sa ta juyo ta saki gaba d'aya sauce d'in mai turirin zafi ba a jikin shi.

Sakeena na gani abinda tayi, tai saurin kai hannunta bakinta ta kulle, tare da zaro manyan idanunta waje, tunda ga kan cikin shi har k'asan shi ya b'aci da sauce, da sauri ta maida idanunta kan kamal wanda yake cizan leb'e tsbaar azaba, da sauri ta juya ta lalumo tissue, ta koma kanshi.

Shirt d'inshi ta d'aga, ta fara goge kan cikin shi, farar fatar wurin tayi jaa saboda zafin abunda ya zubar mishi, gaba d'ayanta a rud'e take, bakinta ba abunda yake ambata sai kalmar haku'ri, a haka da dage tana goge mishi jiki, har ta k'arso kasan shi wurin zip d'in wandon shi, fara goge wurin tayi tana dirza, can kuma da ta gane mi take tayi saurin tsayawa, a hankali ta d'ago da idanunta, suka had'a ido.


Hannunshi na nannad'e akan k'irjinshi, fuskar shi d'auke da murmushin nana nashi, ga ya kafa ta da mayun manyan idanun nan nashi da sunyi ja ja wur, kwyar idanunshi d'auke da wani abun da bata san ko mene ba, d'aga mata gira yayi, sannan a hankali yace,

"Go on, cigaba da abunda kike"

Wani irin abu taji ya taho mata, da sauri ta juya bayanta, wata kunya ce ta kama ta, Allah ya had'a ta da d'an rainin wayo, me ma ya saka ta fara goge mishi jiki bayan ba laifin ta bane shi ne yazo bayan ta yayi mata magana duk ya tsorata ta.

K'ara jin numfashin shi tayi akan wuyanta, a hankali ya fara magana da wannan deep voice d'in tashi, bayan ya ruk'o hannayen ta tare da had'a bayanta da k'irjin shi, a kan kunnanta yace,

"Yanzu ya zakiyi da kayan jikina? bani da wasu kayan"

Wani abu tsi taji ya harba tsakiya kanta, a dar'i tayi saurin matsawa, tare da juyawa da sauke mishi idanunta wanda yanzu suna d'auke da b'accin rai, yana tsaye a wurin, he looks calm and collected, sai ka rantse da Allah bashi yayi mata abunda yayi mata ba yanzun nan,

Haka suka tsaya suna kallon juna, sakeena da idanunta basa d'auke da komi sai baccin rai da haushin shi, kamal kuwa idanunshi d'auke da abubuwan da ta kasa reading, duk yarda take san sanin me yake tunani a lokacin ta kasa, sai da ya gama k'are mata kallo sannan yayi murmushin shi na gefan baki, ya koma hanyar gadon shi, sakeena hangame baki tayi tana kallan shi, sau nawa tayi warning d'inshi na ya daina shigar mata personal space d'inta,

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now