Thirty seven

1.5K 156 37
                                    

Yafi minti talatin yana abu d'aya, sakeena da ummeeta sunyi shiru sunbi k'ofar da kallo, can sai suka ji shiru, an d'anyi minti biyar a haka sannan kuma suka fara jin horn d'inshi, horn yake danna wa ba sasauci kana ji kasan ba lafiya ba, be dad'e ba aka bud'e mishi gate suka ji ya taka motar ya fita a guje, sakeena najin haka tayi wata muguwar ajiyar zuciya tare da zubewa a k'asa da kama k'irjinta, tana maida numfashi d'aya bayan d'aya.

Duk abinda take a idanun ummeeta dan ta kasa gane me ya saka duk tabi ta rud'e, dan ita tasan ko da zai fasa k'ofar bazai tab'a yi ma sakeena wani abu ba sai dai ma ita zaiyi wa cin mutunci.

"Haka kike jin tsoron shi daman?"

Ummeeta tayi mata tambayar da take tunani, itama dan ita ce, da wani yayi wa abunda yai mata yanzu da ta tsula fitsari tare da had'a kwarmatsan da ta barin gidan dan saboda tsoro, amma sai ita ce, wacce ta kile a cikin barikanci, ba irin namijin da bata gani ba, maza basa bata tsoro.

"Ba tsoron shi nake ji ba, tsoron zuciyar shi nake"

A hankali sakeena ta amsa ta, har lokacin tana maida numfashi, bata manta halin da kamal ya cilla ta ba saboda zuciya da tsana, bata manta irin wulaqancin da yayi mata ba, tasan abunda zai iya aikatwa cikin b'accin rai, a hankali ta mik'e tare da yi ma ummeeta sai da safe, sannan ta wuce ta shiga d'aya side d'in, tana jin kwayar idanun ummeeta akan ta.

Tana shiga d'aki ta fad'a kan gado, tare da lumshe idanunta, ba abunda take tunanini irin halin da zata shiga in har kamal ya dawo gidan, wannan karan anya bata wuce gona da iri ba kuwa?? Ta dad'e bata ga irin b'accin ran da ya nuna ba yau, bayan ummeeta ta harzuk'a shi ita kuwa tazo ta k'ar d'ora nata akai, addu'a ta shiga yi Allah ubangiji ya kawo mata karshen auran shi ta huta da jaraba a haka har bacci yayi gaba da ita.

--------------

Kamal na kwance akan makeken gadon shi na hotel, idanunshi a lumshe, dantsan hannunshi nakan fuskar shi, in ka ganshi zaka zata bacci yake amma sam sam, ba abunda ya had'a shi da bacci dan ya manta rabon daya rintsa, ciwon kai ne me azaba ke d'awainiya dashi ba abinda kwakwalwar shi ke so irin hutu amma ya kasa bata abinda take so, saboda kwata kwata yanzu bashi da kwanciyar hankali.

K'ara gyra kwanciyar shi yayi tare da bud'e idanunshi a hankali da saukewa akan mirror d'in gabanshi, shi kanshi yasan ya canza, ya rame, ya fita daga hayyacin shi, ba komi ya haddasa mishi ba sai rashin sa matar shi da baiyi a ido ba na tsawan sati uku.

Yai alk'warin fita daga harkarta tunda ta nuna maganar shi ba komi bace a wurin ta, tunda ta nuna mishi shi bakowa bane, tunda kuma ta zab'i zaman karuwai a gidan shi akan abinda yace mata, abin ba k'aramin ciwo yayi mishi ba, shi ya saka yayi alkwarin nisanta kanshi daga ita, amma kuwa rashin sata a idunshi na nema ya illata shi, dan yanzu kwata kwata baya samun sukuni, masifar so yake ya ganta amma Allah ya sani bazai iya zuwa gidan shi ba dan ba abunda ya tsana a yanzu irin ganin wanan y'ar iskar dan in har iske ta a gidan to zaiyi mata dukan da sai tayi muguwar jinya a asibiti, ko me tsanar dukan macce da yake daga kanta zai fara.

"Me ya saka kika san kawo fitina cikin auran mu?"

A hankali, a sanyaye yayi tambayar, kana ji kasan sakeena yake yi wa dukda bata wurin, k'ara lumshe jajayen idanunshi yayi da yaji wani abu ya taho mishi ya tsaya mishi a zuciya, a hankali ya saka hannu ya dafe k'rjinshi wai ko zai daina jin abun da yake ji.

---------------

Duk suna zaune a parlor, sakeena cikin wata navy blue doguwar riga ta material, kayan kana ganinsu kasan sunsha kud'i, kai ba d'ankwali gashin ta me kyau na kwance cikin ribbon, ummeeta na cikin riga da wando wanda sun d'ame jikinta tsam, ga rigar sleeveless, sakeena da daina mamakin shigar ta dan har ta saba, yau ma dan anyi shigar arziki, sarah ma yau tazo dan kwana take yanzu a gidan.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now