Twenty two

1.6K 167 17
                                    

Duk yarda take so ta daina shiga harkarshi bata iyawa, duk lokacin data ganshi wata irin tafasa zuciyar ta take, kan tayi tunanin kulle bakinta ta maida mashi da murtani, ko yanzu da ya d'aga ta cak akan kafad'arshi bakin ta yak'i ya daina shiru, duk maganganun da take yayi banza da ita sai tafiyar shi yake abunshi, sakeena k'ara saka hannun tayi ta ja mishi gashi da kai mishi duka wai duk dan ya sauke ta, amma ina yak'i ajiye ta har sai da suka shiga wani d'aki da yake a wajen gidan sannan ya dire ta, d'akin kamar store ne, dan taga kwalayen tv, washing machine, microwave, dishwasher, da dai sauran su, tana gama k'arewa d'akin kallo ta juyo ta sauke idanunta akan shi, da suka had'a ido sai da gabanta ya fad'i, fuskar shi ba annuri ko na d'igo d'aya, gaba d'aya kamaninshi sun canza, tsoro ne ya kama, tayi saurin ja baya dan fargabar kada yayi mata wani abu, kamal jajayen idanunshi ya saka akanta ta baya ko k'ifta su, duk da sakeena a tsorace take, haka ta dake ta kawar ta tsoranta gefe ta kalle shi cikin idanunshi, ta fara cewa,

"In ka cigaba da mun irin wannan wulaqanci kamal wallahi zan yi sanadi..."

"SANADIYAR ME??, ME ZAKI IYA YI MUN??"

Kan ta k'rasa zancen ta ya daka mata wata gigitaciyar tsawa da ta saka sakin toshe kunnuwanta da kanta, tare da saurin zubewa a k'asa, dan ya bala'in tsorata ta, a tunaninta kai mata duka zaiyi, barin ma yarda taga gaba d'aya kamun nunshi su canza, farar fusar shi ta koma jaa, ga sai huci yake, kamar wani zaki, haka tayi shiru a tsugunne tana jiran duka kawai sai jinshi tayi yace,

"ki zauna a d'akinan ba abinci, ba ruwa, har sai wannan kan naki ya gane mai damun magana ba inda zai kaiki sai dai ma k'ara miki wahala"

Yarda yayi maganar ya saka jikinta fara rawa, ga yana maganar ya juya ya fita ko kallanta bai k'ara yi ba, sakeena tsabar shock da tsoro ta kasa mosti, har lokacin jikinta rawa yake, tsawa ya daka mata kawai amma gaba d'aya ya rikita ta, wannan wana irin namiji ne, gaskiya tana cikin wahala, ta shiga uku, k'arar muk'ullin da taji ne ya dawo da ita daga duniyar da take, ta mahaukacin sauri ta mik'e tayi hanyar k'ofar tana bugawa dan ya bud'e, haka yayi kunnane shegu da ita ya koma cikin gidan, sakeena kuwa tai ta faman buga k'ofa har ta gaji, ta samu wuri ta zauna a k'asan d'akin tayi shiru, ta zuba ma bango d'akin ido, a haka har aka fara kiran sallar la'asar, tana ji mai gadi ya bud'e mishi gate ya fita masallaci, sakeena saka kanta tayi akan cinyoyinta tayi shiru, tsabar takai ci tama kasa kuka, dan tagane komai kukan da zatai kamal bazai tab'a tausaya mata ba, saboda zuciyar shi a kyankyashe take, kamar dutse take, bashi da imani ko da na sakwan d'aya, ya saka an dawo da ita gidan shi dan kawai ya cigaba da wulaqanta ta, da ya barta acan da jabir ya cece ta, ta fita daga hannunshi, wani irin bak'in ciki ne ya k'ara rufeta, ta fara niyar tashi tayi salla la'asar tunda tana da alwala, kawai sai jin period d'inta tayi, hankalinta ne ya k'ara tashi, da ta tuna a yanayin da take, ga ba toilet ko wani abu d'akin, k'ara kank'ame jikinta tayi kwalla ta cika idanunta, wai ita yau ake wa wannan irin cin mutunci, da gatan ta da komi ya kama ya kulle ta a d'aki kamar wata prisoner , lallai kamal bak'in mugun ne,

A haka tana zaune ita kad'ai cikin duhu, dan ta nemi switch d'in fitila ta rasa, ga zafin gari ya rufe d'akin dan ba ko fanka, yanzu ta fara jin k'ishin ruwa dan da ta ci abinci d'azu bata sha ruwa ba, tana ji ya fita a mota bayan ya dawo daga masallaci, har yanzu bai dawo ba, d'azu ta tashi ta lek'a ta window tana kwalla ma mai gadin gidan kira dan yazo ya taimaketa amma ina, ko yaji ta ko baiji ba bama ta sani ba dan ko kallan d'akin baiyi ba, haka ta koma ta zauna tare da zubawa sarautar Allah ido, ta cigaba da zama ita kad'ai cikin duhu, har taji k'aran gate alamun kamal ya dawo, da sauri ta mik'e ta l'eka window, dan a zatan ta zai bud'e mata k'ofa sai gani tayi yayi cikin gidan, ko kallon inda dake baiyi ba, wata tsinuwar sakeena ta k'ara mishi sannan ta samu wuri ta zuana.

Kwanan zaune tayi yanzu rana ta fito sosai bata ji d'uriyar kamal ba tun da daddare da ya shiga gidan, Allah ya taimake ta period d'inta kad'an yake zuwa bata b'ata jikinta ba sosai, k'ishin ruwa ta fara addabar ta, har ta fara zama weak, tana kwance dai dai saitin k'ofa, tana jiran ikon Allah, sai dai ta kulle idanunta tayi bacci ta farka ba abunda take iya yi, har duhu ya fara, yanzu bama ta iya d'aga koda d'an yatsan ta saboda tsabar kishin ruwa, gaba d'aya ta zama dehydrated, yarda take jinta bata da wani k'arfi, daman lafiya bata gama isarta ba, har ta k'addarawa kanta mutuwar ta tazo, a haka ta cigaba da kwanciya har dare yayi sosai, ta tabbata ta kusa awa 30 a d'akin in ma bata fi ba, yanzu har numfasin ta ya fara sama, hawaye ma sun kasa zuba saboda ba ruwa a jikinta, ko bud'e idanunta ta kasa yi, sakeena ta barwa Allah komi ta cigaba da kwanciyar ta tana addu'a dukda da kyar take samu tayi,

ZAFIN RABO ✔️Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora