Forty one

2.2K 164 37
                                    

Tunda suka sauka a garin kano ba wanda ya cewa kowa komi, kana ganin tunani ne da dama ya cika kan abba, shi kuwa imran da ya rako shin dan ganin in har be biyo shi ba to za'a iya smaun matsala barin ma yarda abba yake in rai ya b'aci, addu'a yake yi ma kamal a k'asan ranshi na Allah yasa duk abunda suka ji k'arya ne.

Driver d'in jibgegiyar Range Rover ne ya fara horn a lokacin da suke iso gidan kamal d'in, imran k'ara sacan kallon abba yayi yage ya k'ara had'e rai ba alamar wasa a fuskar shi, shi da bashi ne kamal ba sai da ya tsure.

Me gadin gadin gidan ne ya fito da sauri ya lek'o, yana ganin motar be tsaya tambaya ba kawai ya bud'e dan ya tabbata ba k'aramin mutum bane, a hanakli suka cusa kan motar suka shige, imran na gani motar kamal a pake gabanshi ya fad'i, shi kuwa abba ko tsayawa baiyi ba motar ta tsaye ya bud'e ya fito.

Direct wurin k'ofar shiga yayi ya fara knocking, sai dai shiru ba'a bud'e ba, danna doorbell ya k'ara yi shima shiru, juyawa yayi ya fara tambayar malam isyaku da yake tsaye a wuri d'aya tun bayan kulle gate d'in da yayi.

"Basa ciki ne??"

"Suna nan dan yau ba wanda ya fita a cikin su"

Cikin ladabi yake maganar, dan daga ganin mutumin yaga suna kama da me gidan shi, ba tantama sun had'a dangi, kada yaje yayi wani abun a kore shi daga aiki danshi kam ba k'aramin samu yake da aikin gadin nan ba ga Allah ya had'a shi da me gida d'an albarka me sakar mishi.

"Ko zaku bi ta kitchen naga busu ciki kullewa ba"

Be gama maganar ba, abba ya fara takawa, ganin haka malam isyaku yayi saurin yin gaba dan yi musu jagora, imran ma na bayan su yayi shiru yana ta sak'e sak'e a ranshi, sai da suka iso k'ofar kitchen d'in mallam isyaku ya bud'e sai ga k'ofa ta bud'u.

Abba baiyi wata wata ba kawai ya fad'a ciki, bayan ya wuce kitchen d'in ya shige cikin parlon, sallam ya fara dokawa, amma shiru ba wanda ya amsa, yafi minti biyu yana abu d'aya abun har ya fara bama abba mamaki na ance suna nan amma ga ba alamar suna gidan.

Imran na gefe har lokacin bai ce komi ba, har a lokacin jinshi yake dabam ga tsoron da yaje jiyewa kamal fal cikin shi, shi ya fara jin kamar ana amsa sallama daga cikin d'akin gaban su, hankali shi ne ya karkata kan d'akin yayin da a dai dai lokacin yaga an murd'a handle d'in, jira yake yaga an fito sai yaga shiru, k'ara murd'a handle d'in amma still k'ofar bata bud'e ba, sai a lokacin ya gane k'ofar nada matsala.

"Abba ina ji suna nan, dan gashi kamar ana son bud'e k'ofar nan"

Yana fad'a yayi wurin k'ofar, yayin da shima abba ya maida hankalin shi wurin, yasa hannu dan danna handle d'in kawai suka ga k'ofar ta bud'e.

Carko carko sukayi suna kallon juna, idanunta d'auke da ragowar bacci daga gani baccin da tayi be gamar isar ta ba, ga tsoro ya fara bayyana a fuskar ta, tana sanye cikin bubun da ta saka d'azu da mayafi Allah ya taimaka hannun kayan dogo ne, tsoro sosai ya bayyana a fuskar ta amma imran baiyi mamaki ba dan yasan abun akwai tsoro kiga kawai namijin da biki sani ba a cikin gidan ki,  a hankali ta maida idanunta kan abba, tana ganin abba kuma mamaki ya dawo kan fuskar ta, da sauri ta zube tare da fara mik'a gaisuwar ta.

————————————

Tun jin doorbell d'in da ummeeta tayi hankalin ta ya tashi, badan komi ba dan kada kamal ya tashi, a tsorace tayi saurin rarumo rigar ta da ta cire tayi ta maida jikinta, mai da idanunta tayi kan kamal taga har lokacin bacci yake me nauyi, wata ajiyar zuciya ta yi.

Amma tana jin maganar bak'i a waje ta k'ara shiga wani sabon rud'un, duk ka ganta ta rikice, tsoron kada asirin ta ya tonu ga bata aikta abunda boko ya bada umarni tayi ba, dan tasan in har kamal ya tashi yaji abunda tayi to wallahi sai na lahira yafi ta jin dad'i.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now