Eleven

1.5K 140 2
                                    

Duk jikinta ba ya mata wani dad'i tun jiya bayan ta gane wa zata aura, jinta take yi daban, ba abunda bata sak'awa a ranta yanzu da take zaman jiran daddy ya dawo daga tafiyar da yayi, zuciyar ta ba abunda bata ce mata ba, har guduwa tace tayi amma ina baza ta iya ba, tana da hanyar da zata iya komawa wurin dangin mamanta amma in har ta gudu tabar gidan ba tama daddy adalci ba a ganinta,

"Ke adalci yayi miki da zai miki auran dole"

Wani b'ari na zuciyar ta ta fad'i, Sakeena saurin girgiza kanta tayi tare da kawar da tunanin da sauri, tana cikin wannan taji an tab'a ta, tana maida idanunta wurin taga wata k'anwar mommy ce me suna Maryam a tsaye, Maryam d'in ta girmeta amma ba sosai ba, kuma ba laifi suna shiri, tama fi shiri da ita akan shaheeda, duk da akwai aminci tsakanin su bata ji dad'in ganinta a wurin ba, dan tana so ta kad'ai ce ita d'aya dan hayaniya bak'i ce da suka cika gidan ya dameta shi ya saka ta fito garden d'in gidan dan Shan iska da samu ta tattro nustuwar ta,

"Ke kad'ai a zaune tun d'azu ba ko y'an hira"

Maryam tayi mata magana tare da samun wuri ta zauna a kujerar kusa da Sakeena, murmushin yak'e tayi bayan ta maida kallonta kan yatsun hannunta, har lokacin tana jin idanun maryam d'in akan ta,

"Kinga yarda kika rame a yini d'aya kawai, yaushe rabon da kikai wani abu bakin ki?"

Bata amsa ta ba, dan rabon ta da abinci tun jiya da rana, ga yanzu la'asar ta gaba to, kwata kwata bata jin cin wani abu, haka suka zauna ba wanda ya k'ara ce wa kowa komi sai can, maryam ta k'ara cewa,

"Kinsan daddy ya shigo gidan nan tun d'azu"

Da wani irin sauri sakeena ta mik'e har tana jin jiri, ita kuwa maryam binta tayi da kallo,

"Me ya saka baki gaya mun ba tun d'azu"

Tana maganar tayi hanyar cikin gida tana banka wani sauri, maryam ma binta tayi, sakeena direct side d'in daddy tayi, tana kuwa shiga ta tarar da mommy a bakin k'ofa tana shirin fitowa,

"Yauwa dama ke zan tafi nema, kawun ki yace in kira ki"

Wani irin fad'uwa gaban ta yayi, jikinta ya fara rawa, ta kasa mosti, bama tasan lokacin da mommy da matso dab da ita ba sai da taji hanayen ta akan k'afad'arta,

"Ki nustu, in kin shiga wurin shi ki tabbata kin gaya mishi duk abunda ke ranki, kada ki saki ki b'oye mishi komi, nayi mishi magana duk da bai dad'e da dawo wa ba na tabbata zai fi so yaji sauran bayanin daga wurin ki"

A hankali tayi mata maganar, ita kuwa sakeena kanta na k'asa ga idanunta sun cika taf da kwalla, mommy ce ta saka hannuta ta d'aga hab'ar ta yarda zata kalle ta,

"Ba wanda yake sonki duk duniyar nan sama da kawun ki, dukda yana ta tsawri amma nasan zai ji kukan ki ya canza shawarar nan tashi tunda kin nuna bakya so"

Wani sanyi taji a ranta dukda jikinta bai bar rawa kuma zuciyar ta bata bar bugawa ba, mommy na tafiya daga wurin tayi ajiyar zuciya tare da tura k'ofar parlor had'e da sallama da addu'a a ranta.

--------

Daddy ta tarar a zaune akan wata makekiyar kujera, tunda ta shigo idanun shi na kanta har ta samu wuri ta zauna, shiru tayi ta kasa cewa komi tsabar tsoro da fargabar da take ji, sun dad'e a haka ta kasa bud'e bakin ta tayi magana, shi kuwa da ya gaji da zaman shiru ya fara cewa,

"Ina dawo wa aka sanar dani kina da wani muhimmin abu da zaki gaya mun, ki fara baya ni ina sauraron ki"

K'ara jin wani fad'uwar gaban tayi, a haka ta dake ta fara mishi magana a hankali, kan ta gama baya ni fuskar ta ta jik'e sharkaf da hawaye, bayan rawar da muryar ta take, daddy yayi shiru a wurin yana sauraron ta, ga kallo da yake binta dashi, sai da ta gama tsab sannan ya fara cewa,

"Duk wannan bayani da kika mun baki gaya mun dalilin da bakya son ki aure shi ba"

Ta ina zata fara mishi bayani, ta ina za ta fara gaya mishi twin d'in tsohon saurayin ta ne wanda taso kamar ranta, me ya saka daddy bazai gane ba, me ya saka daddy ke san jefa ta cikin mugun hali, har ga Allah bata ji zata iya auran Kamal, barin ma yarda aka ce mata kamar da suke da Kamil tab'a ci, wani sabon kukan da sake saki a wurin, sosai take kuka soboda a lokacin shi kad'ai ne makamin ta, dan watak'ila ya ganta a haka zai hakura ya kyale ta amma da taga har an kusa awa be ce mata komi ba ta d'ago da idanunta da suke kallan k'asa tunda ta shigo ta d'ora a kan shi,

"Daddy wallahi ka aura mun shi zaka neme ni ka rasa, kuma baza ka tab'a samu na ba duk nema na da zakayi"

A lokacin ta d'anga ya motsa, lumshe idanun shi yayi sannan can ya bud'e su,

"Sakeena kina da hankali kike gaya mun wannan maganar?"

Ranshi a mugun b'ace yayi maganar, ita kuwa yanzu ta hawayen ta sun tsaya, ta kuma kafa mishi ido, ka kalle ta idanunta basa d'auke da ko alamar wasa, da gaske take in har daddy ya dage sai tayi aure zata kwashe ina ta ina ta ta bar mishi gidan, ji tayi yayi ajiyar zuciya ya girgiza kan shi,

"Tom shikenan naji, ki tashi ki koma cika amma ki tabbata kin kawo mun wani tsayaye kafin k'arshen shekarar nan, Allah ya miki albarka"

Wani irin dad'i taji ya kamata, har sai da kwalla ta fad'o fuskar ta, ta saki wani murmushi,

"Dan Allah da gaske kake?"

A rikice ta tambaye shi, shi kuwa d'aga mata kai yayi yai mata nuni da ta tashi ta fita, haka sakeena ta mik'e tana zuba mishi godiya har ta bar side d'inshi, tana shiga cikin gida tayi wurin mommy a guje ta rungume ta, tana murmushi ita kuwa mommy da ta ganta a haka tasan an sami abun da ake so, itama k'ara rungumota tayi tana nata murmushi tare da share y'an wurin da ke faman tambayar me ya faru.

---------

Tana kwance a kan gadon d'akin ta tana kar k'ad'a k'afa wani littafi na hannunta tana karanta wa, kwana biyu kullum tana cikin farin ciki, jinta take kamar a sama yanzu bata da wata damuwa, sati biyu yanzu ta fasa auran ta da akai, duk masoyin ta da yaji sai da ya taya ta murna, tayi nisa a cikin littafin taji ana kwad'a mata kira tun daga waje kuma muryar mommy, sauri tayi ta ajiye littafin dan kiran da take mata da ga ji ba na lafiya bane, ta mik'e zata k'arsa wurin mommy taga an banko k'ofa ta fad'o d'akin a burkice, Sakeena na ganinta a haka hankalin ta ya tashi, tayi saurin zuwa wurin ta tana tambayar ta lafiya, abun da taji bayan mommy ta bud'e bakin ta ya saka ta shiga cikin tsananin tashi hankali ta farar d'aya,

"Sakeena ya zamuyi, kawun ki ya d'aura miki aure yanzu yanzun nan"

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now