Thirty eight

1.6K 222 35
                                    

Yarda take avoiding kamal a gidan kamar wani mala'ikan mutuwa, kwata kwata bata bari su kasance wuri d'aya, dan yanzu Allah ya d'ora mata wani irin mahaukacin tsoron shi tun bayan abunda taga yayi wa ummeeta, kwanaki hud'u da suka wuce, dan haka in har yana gida bata fitowa har sai taji motar shi ta tashi alamar ya fita dan Allah yasan baza ta iya ta zuciyar shi ba.

Yanzu haka tana mak'ale a cikin d'aki, har yanzu tana guest room ta kasa komawa ai nayin d'akin ta dukda an gera k'ofar da kamal ya fasa kamar wani abu bai tab'a faruwa ba amma still ta kasa komawa, dan bama taso su had'u koya yake.

Jiya ma da ta fito kitchen d'uakar ruwa, tana fitowa daga side d'in, ta tsince shi a parlor yana zaune yana danna waya, gabanta sai da yayi wata muguwar fad'uwa dan a zatan ta baya nan dan taji k'arar motar, wani irin juyawa tayi zata koma ciki a guje, muryar shi ta dakatar da ita,

"Ki k'araso kiyi me zakiyi i dont bite"

Ko da yayi maganar baya kallonta, kamar ma bada ita yake ba, ga ya had'e muryar shi da fuska kamar wanda bai tab'a dariya, tsurewa ta k'ara yi amma a haka ta dake ta tafi sad'f sad'af kamar mara gaskiya ta shiga kitchen d'in, tana shiga ta fara maida numfashi, ta dad'e tana tattaro nustuwar ta snnan ta samu ta d'auko ruwan ta fito, tana fito ta sake cin k'aro da manyan idanunshi akan ta, ya ajiye wayar shi a gefe, hannushi nanad'e a fad'ed'an k'irjinshi, sauri tayi ta sauke idanunta a k'asa dan kawai ganin shi ya k'ara hardasa mata tsoro, a hankali tabi ta yi d'aki tana kuwa jin kwyaar idanunshi akan ta har ta b'acce.

Ajiyar zuciya tayi tare da gyra kwanciyar ta, ita haka rayuwa zata cigaban mata kenan, cikin b'akin ciki da k'unar rai dan tasan in har tana auran kamal baza ta tab'a kasancewa cikin farin ciki ba, hope d'inta gaba d'aya ya ruguza mata shi na barin gidan dan yanzu ta tabbata ummeeta baza ta k'ara takowa gidan ba saboda cin mutuncin da yayi mata, har yanzu tana tuna yarda ya fito da ummeeta daga d'akin tsirara bayan ya mata duka sannan ya cilla ta waje dukda yasan basu kad'ai bane a gida, da malam isyaku, ji tayi tsoron shi ya k'ara kamata.

"Allah ka raba ni da zuciyar kamal, Kada ka k'ara bari na shiga bad side d'inshi"

A hankali tayi addu'ar, ta k'ara jan bargonta ta, ta fara shirin bacci bayan ta tofe jikinta da addu'ar bacci.

----------

Yana jin gine, jikin k'ofar da take saitin gadon da yake a guest room d'in, hannunshi na cikin aljihun wandon shi, mayun manyan idanunshi kaf akan kyakyawar fuskar ta, baya ko k'ifta su, kallo yake mata, kallo me cike da abubuwa da dama, amma ita bama tasan ana yi ba dan baccin ta take sha.

Ya dad'e a jinginan da yake sai can kuma a hankali ya fara takawa baka jin ko sautin takun shi ya k'araso kusa da gadon, k'ara kafa wa kyaywara fuskar ido yayi, a hankali kuwa ya samu wuri ya zauna kusa da ita, amma har lokacin bai d'auke idanunshi daga kanta fuskar ta ba, ya fi mituna yana abu d'aya can kuwa ya saka hannun ya fara shafar fuskar ta a hankali, idanunshi sun k'ara canza wa, brown eyes d'inshin sun k'ara duhu, kallon da yake mata wanda zai saka ko wacce gab'a ta jikin ka sagewa da yin sanyi in har kai ake yima shi.

"Har yanzu fushi nake dake"

A hankali ya furta, yarda ko na kusa dashi bazai ji ba,

"Tsanata da kikayi tayi yawo haka da har ki kawo wacce zata ruguza mun rayuwa, ta saka ubangiji na fushi dani ta kuma saka iyaye na fushi dani"

A hankali ya k'ara fad'a, har lokacin yana shafa fuskar ta, abunda tayi mishi yayi mugun saka shi cikin k'unar ran da ya dad'e bai shiga ba, ta saka shi jin haushin ta, abun ba k'aramun yi mishi ciwo yiyi ba barin ma in har ya tuna da saninta duk abun ya faru.

"Kai ka manta abunda kayi mata? Ka kaita gidan karuwai ranar daran auran ku ka bada umarnin a tsige mata duk wani mutuncin ta"

Wani b'ari na zuciyar shi ya sanar dashi, a hankali kamal ya lumshe idanunshi, ji yayi zuciyar shi nayi mishi wani irin zugi, bayan wani irin zafi da tayi kamar garwashin wuta, har yanzu abun na d'awainiya da shi, baya ji zai tab'a yafe ma kanshi har abada, yasan aikin zuciya ne da zafin rabuwar shi da tilon k'anin shi yasa ya aikata haka, dan yanzu ya tabbata bata yi abunda ya zata tayi ba, bai fahimce ta bane, koma tayi bata cancanci abunda yayi mata ba.

ZAFIN RABO ✔️Where stories live. Discover now